02/09/2024
Ɗan Takarar Kujerar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Dala ta Jihar Kano dake Arewacin Najeriya, Hon. Rabiu Musa Abdullahi ya bayyana ƙudirinsa na mayar da ƙaramar hukumar tamkar wata 'yar ƙaramar London matuƙar al'ummar yankin s**a bashi dama Jagorantarsu.
Honarabul Rabiun Alhaji ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da jaridar Kwalla TV Hausa a yammacin yau Litinin, a dai-dai lokacin da ya ke bayyana aniyarsa na tsayawa takarar Shugabancin ƙaramar hukumar tasu ta Dala a ƙarƙashin Jam'iyyar NNPP, a zaɓen da ake shirin gudanarwa a watan Nuwamba me zuwa. A cewar Honarabul Rabiu "Da zarar na sami nasarar ɗarewa kan karagar mulkin ƙaramar hukumar zan bunƙasa Fannin Ilimin, samar da ayyuka da Sana'oin dogaro da kai ga Mata da Matasa, baya ga gudanar da ayyukan raya ƙasa dama maida hankali akan ingana harkar Lafiya a faɗin ƙaramar hukumar"
Honarabul Rabiu dai yayi shura ne a fannin kasuwanci ta yadda shafe kusan shekaru 20 daban-daban, baya ga yadda yake gudanar da harkokin kasuwancin sa a Jihohin Arewacin Najeriya.