12/12/2024
Bari kuji tarihin Elon Musk da budurwarsa Amber heard, Elon Musk shine wanda yafi kowa kudi a duniya yanzu haka!
A hirar da akai da shi ya bayyana cewa bayan sun rabu da budurwarsa sai da ya dauko duk wani receipt na kuddin daya san ya taba kashe mata ko ya bata sannan yace sai ta biyashi.
Elon Musk ya bayyana cewa yana matukar son budurwarsa shiyasa ya shirya siyan kamfanin sada zumunta na Twitter domin ya ba ta kyautar sa a ranar bikin masoya ta duniya wato (Valentine's day) Amma sai akayi rashin sa'a kafin wannan ranar budurwarsa ta yaudare shi sannan ta fara soyayya da wani mutum daban sannan ta cigaba da holewarta tare da saurayinta a Twitter din .
Shi kuma saboda Jin haushin hakan bayan ya siye kamfanin sai ya goge account dinta daga Twitter din gaba daya sannan kuma ya nemo sabon saurayin nata ya bashi aiki a kamfanin sa, Shi kuma saurayin ganin haka yasa shima ya rabu da ita saboda ta ci amanar sabon ogan sa 😜
Sannan Kuma Elon Musk ya bayyana cewa shi fa indai harkar mata ce wallahi shi kankamo ne bazai iya asarar kuddin sa akan mata ba shiyasa har yanzu bashi da budurwa ko abokiyar zama.
SHIN WANNE DARASI KA KOYA DAGA LABARIN ELON MUSK TARE DA BUDURWARSA AMBER HEARD.
✍️ AAliyu Dan Musa