Salafiyyah Network Nigeria TV

  • Home
  • Salafiyyah Network Nigeria TV

Salafiyyah Network Nigeria TV This page belongs to the fans of the late Ash-Sheikh Muhammad Auwal Adam Albaniy Zaria (Rahimahullah

17/09/2025

'YAR MARIGAYI MALAM ALBANY ZARIA TA RUBUTA Aisha Albaniy Biz ✍️

INSHA'ALLAHU (T) BABA ZAMU CIKA MAKA BURIN KA😭😭!

Allahu Akbar! Allah ya jiqan ka Baba da kai da yayana Abdullahi da Mamana Ummu AbdulBarri.

Wa'dannnan bayanan naka sun 'kara fito min da dalilin da yasa ka zaunar dani da Abdullahi (marigayi) Kace mana mu dage mu ci WAEC zaka Kai mu Sudan muje mu yi karatu don mu taimaka maka wajen gudanar da Daarul Hadeethis Salafiyyah 😭😭. Allah ya jiqan ka Baba yasa Jannatil Firdausi ce makomar ka😭😭.

Abdullahi dai yayi Shahada tare dakai insha'Allahu (T). Amma ni da sauran 'yan'uwana muna masu tabbatar maka da cewa insha'Allahu (T) wannan burin naka sai mun cika maka shi indai muna numfashi a doron 'kasa.

16/09/2025

✓Imam Malik (Shugaban Mazhabar Malikiyya) Yace:- Duk Wanda Yazagi Sahabin Manzon Allah (S.A.W) Yazama Arne.

14/09/2025

TALALA CE

Idan Allah Yayi fushi da bawa, ya kuma yanke alaka dashi kuma tabewa ta tabbata akan shi, sai Allah Yayi ta buda masa acikin harkokin sa.

Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "Idan ka ga Allah (SWT) yana bawa mutum walwala da wadata a rayuwar duniya alhali shi mai saba masa ne, to talala Allah yayi mishi."

[Al-Musnad Imam Ahmad : 16673]

Allah Madaukaki Ya fadi acikin Suratul-An'am cewa:

فَلَمَّا نَسُواْ مَا ذُكِّرُواْ بِهِۦ فَتَحْنَا عَلَيْهِمْ أَبْوَٰبَ كُلِّ شَىْءٍ حَتَّىٰٓ إِذَا فَرِحُواْ بِمَآ أُوتُوٓاْ أَخَذْنَٰهُم بَغْتَةً فَإِذَا هُم مُّبْلِسُونَ

"Sa’annan kuma a lokacin da s**a manta da abinda aka tunatar da su da shi, sai muka buɗe, a kansu, ƙofofin dukkan komai, har a lokacin da s**a yi farin ciki da abinda aka basu, muka k**a su, kwatsam, sai gasu sun yi tsuru-tsuru."

[Suratul-An'am : 44]

Wani daga cikin magabata yana cewa: Sau da yawa akwai wadanda aka yi musu talala da ni'imomin da Allah ya musu amma basu sani ba.

14/09/2025

“Abokan zamantakewa a kowane fanni na rayuwa, su ne masu buɗaɗɗiyar zuciya daɗin sha'ani garesu, idan ka burgesu sai su yaba maka, idan kai musu laifi sai su faɗa maka, idan ka aikata ba dai-dai ba sai su nuna maka hanya game da ƙarfafa maka gwuiwa tare da maka gyara babu ɓoye-ɓoye b***e rufa-rufa.”

13/09/2025

•BA'A WASA DA LOKACIN KARATU!
•Akwai Memory Card 32gb Cike Da Karatuttukan Mallam Albani Zaria (R.H)Na Siyarwa N5k, Duk Mai Buqata Ya Rubuta Albani Memory Card Ta Whatsapp Ta Wannan Lambar +2348146535352

12/09/2025

•Tsokaci Kan Tsaftar Masallaci.
•Akwai Memory Card 32gb Cike Da Karatuttukan Mallam Albani Zaria (R.H)Na Siyarwa N5k, Duk Mai Buqata Ya Rubuta Albani Memory Card Ta Whatsapp Ta Wannan Lambar +2348146535352

12/09/2025

Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan Allah ya ba wa ɗayanku alheri to ya fara da kansa sai kuma iyalan gidansa.”

~ Sahih Muslim: 1822

Duk sanda Allah ya ma wata Ni’ima, to ka fara moran wannan abun sannan iyalanka ka jiyar da su dadi, ba ka zama mai taimako a wajen ba amma iyalanka na kukan kana masu rowa, wannan ba dabi’a ce mai kyau ba.

08/09/2025

FA'IDOJI DAGA CIKIN TATTAUNAWAR SHEIKH BARRISTER MUHAMMADU SANI DA TASHAR HASKE REDIO COOMASIE, GHANA. (001)

Ala'kar Sheikh Barrister Muhammad Sani da Ash-Sheikh Albaniy Zaria (RH).

02/09/2025

TA'AZIYYA GA ABU AISHA AUZA'I AHMAD ABDULLAHI DA SAURAN 'YAN'UWA DA ABOKANAYEN ARZIKI.

Innalillahi wa inna ilaihi Rajiun. Allah yayi ma Hajara Ahmad Abdullah rasuwa, 'kanuwa ga 'dan'uwa Abu Aisha Auza'i Ahmad.

Muna rokon Allah ya gafarta mata ya kuma sa Jannatil Firdausi ita ce makoma gare ta.

30/08/2025

GARGAƊI WAJEN AIKATA BIDIʼAR BIKIN MAULIDI

Asalin Maulidi: Bidi'ancin Maulidi ya faru ne a daular Ƴaƴan Ubaid (Bani-Ubaid) a cikin daular shi'a rafidawa, wanda ake musu laƙabi da Faɗimiyya. Kuma haƙiƙa waɗannan mutanen sun ƙirƙiri maulidin Annabi (ﷺ) da alayen gidansa da sauransu daga cikin waliyyai da salihan bayi, kai harda waɗanda suke kan ɓata da ƙarya na daga cikin masu aƙidar bautan ƙaburbura, sai s**a fara yin bikin sabon shekara suna masu koyi da yahudawa, sai maulidin Annabi (ﷺ) koyi da Nasara, sai maulidin Aashura, sai maulidin Ali dan Abi Ɗalib (RA), sai maulidin Hassan da Hussain, sai maulidin faɗima (RA), sai maulidin khalifan da yake kan shugabanci, sai maulidin rajab, sai maulidin daren nasfa, sai maulidin farkon sha'aban da tsakiyarta, sai maulidin gadir, sai maulidin shigowar sanyi da shigowar zafi, da bazara, sai bikin khalij da ranar nuruz da sauransu masu yawa. Mutum na farko da ya ƙirƙire ta shi ne Al'mu'izz li dinillah a shekara ta 263 na hijira, a garin Al-ƙahirah, sai bikin ya cigaba har zuwa lokacin Abu Qasim shugaban rundunar musulunci na Ibn Badr Aljamali, da kuma mataimakin Khalifa Al'musta'ali billah a shekaran 490 na hijra, sai kuma da waɗanda s**a biyo bayansu k**ar su Umar Ɗan Muhammad Al-malal irbali, ɗaya daga cikin sufaye masu shuhura su 16, sai kuma aka sake samun wanda ya sake dawo da wannan bidi'a ta maulidi, da wannan malik Irbal su 14 da sauransu.

~ Sheikh Muhammad Aliyu Farkus

DAREN DA BA ZAN TABA MANTAWA A RAYUWA NA BA!'Yar Marigayi Sheikh Albaniy Zaria wato Aisha Albaniy Biz ta bada labarin✍️D...
29/08/2025

DAREN DA BA ZAN TABA MANTAWA A RAYUWA NA BA!

'Yar Marigayi Sheikh Albaniy Zaria wato Aisha Albaniy Biz ta bada labarin✍️

Daren da ba zan ta'ba mantawa a rayuwa na ba shine daren da aka kashe mahaifina watau Malam Muh'd Auwal Adam Albaniy Zaria da yaya na Abdullahi da Mama na Ummu Abdulbarri😭😭, har yanzu sabo nake jin sa inna tuna wannan ranar.

Ba na mantawa ina hostel bayan mun fito exam ta NECO ranar asabar 2014 aka ce azo a tada generator don ayi karatun yamma bayan la'asar da aka saba yi, Abdullahi ne yazo ya tada generator, dana hango shi na tafi da sauri nace dashi Abdullahi muna ta shirye shiryen candy amma bani da kudi kuma ba na son na tambayi baba, yace ki bari zan baki kudin, nayi godiya, ya tada generator yayi gaba, ashe wannan ita ce rana ta karshe da zamu hadu dashi😭.

Kafin nan mun dawo exam bayan azahar mun gajji muka ci abinci muka yi sallah duk muka 'bingire da bacci 😭 ashe baccin asara ne da bahaushe kance ashe muna baccin da baza muyi na daren ranar ba😭😭, bamu tashi baccin ba sai 4:30pm shigowan Abdullahi don ya tada generator ya tashe mu❗

Bayan Baba (Malam Albany) ya kammala karatu aka yi sallar magrib, dama bayan sallah isha zasu tafi markazus Salafiyyah don yin karatun littafin bukhari, anan ne fa fargaba ta soma. Mu student muna ta jiran Baba ya dawo don 10pm ake tasowa zuwa 10:30pm yana dawowa ake tada mana generator mu samu muyi karatun exam, muka ji shiru🤔, shiru basu dawo ba da yake katangar gidan Baba (Malam Albaniy) da hostel dinmu 'daya ce, don da 'kofa ma a tsakanin mu, ya kan bude ya shigo don bincikar lafiyan daliban shi.

A lokacin 'daliban waje boarders suna da 'karamar waya Nokia da s**an kira iyayensu don gaisawa, anan ne fa misalin karfe 10:20pm wani da muka sani yakira mu yace kunji harbi kuwa😳? Muka ce a'a bamu ji ba, yace lallai ana harbi anan kusa da ku Allah yasa lafiya, a nan ne fa muka tsorata🥹 muka natsu, bayan wayanshi se ga wani junior student domin a lokacin duk anyi hutu mu kadai ne a school don muna exam din NECO, in muka gama kuma za muyi WAEC ya kiramu yace ina Aisha? nace gani yace kuyi HAKURI ALLAH YA KARBI RAN BABA duk haka muke Kiransa da BABA ko DIRECTOR.

Me zamuyi banda kuka da salati? Tambaya da wasun mu ke mun suna kuka, kar dai ace garbin da wancan yace ya ji su Baba aka kashe⁉️ Ai nan da nan muka sake kiranshi. muka ce Baba ya rasu tayaya❓ Yace bakuji harbi bi ba? to su aka kashe da Abdullahi da Ummu Abdulbarri 😭😭 ai sai 'daki ya kara rikicewa❗ Allah Ya bani karfin hali na koma ina rarrashinsu ni da aminiyata Asmaau tana mana nasiha sanan masu ihu s**a sassauta 😭

A wannan daren Baba (Malam Albaniy Zaria) ya yima yara 'kannen mu da suke gida alkawarin yau za aci dadi😭 kar wanda yayi bacci. kaji ne ya siya 50+ da bread manya kusan 10 don ayi farfesu da bread aci a daren, har yana musu wasa duk wanda ya cika cikin shi da abinci ya rasa inda ze ci kaza! Yara s**a yi ta murna ashe ba za'aci kaza da dadi ba 😭😭.

Ada da farko yana zuwa karatun Bukhari da mu, daga baya da muka koma hostel sai ya dena zuwa da kowa, amma ganin a lokacin anyi hutu sai ranar yace duka yara maza su shirya ze je da su.
Abdullahi
Abdulbarri
Abdulwahid
Abdulhalim
Abdulhaqqa
Da wasu daga cikin daliban sa maza, 'katuwan mota s**a cika, sai Ummu Abdulbarri a gaba kusa dashi, bana mantawa Abdulbarri yace BABA kayana duk sunyi datti, yace kaje Abdullahi ya ara maka, abun fa k**ar yana ji a jikinshi, don bai taba irin wannan zugan ba a motanshi, ko lokacin da yake zuwa da mu motan da ake kaimu daban tashi daga shi sai matan shi, amma a wannan rana yace dukansu su shirya...ashe zasu ga zahiri ne 😭😭😭😭

Daf da zasu shigo layin mu aka samu 'yan bindiga daba a san ko su waye ba s**a rinƙa harbin motan BABA ta ko ina😭😭😭 BABA cewa yake ku tsaya na fito ku kasheni, amma kar ku harbi sauran 😭😭😭 a wannan lokacin tuni Abdullahi da Ummu Abdulbarri sun mutu, 😭😭 bayan sunyi harbi s**a gudu s**a bar su cikin jini, Abdulwahid ne Allah ya bashi iko ya fito ya dafe BABA yana ihu a t**i yana dan Allah ku temakemu an harbi Albaniy, har lokacin Baba da ransa😭

Anan ne wani bawan Allah ya dauke su sai asibiti, anan ne BABA ya cika da kalmar shahada a gaban dalibansa, su kuma wanda s**a ji rauni akayi asibiti dasu, Abdulwahid ne ko kwarzane bai same shi ba, amma babu wanda be raunata ba. Abdullahi da Ummu Abdulbarri kam tuni rai yayi halinsa 😭 da wannan ina musu addu'a
ٱللَّهُمَّ ٱغْفِرْ لَهُمۡ وَٱرْحَمْهُمۡ، وَعَافِهِمۡ وَٱعْفُ عَنْهُمۡ، Ya Allah, ka gafarta musu, ka yi musu rahama, ka yalwata musu 'kabarinsu, ka sa 'kabarinsu ya kasance dausayin Aljanna, ka sanya su cikin rahamarka tare da salihan bayi Aameen

Muna yi ma wadanda s**a zalunce su damu addu'a da cewa Allah Yaa isa k**ar yadda BABA yayi musu kafin ya rasu❗ba zamu yafe ba, kuma ba zamu manta ba 😭

Kuyi HAKURI da rubutuna inayine Ina kuka k**ar yanzu nake ganin gawawwakin a gabana😭

12/08/2025

•1️⃣2️⃣Hiqbatun Minat Tareekh
•Akwai Memory Card 32gb Cike Da Karatuttukan Mallam Albani Zaria (R.H)Na Siyarwa N5k, Duk Mai Buqata Ya Rubuta Albani Memory Card Ta Whatsapp Ta Wannan Lambar +2348146535352

Address


Telephone

+2348104584828

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Salafiyyah Network Nigeria TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Salafiyyah Network Nigeria TV:

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share