RCN Hausa

RCN Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from RCN Hausa, Social Media Agency, Abuja.

Ƙungiyar Arewa Media Writers Ta Halarci Taron Wayar Da Kan Al'umma Da Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya Ta Shirya A ...
13/10/2024

Ƙungiyar Arewa Media Writers Ta Halarci Taron Wayar Da Kan Al'umma Da Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya Ta Shirya A Jihar Katsina

Daga Kungiyar Arewa Media Writers

Ƙungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani "Arewa Media Writers" ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Comr Haidar H. Hasheem, ta halarci taron wayar da kan al'umma a jihar Katsina. Taron na kwana guda an shirya shi ne ƙarƙashin gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya (Coalition of Northern Groups - CNG), wanda aka gudanar a jiya Asabar bisa jagorancin Shugaban kwamitin amintattu na CNG, Dr. Nastura Ashir Shariff.

Taron ya samu halartar shugabannin ƙungiyar a matakin jiha da kuma mambobi daga Katsina, inda aka samu wakilcin shugaban Arewa Media Writers na jihar Katsina, Comr Nura Siniya, tare da shugabannin ƙungiyar na jihar Katsina da sauran mambobi. Wannan taro na da muhimmanci wajen tattauna matsalolin tsaro da kuma yadda za a kare yara daga shan miyagun ƙwayoyi, musamman a yankin Arewacin Najeriya.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Comr Haidar H. Hasheem, ya yi jawabi a wajen taron, inda ya nuna muhimmancin haɗin kai wajen magance matsalolin da suke addabar yankin Arewa. Ya kuma jaddada cewa, akwai buƙatar gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa hannu wajen kare martabar yankin ta hanyar magance matsalolin tsaro da shaye-shayen kayan maye.

A yayin taron, an gabatar da tattaunawa mai zurfi kan hanyoyin da za a bi domin ƙarfafa tsaron al'umma da kuma samar da shawarwari akan dabaru da za su taimaka wajen tsaftace rayuwar matasa da kare su daga faɗawa cikin haɗarin shaye-shaye. Haka kuma an yi kira ga iyaye da su yi amfani da damar wajen kula da tarbiyyar 'ya'yansu.

A ƙarshe, Comr Haidar H. Hasheem, ya buƙaci mambobin ƙungiyar da al’umma baki ɗaya su ci gaba da bayar da goyon baya domin samun nasarar burin da aka sanya a gaba na inganta tsaro da walwalar al’umma.

Arewa Media Writers na bukatar addu'oinku domin ganin ta sauke babban aikin da ta ɗauka a wannan lokaci.

Ƙungiyar Arewa Media Writers Ta Kasa Ta Ziyarci Shugabannin Kungiyar Reshen Jihar Katsina Domin Tattaunawa Kan Inganta A...
12/10/2024

Ƙungiyar Arewa Media Writers Ta Kasa Ta Ziyarci Shugabannin Kungiyar Reshen Jihar Katsina Domin Tattaunawa Kan Inganta Ayyukan Kungiyar.

Daga Ƙungiyar Arewa Media Writers.

A wani rangadi na zagayen jihohin Arewa 20 har da babban birnin tarayya Abuja, sabon shugaban ƙungiyar marubutan Arewa a kafofin sada zumunta na zamani wato "Arewa Media Writers" na ƙasa, Comr Haidar H. Hasheem, ya jagoranci wata muhimmiya ziyarar rangadi zuwa jihar Katsina ranar Juma'a 11 ga watan Oktoba shekarar 2024, inda ya gana da shugabannin kungiyar reshen jihar da wasu mambobi na ƙungiyar.

Wannan taro na musamman ya samu halartar manyan shugabannin kungiyar Arewa Media Writers reshen jihar Katsina tare bisa jagorancin shugaban ƙungiyar a jihar Katsina Comr Nura Siniya, wanda s**a tarbi sabon shugaban ƙungiyar na ƙasa Comrd Haidar H. Hasheem da tawagarsa.

Manufar wannan taro ita ce farfaɗo da shugabancin kungiyar a jihar Katsina, da kuma farfaɗo da ayyukan ƙungiyar a jihar. Shugabannin ƙasa da na jihar sun tattauna batutuwa masu muhimmanci kan yadda za'a inganta ƙungiyar, ta hanyar rubuce-rubuce da zasu taimaka wajen inganta yankin Arewa baki ɗaya.

A yayin da yake jawabi, Shugaban kungiyar na ƙasa, Comr Haidar H. Hasheem, ya nuna farin cikinsa game da yadda shugabannin na jihar Katsina s**a yiwa wajen ciyar farin ɗango,Mahalartan sun matukar nuna ƙwazo sun kuma nuna a shirye suke don aiki tuƙuru wa ƙungiyar. Haidar ya jaddada cewa haɗin kai da aiki tare sune kaɗai zasu taimaka wajen cimma burin ƙungiyar, tare da tabbatar da cewa za'a yi aiki tukuru don amfanar da ƙungiyar baki ɗaya.

Shugabannin sun yi nazari kan yadda za a tabbatar da cewa ƙungiyar ta cigaba da kasancewa cikin tsari, tare da yin amfani da rubuce-rubuce wajen haɓaka ilimi da kuma wayar da kai a yankin Arewa. Haka kuma an tattauna dabaru na zamani da zasu taimaka wajen isar da saƙonni ga al'umma cikin ingantacciyar hanya don kiyaye yaɗa labarin ƙanzon-kurege cikin al'umma.

Bayan kammala jawabin Shugaban ƙungiyar, an ba mahalarta damar bayyana ra'ayoyinsu ta hanyar tattaunawa kan manyan tsare-tsaren ƙungiyar. Haka zalika, an tattauna hanyoyin da za'ayi amfani da su wajen samar da horo ga mambobi, domin su ƙara ƙwarewa a harkar rubuce-rubuce da sauran abubuwan da za su taimaka musu wajen dogaro da kansu.

A ƙarshe, Shugaban ƙungiyar, Comr Haidar H. Hasheem, ya yi kira ga shugabannin reshen Jihar Katsina da mambobinsu cewa su cigaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukan ƙungiyar k**ar yadda s**a saba,Ya kuwa basu tabbacin dukkan goyan baya da duk wani taimako daga shugabannin kungiyar matakin ƙasa don tabbatar da samun nasarar kungiya a Jihar Katsina.

Taron ya ƙare da jawabin rufewa daga bakin ɗaya cikin jagororin Kungiyar a matakin ƙasa Comr Ɗan Arewa, inda yay godiya ga dukkan mahalarta taron,tare da yin fatan alheri ga cigaban ƙungiyar.

Arewa Media Writers tana buƙatar addu'oinku a kowanne lokaci don ganin ta cimma burikanta na alkhairi da ta sanya gaba.

YANZU-YANZU: An saki Seaman Abbas amma kuma an koreshi daga aikiK**ar yadda kuke gani yau dai ga Seaman Abbas da Matarsa...
27/09/2024

YANZU-YANZU: An saki Seaman Abbas amma kuma an koreshi daga aiki

K**ar yadda kuke gani yau dai ga Seaman Abbas da Matarsa Hussaina zaune a tare bayan sake shi da hukumar sojin ruwa tayi daga tsare tsawon shekaru 6.....

Mai Brekete Family, wato Ordinary President Ya kirawo mai magana da yawun rundunar tsaron kasa don ya tabbatarwa duniya cewa Seaman Abbas shin sakinsa akayi kokuwa guduwa yayi daga inda yake tsare, inda aka tabbatar sakin sa akai

Meye ra'ayin ku ?

Dawo da Sanusi kan mulkin masarautar Kano na daga cikin abubuwa mafi muhimmaci a rayuwa ta - El-RufaiTsohon Gwamnan jiha...
25/09/2024

Dawo da Sanusi kan mulkin masarautar Kano na daga cikin abubuwa mafi muhimmaci a rayuwa ta - El-Rufai

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yabawa Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf kan dawo da Muhammadu Sanusi na II kan karagar mulkin Kano.

El-Rufai, ya ce dawo da Sarkin na daya daga cikin "Abubuwa mafiya muhimmaci da s**a faru a rayuwat".

Tsohon Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau Laraba, a yayin taron horas da matasa kan fasahar zamani na jihohin Arewa mai suna Arewa Tech Fest dake gudana a Kano.

Taron ya samu halartar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf wanda ya samu wakilcin mataimakinsa da Gwamnan Katsina, Dikko Radda da wakilcin Gwamnan Zamfara.

24/09/2024

S.A.W 🥰🥰🥰

Da Ɗumi-Ɗumi.Ɗan takarar gwamnan jihar Edo na jam'iyyar APC Monday Okpebholo ya lashe zaɓen gwamnan jihar da rinjaye kur...
22/09/2024

Da Ɗumi-Ɗumi.

Ɗan takarar gwamnan jihar Edo na jam'iyyar APC Monday Okpebholo ya lashe zaɓen gwamnan jihar da rinjaye kuru'u 291,667 ,yayi rinjaye kan ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP Asue Ighodalo mai kuru'u 247,274.

Abdulkadir Nafi'u.

Labari cikin Hotuna.Yadda ɗumbin al'ummar ƙaramar hukumar Batsari s**a fito maza da mata, yara da manya a yau Asabar 21/...
21/09/2024

Labari cikin Hotuna.

Yadda ɗumbin al'ummar ƙaramar hukumar Batsari s**a fito maza da mata, yara da manya a yau Asabar 21/9/2024 don gudanar da sallar Nafila da addu'o'i gameda halin matsin rayuwa da matsalar tsaro da suke ciki,don neman gafara da rokon sauki ga Allah.....

Irin haka dai mako biyu da s**a gabata Al'ummar ƙaramar hukumar s**a fito don sallatar Nafila da addu'o'i gameda halin da suke ciki na tsananin rayuwa da matsalar tsaro wanda suke fama dashi,da zummar Allah ya yaye masu yanayin yakuma kawo masu karshen matsalar tsaro da suke ciki.....

TIRKASHI: Wani likita dake Zaria ya ajiye aikin shi saboda Mining din HAMSTER. Ma'aikacin Asibiti mai suna Pharm Musa A ...
20/09/2024

TIRKASHI: Wani likita dake Zaria ya ajiye aikin shi saboda Mining din HAMSTER.

Ma'aikacin Asibiti mai suna Pharm Musa A Bello Zaria, ya bayyana takkaddar ajiye aikin shi a safinshi na Facebook inda ya bayyana cewa ya ajiye aikin nashi ne kan saran tsammanin fashewar HAMSTER wanda zai zama miloniya ya bude kamfanoni da kudin Mining din tare da daukar ma'aikata aiki a karkashin kamfanin nashi.

Wace shawara zaku bashi?

Asibitin koyarwa na tarayya a jihar Gombe ya hana ma'aikatansa mainin na kirifto a lokutan aiki.
19/09/2024

Asibitin koyarwa na tarayya a jihar Gombe ya hana ma'aikatansa mainin na kirifto a lokutan aiki.

Hukumar Jarabawa ta Kasa NECO ta fitar da sak**akon jarabawar ɗalibai na shekarara 2024.
19/09/2024

Hukumar Jarabawa ta Kasa NECO ta fitar da sak**akon jarabawar ɗalibai na shekarara 2024.

INNAA LILLAAHI WA INNAA ILAIHI RAAJI'UUN Ƴan uwa masu Albarka mu taru ƙonmu da kwarkwatan mu domin mu halaka wannan tsin...
19/09/2024

INNAA LILLAAHI WA INNAA ILAIHI RAAJI'UUN
Ƴan uwa masu Albarka mu taru ƙonmu da kwarkwatan mu domin mu halaka wannan tsinan nan page ɗin

Innaa Lillaahi Wa Innaa Ilaihi Raaji'uun
Abin takaici videos ɗin ayoyin Qur'aani ake rerawa tare da kiɗa sannan da ƴan Mata Ana rawa a gidan casu.

Mu Nome Wannan Shafin Ta Hanyar Yin Report Ɗin shi

Ga link ɗin nan:👇
https://www.facebook.com/profile.php?id=61566336471182

https://www.facebook.com/61566336471182/videos/1551748778754184/?app=fbl

Bankin CBN zai fara daukar harajin tsaron yanar gizo na "Cyber security Levy" daga masu ajiyar kudi a bankuna.Me zaku ce...
19/09/2024

Bankin CBN zai fara daukar harajin tsaron yanar gizo na "Cyber security Levy" daga masu ajiyar kudi a bankuna.

Me zaku ce ??

DA ƊUMI ƊUMI: Kwalejin Tarayya Na Horas Da Malamai FCE Zariya Ta Zama Jami'a.Makarantar ilimi ta horas da malamai ta tar...
18/09/2024

DA ƊUMI ƊUMI: Kwalejin Tarayya Na Horas Da Malamai FCE Zariya Ta Zama Jami'a.

Makarantar ilimi ta horas da malamai ta tarayya wacce aka fi sani da ‘Federal Collage Of Education Zaria’ ta zama Jami'ar Tarayyar ilimi na horas da malamai, inda yanzu ake kiranta da ‘Federal University Of Education Zaria.’

Bugu da ƙari makarantar sashen ilimin ta tarayya wacce a yanzu ta koma ‘Federal University Of Education Zaria’ ta naɗa Dr. Balarabe wanda ya taɓa riƙe shugaban makarantar lokacin tana kwalejin ilimi na horas da malamai wato ‘Provost' a kwalejin, matsayin mataimakin Shugaban riƙo na jami'ar ilimi ta tarayya dake Zariya (FUEZ).

DA DUMI-DUMI: Sojin Nigeria Sun K**a k**a Wasu Mutane Da Suke Yiwa 'Yan Bîndîgá Safarar Mak**ai  A Jihar Filato Manjo St...
17/09/2024

DA DUMI-DUMI: Sojin Nigeria Sun K**a k**a Wasu Mutane Da Suke Yiwa 'Yan Bîndîgá Safarar Mak**ai A Jihar Filato

Manjo Stephen Zhakom ya fitar ranar Talata, ya ce an samu nasarar ce bayan wani aikin samame da s**a kai jihar, inda ya ce hakan na cikin zimmar sojoji na ganin sun kakkaɓe masu rike da mak**ai ba bisa ka'ida ba.

"An fara samamen da dakarun Operation Safe Haven s**a yi tare da haɗin gwiwar wasu jami'an tsaro ne a ranar Litinin da daddare har zuwa safiyar yau Talata," in ji shi.

Ya ce dakarun sun yi wa maɓoyar wani mai safarar bindigogi mai suna Mohammed Sani a garin Naraguta kan hanyar Bauchi zuwa Jos, inda nan ne kuma s**a yi nasarar k**a shi tare da wasu mutum huɗu.

Mak**ai da sojojin s**a kwace sun haɗa da bindigar AK-47 guda biyu, alburusai da sauransu.

Zhakom ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan mutanen da aka k**a d anufin ƙara samun bayanai da za su kai ga k**a sauran masu harkar domin daƙile aikinsu.

Majiya BBC Hausa

Tsohon shugaban Amurka, Trump ya shiga harkar crypto Tsohon shugaban kasar Amurka, Donal Trump tare da 'ya'yan sa sun ka...
17/09/2024

Tsohon shugaban Amurka, Trump ya shiga harkar crypto

Tsohon shugaban kasar Amurka, Donal Trump tare da 'ya'yan sa sun kaddamar da manhajar hada-hadar kudi ta yanar gizo da aka fi sani da cryptocurrency.

Ba a yi wani cikakken bayani ba kan tsarin crypto din da Trump, wanda shi ne dan takara shugaban kasa a jam'iyyar Republican da ahalinsa su ka samar a wani bikin kaddamarwar da aka yi na kai-tsaye tsawon awanni biyu a shafin sada zumunta.

An yi ƙaddamarwar ne k**ar yadda aka tsara kuma ba a fasa ba duk da yunkurin kashe Trump da aka yi a ranar Lahadi.

World Liberty Financial dai tayi niyyar yin aiki ga tsarin crypto din na Trump inda za a baiwa mutane damar bada aro ko karbar aron kudin crypto wanda shafukan cryptocurrency da dama ke yi.

Dan tsohon shugaban kasar, mai suna Trump Jr. ya bayyana lamarin a matsayin "Fara juyin juya hali a fannin hada hadar kudi", a yayin gabatarwar a shafin X.

Daily Nigerian Hausa

MS Adamu.Ogan Abbas jami'in Sojin Ruwa da yakwashe shekara 6 ana azabtar dashi don yaje Sallah ba tare da izinin ogansa ...
15/09/2024

MS Adamu.

Ogan Abbas jami'in Sojin Ruwa da yakwashe shekara 6 ana azabtar dashi don yaje Sallah ba tare da izinin ogansa ba.

Dan uwan mu ne ɗan Najeriya,ɗan Arewa kuma musulmi.....Jami'in soji ne da ya amince yabar iyalansa don bautawa ƙasar sa ...
15/09/2024

Dan uwan mu ne ɗan Najeriya,ɗan Arewa kuma musulmi.....

Jami'in soji ne da ya amince yabar iyalansa don bautawa ƙasar sa ta hanyar kare rayuka,lafiya da dukiyar al'umma....

Yana bukatar addu'ar mu,ga halin da ogansa na aiki ya jefashi tsawon shekaru 6 bisa laifin yaje sallah ba tareda sanarwa ogansa ba....

Tsawon shekaru 6 ana gana masa azaba,bashida mai taimako sai Allah,aikinsa bautawa ƙasar sa,laifinsa yin Sallah kan lokaci....

Allah ka bawa Abbas mafita,ka karfafi zuciyar iyalansa,Ubangiji kayi masa sakayya Ga ogansa da ya zalunceshi,da duk wanda ya goyi bayan zaluntar Abbas bisa laifinsa na sallah kan lokaci.

🖊️ Abdulkadir Nafi'u

15/09/2024

Daga dajin Zamfara:Bidiyon jami'in Sojin da ya halaka ɗan bindiga Halilu Sububu da yaransa.

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when RCN Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share