26/05/2024
Babu wanda ya fi karfin bin doka komai girmansa, don haka Gwamna Abba yabi umurnin kotu, Inji Sheikh Dahiru Bauchi.
Sheikh Dahiru Bauchi, ya kuma tunatar da gwamnan Kano, Abba Yusuf cewa shi ma ya tabbata a kan kujerar gwamna ne saboda hukuncin kotu.
Sheihin ya kara da cewa "Babu wanda ya fi karfin doka komai girmansa, don haka akwai bukatar gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da zaman lafiya da adalci a jihar tare da kaucewa abin da zai haifar da rikici.
“Tunda kotu ta shiga tsakani, to akwai bukatar kowane bangare ya mutunta doka domin zaman lafiya.
"Ba daidai ba ne gwamnatin jihar Kano ta yi gaban kanta ta nada sabon Sarkin Kano, tare da tube sarakunan jihar biyar duk da umarnin kotu”.
Sheikh Dahiru Bauchi ya yi magana ne ta bakin shugaban gidauniyar Dahiru Bauchi, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi a wani taron manema labarai a Bauchi ranar Lahadi.
✍️ Comr Abba Sani Pantami