Jaridar demokraɗiyya

Jaridar demokraɗiyya News in hausa language

Ministan Ilimi Dakta Tunji Alausa ya roki Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS) da sauran kungiyoyin ɗalibai su hada kai domi...
27/08/2026

Ministan Ilimi Dakta Tunji Alausa ya roki Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS) da sauran kungiyoyin ɗalibai su hada kai domin bawa Shugaba Tinubu kuri’u miliyan 10 a zaben 2027.

Alausa ya yi wannan rokon ne yayin da shugabannin NANS da sauran kungiyoyin ɗalibai s**a kai masa ziyara a ofishinsa.

Ministan ya ce ɗaliban Najeriya suna da muhimmiyar rawa da zasu taka a zaben 2027, duba da yadda s**a amfana da sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta kawo a bangaren ilimi.

Ya ce fiye da dalibai miliyan 1.6 s**a amfana da shirin bayar da bashi ga dalibai wato NELFUND.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Shugaban kungiyar NANS Kwamarex Babatunde Afeez Akinteye, ya yabawa gwamnatin Tinubu kan shirye-shiryen NELFUND da TVET, yana mai cewa shirye-shiryen sun yi matukar tasiri ga rayuwar dalibai.

Akinteye ya bukaci gwamnati ta kara mayar da hankali kan wajen magance matsalolin da s**a shafi bayar da tallafin karatu.

27/08/2026

Shugaban EFCC ya bayyana shirin da hukumar ke yi kan kadarorin Abubakar Malami da ba su a cikin 48 da aka kwace - Karin bayani a sashen sharhi.

Hoto: Abubakar Malami, SAN (Facebook) (X)

27/08/2026

Ana magana da harshen a ƙauyuka da garuruwa da kasuwanni da makarantu da kafafen yaɗa labarai da sauran hulɗoɗin yau da kullum.

Karin bayani - https://bbc.in/4qE56TF

27/08/2026

Babban Malamin Addinin Musulinci A Nijeriya, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, Ya Bayyana Cewa, Fadin Kalmar Muslim-muslim Ko Kirista-kiristan Ticket Bazai Zama Makami Wajen Yakin Neman Zaɓe Ga Jagorori Nagari Ba A Nijeriya.

Sheikh Nuru, Yace, A Lokacin Da Ta'adanci Da Sace-sace Da Kashe Mutane Ke Cigaba Da Kamari, A Daa Ana Daukar Mutum Daya Zuwa Biyu, Amma Yanzu Har Masallaci Ake Zuwa Ana Kwashe Mutane Gaba Daya A Tafi Daji Dasu A Nijeriya.

27/08/2026

Kwamared Waiya ya faɗi hakan lokacin da ya ke karbar bakuncin tsofaffin daraktocin mulki da shugabannin ofisoshi da sakatarorin ƙananan hukumomin Kano 44 waɗanda ya ce tsohon gwamna Kwankwaso ya bayar da umarni a sallama a gwamnatin Abba farkon hawa mulki a tsakanin 2023 zuwa 2024.

Kwamishinan ya shaida cewa a baya Sanata Kwankwaso ne ya tilastawa gwamna Abba Kabir Yusuf ya aiwatar da wasu abubuwa da s**a saɓa da ci gaban Kano.

27/08/2026

Ma'aikatan filin jirgin saman birnin Frankfurt na Jamus guda shida sun kamu da cutar malaria, inda biyu daga ciki s**a mutu, sak**akon cizon sauro da wani jirgin sama ya dauko daga Afirka.

Cibiyar lafiya ta Jamus Robert Koch Institut, ta ce nau'in sauro mai suna Anopheles da aka shigo da shi ta jirgin sama ne ya ciji ma'aikatan shida.

27/08/2026

Rahotanni daga Villa sun bayyana cewa Shugaba Tinubu ya shiga ganawar sirri da gwamnonin jam’iyyar APC.

Ganawar na zuwa ne kwanaki kadan bayan fitar da sunayen mambobin kwamitin yakin neman zaben Tinubu a 2027.

Shin me kuke tunanin zasu tattauna?

27/08/2026

Tsohon shugaban rundunar sojin Bosnia kuma guda cikin kwamandodin da su ka yiwa dubban Musulmi kisan ƙare dangi a ƙasar, Ratko Mladic ya mutu yana da shekaru 84 yau alhamis.

Mladic wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da cewar ya aikata laifukan yaƙi, ya jagoranci kisan musulmi aƙalla dubu 8,000 a shekarar 1995, kisa mafi muni da nahiyar Turai ta gani tun bayan yaƙin duniya na 11.

Ƙarin bayani: https://rfi.my/CzrN

Am0rk@ na ci gaba da tura 'Yan aike domin shawo kan lran.Game da ziyarar Ministan Harkokin Wajen Qatar zuwa Iran a daida...
27/08/2026

Am0rk@ na ci gaba da tura 'Yan aike domin shawo kan lran.

Game da ziyarar Ministan Harkokin Wajen Qatar zuwa Iran a daidai wannan lokaci.

Abin da ake gani a yanzu shi ne, Amurka ba ta son dakatar da yaƙin ko cimma wata yarjejeniyar ƙarshe da lɍ@ñ hair sai an cika wasu sharudda da s**a yi daidai da muradun ƙasar Ɗanyahoo. A lokaci guda kuma, Tuɍ0m yana cikin matsin lamba: a gefe guda akwai ƙarfin sojan lɍ@n ya zama barazana gare shi domin ba su tsammaci haka a farko, wanda ya haifar da gagaruma asarar da ta haifar da manyan matsaloli ga ci gaba da hare-haren Æm0rk@ kan lran, a ɗayan gefen kuma akwai matsin lamba daga masu goyon bayan ƙasar Ɗanyahoo a cikin Æm0ɍk@.

Kwana biyu da s**a wuce, wani babban jami’in Pakistan ya je Tehran babban birnin lran domin isar da saƙonni da buƙatun Æm0ɍk@, amma Iran ta ƙi amincewa da su gaba ɗaya.

Yanzu kuma Qatar ta shiga lamarin. Firaministan Qatar kuma Ministan Harkokin Wajenta, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, ya je Tehran ne domin tattaunawa kan yadda za a yayyafawa zuciyar lran ruwan sanyi rage tashjn rikici da kuma sake buɗe hanyar diflomasiyya tsakanin lɍan da Æm0ɍk@.

Amma idan aka yi la’akari da wasu abubuwa lɍañ za ta iya nacewa a kan wasu muhimman sharuddanta.

Na farko: A ɗage dukkan takunkuman Æm0ɍk@ gaba ɗaya, ba a ɗage wani ɓangare kawai ba.

Na biyu: A kawo ƙarshen takunkumin katangewar ruwa da sauran matsin lambar tattalin arziki, sannan sojojin Æm0rk@ su rage ko su janye daga yankin gaba ɗaya.

Na uku: Batun Mashigin Hormuz ya kasance babban abin da ake takaddama a kai. Iran na son a mutunta matsayinta da ikonta a yankin, yayin da Æm0rk@ ke son mashigin ya kasance hanyar ruwa ta ƙasa da ƙasa wadda kowa zai iya amfani da ita domin ta samu ikon kubuta daga masifar karayar tattalin arziki da ke fuskanto ta. Wannan rashin jituwa na daga cikin abubuwan da s**a kawo cikas ga yarjejeniyar baya.

Na huɗu: Batun kuɗaɗen da ake karɓa daga zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigin na daga cikin muhimman batutuwan da Iran ke son a tattauna.

Na biyar: A yi yarjejeniya ta dakatar da yaƙin wadda za ta haɗa da ɗage takunkumi da kuma warware matsalar Mashigin Hormuz, maimakon a ware batutuwan ɗaya bayan ɗaya.

Me zai faru idan Iran ta amince?

Idan Tehran ta amince ta buɗe Mashigin Hormuz a madadin ɗage wani ɓangare kawai na takunkuman tattalin arziki, hakan zai iya nuna cewa rage matsin tattalin arziki shi ne babban abin da take nema.

Amma idan Iran ta ƙi amincewa da tayin Qatar, hakan zai ƙara nuna cewa tana kallon batun a matsayin babbar matsala ta siyasa, tsaro da kuma ikon yankin, ba wai tattalin arziki kaɗai ba.

A halin yanzu, Qatar da Oman suna ƙoƙarin samar da wata hanya ta wucin gadi da za ta ba jiragen ruwa damar wucewa ta Mashigin Hormuz, ciki har da shirin wata hanyar zirga-zirgar ruwa ta wucin gadi da kuma aikin kawar da nakiyoyi.

Idan diflomasiyyar ta gaza yin nasara fa?

Idan ƙoƙarin Qatar, Pakistan da Oman ya kasa samar da yarjejeniya, akwai yiwuwar abubuwa su ƙara tsananta:

1. Sake barkewar yaƙi:
Amurka da Iran na iya komawa ga ƙarin matakin soja idan diflomasiyya ta gaza.

2. Gulf ya koma filin yaƙi:
Idan rikicin ya sake ƙamawa, ƙasashen yankin za su iya shiga cikin babbar barazana, musamman saboda muhimmancin Mashigin Hormuz.

3. Matsalar mak**ashi ta duniya:
Raguwar zirga-zirgar mai da iskar gas ta Hormuz na iya ƙara matsa farashin mak**ashi tare da jefa tattalin arzikin duniya cikin matsala. Kafin yaƙin, kusan ganga miliyan 20 na mai a rana ke wucewa ta mashigin; yanzu zirga-zirgar ta ragu sosai.

A taƙaice

A yanzu ana ganin gagarumin ƙoƙarin diflomasiyya daga Qatar, Pakistan da Oman domin hana rikicin Iran da Amurka sake komawa yaƙi.

Qatar na da babban sha’awa wajen ganin an buɗe Hormuz, saboda tattalin arzikinta ya dogara sosai da fitar da LNG (Liquefied naturar Gas) ta wannan mashigi. Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya riga ya yi wa fitar da LNG na Qatar babban tasiri.

Saboda haka, ziyarar Qatar zuwa Tehran ba ziyarar diflomasiyya ce kawai ba; **batun Hormuz, takunkuman Amurka, dakatar da yaƙi da kuma makomar tattaunawar Iran da Amurka duk suna kan teburin tattaunawar.**

Inji wani masani

Almujtabah Abubakar

‎Lahaula walaquwwata illah billah 🤔✊‎Iran Allah ya saka da alkhairi. Wlh ko yanzu ƙasar Iran sun fitar da mu kunya. Sun ...
27/08/2026

‎Lahaula walaquwwata illah billah 🤔✊
‎Iran Allah ya saka da alkhairi. Wlh ko yanzu ƙasar Iran sun fitar da mu kunya. Sun ci uwar Æmerîcã da ïsra'læ ona to the highest order. Wannan makamin da kuke gani sunan sa "Razor-thin Messile Persian-etched conformal antenna". Zunzurutun masana kimiyya da fasahar Aerospace technology ne na ƙasar Iran su ka shiga Messile City ɗin su dake Isfahan City su ka ƙirƙire shi. Malam makami ne da yake da maximum bandwidth aerodynamic technology na innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. A yadda s**a ƙera shi, arrowhead ɗin da yake jikin sa hatta Air-Defence RADAR 📡 ma bata iya ganin sa ballantana ma ta iya k**a shi. ‎Sun ƙera shi ne da sinadarin Laser Conductive Copper sannan su ka sake zuba masa zunzurutun fasahar Flexible Micrometer precision saboda ya keta alfarmar Air-Defence technology na waɗancan 'ya'yan karnukan.
‎Iran sun yi amfani da kimiyyar Complex 3D-curved fuselages mai ɗauke da Aerosol Space Optimization technology wanda hatta RADAR 📡 ma bata isa ta k**a shi ba saboda wannan ring circle ɗin da yake da shi.

Abinda ya fi komai ɗaukar hankali a kimiyyar wannan messiles ɗin shine; iska, hazo, duhu ko yankewar transmission na signal ba ya taɓa hana shi sauƙa indai ya bar radius circle ɗin da aka harba shi. ‎Wannan dai ita ce Iran ɗin da kake jin labarin su. Sun shekara sama da dubu 6000 a duniya su na fuskantar maƙiya tun zamanin Annabawa har yau ɗin basu huta ba. A tarihin ƙasar Iran, Khalid bn Walid shi kaɗai ne mutumin da ya taɓa cin su da yaƙi a duniya. Ƙasar Iran typical battle ground ce ta lahaula walaquwwata illah billah. They have survived thousands of war crises beyond human imagination. Ba ruwan su da wani maganar an buɗe campaign ɗin wani ɗan asara ko maganar wani zaɓen cike gurbi irin na jihar Osun. Ba abinda ya haɗa su da karnukan farautar 'yan siyasa ko wasu Delegates 'ya'yan yunwa marasa albarka. They Only deals with absolute human intelligence. Ba abinda ya haɗa su da wata demokradiyyar ku ta asara da mutuwar zuciya shiyasa ko cokali bama iya ƙerawa😒👌

‎kuyimana follow Mujtaba Dan Jarida

@

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar demokraɗiyya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share