29/08/2025
DAREN DA BA ZAN TABA MANTAWA A RAYUWA NA BA!
'Yar Marigayi Sheikh Albaniy Zaria wato Aisha Albaniy Biz ta bada labarin✍️
Daren da ba zan ta'ba mantawa a rayuwa na ba shine daren da aka kashe mahaifina watau Malam Muh'd Auwal Adam Albaniy Zaria da yaya na Abdullahi da Mama na Ummu Abdulbarri😭😭, har yanzu sabo nake jin sa inna tuna wannan ranar.
Ba na mantawa ina hostel bayan mun fito exam ta NECO ranar asabar 2014 aka ce azo a tada generator don ayi karatun yamma bayan la'asar da aka saba yi, Abdullahi ne yazo ya tada generator, dana hango shi na tafi da sauri nace dashi Abdullahi muna ta shirye shiryen candy amma bani da kudi kuma ba na son na tambayi baba, yace ki bari zan baki kudin, nayi godiya, ya tada generator yayi gaba, ashe wannan ita ce rana ta karshe da zamu hadu dashi😭.
Kafin nan mun dawo exam bayan azahar mun gajji muka ci abinci muka yi sallah duk muka 'bingire da bacci 😭 ashe baccin asara ne da bahaushe kance ashe muna baccin da baza muyi na daren ranar ba😭😭, bamu tashi baccin ba sai 4:30pm shigowan Abdullahi don ya tada generator ya tashe mu❗
Bayan Baba (Malam Albany) ya kammala karatu aka yi sallar magrib, dama bayan sallah isha zasu tafi markazus Salafiyyah don yin karatun littafin bukhari, anan ne fa fargaba ta soma. Mu student muna ta jiran Baba ya dawo don 10pm ake tasowa zuwa 10:30pm yana dawowa ake tada mana generator mu samu muyi karatun exam, muka ji shiru🤔, shiru basu dawo ba da yake katangar gidan Baba (Malam Albaniy) da hostel dinmu 'daya ce, don da 'kofa ma a tsakanin mu, ya kan bude ya shigo don bincikar lafiyan daliban shi.
A lokacin 'daliban waje boarders suna da 'karamar waya Nokia da s**an kira iyayensu don gaisawa, anan ne fa misalin karfe 10:20pm wani da muka sani yakira mu yace kunji harbi kuwa😳? Muka ce a'a bamu ji ba, yace lallai ana harbi anan kusa da ku Allah yasa lafiya, a nan ne fa muka tsorata🥹 muka natsu, bayan wayanshi se ga wani junior student domin a lokacin duk anyi hutu mu kadai ne a school don muna exam din NECO, in muka gama kuma za muyi WAEC ya kiramu yace ina Aisha? nace gani yace kuyi HAKURI ALLAH YA KARBI RAN BABA duk haka muke Kiransa da BABA ko DIRECTOR.
Me zamuyi banda kuka da salati? Tambaya da wasun mu ke mun suna kuka, kar dai ace garbin da wancan yace ya ji su Baba aka kashe⁉️ Ai nan da nan muka sake kiranshi. muka ce Baba ya rasu tayaya❓ Yace bakuji harbi bi ba? to su aka kashe da Abdullahi da Ummu Abdulbarri 😭😭 ai sai 'daki ya kara rikicewa❗ Allah Ya bani karfin hali na koma ina rarrashinsu ni da aminiyata Asmaau tana mana nasiha sanan masu ihu s**a sassauta 😭
A wannan daren Baba (Malam Albaniy Zaria) ya yima yara 'kannen mu da suke gida alkawarin yau za aci dadi😭 kar wanda yayi bacci. kaji ne ya siya 50+ da bread manya kusan 10 don ayi farfesu da bread aci a daren, har yana musu wasa duk wanda ya cika cikin shi da abinci ya rasa inda ze ci kaza! Yara s**a yi ta murna ashe ba za'aci kaza da dadi ba 😭😭.
Ada da farko yana zuwa karatun Bukhari da mu, daga baya da muka koma hostel sai ya dena zuwa da kowa, amma ganin a lokacin anyi hutu sai ranar yace duka yara maza su shirya ze je da su.
Abdullahi
Abdulbarri
Abdulwahid
Abdulhalim
Abdulhaqqa
Da wasu daga cikin daliban sa maza, 'katuwan mota s**a cika, sai Ummu Abdulbarri a gaba kusa dashi, bana mantawa Abdulbarri yace BABA kayana duk sunyi datti, yace kaje Abdullahi ya ara maka, abun fa k**ar yana ji a jikinshi, don bai taba irin wannan zugan ba a motanshi, ko lokacin da yake zuwa da mu motan da ake kaimu daban tashi daga shi sai matan shi, amma a wannan rana yace dukansu su shirya...ashe zasu ga zahiri ne 😭😭😭😭
Daf da zasu shigo layin mu aka samu 'yan bindiga daba a san ko su waye ba s**a rinƙa harbin motan BABA ta ko ina😭😭😭 BABA cewa yake ku tsaya na fito ku kasheni, amma kar ku harbi sauran 😭😭😭 a wannan lokacin tuni Abdullahi da Ummu Abdulbarri sun mutu, 😭😭 bayan sunyi harbi s**a gudu s**a bar su cikin jini, Abdulwahid ne Allah ya bashi iko ya fito ya dafe BABA yana ihu a t**i yana dan Allah ku temakemu an harbi Albaniy, har lokacin Baba da ransa😭
Anan ne wani bawan Allah ya dauke su sai asibiti, anan ne BABA ya cika da kalmar shahada a gaban dalibansa, su kuma wanda s**a ji rauni akayi asibiti dasu, Abdulwahid ne ko kwarzane bai same shi ba, amma babu wanda be raunata ba. Abdullahi da Ummu Abdulbarri kam tuni rai yayi halinsa 😭 da wannan ina musu addu'a
ٱللَّهُمَّ ٱغْفِرْ لَهُمۡ وَٱرْحَمْهُمۡ، وَعَافِهِمۡ وَٱعْفُ عَنْهُمۡ، Ya Allah, ka gafarta musu, ka yi musu rahama, ka yalwata musu 'kabarinsu, ka sa 'kabarinsu ya kasance dausayin Aljanna, ka sanya su cikin rahamarka tare da salihan bayi Aameen
Muna yi ma wadanda s**a zalunce su damu addu'a da cewa Allah Yaa isa k**ar yadda BABA yayi musu kafin ya rasu❗ba zamu yafe ba, kuma ba zamu manta ba 😭
Kuyi HAKURI da rubutuna inayine Ina kuka k**ar yanzu nake ganin gawawwakin a gabana😭