08/01/2026
📶 Daya daga cikin manyan dalilan da Nico Williams ya zaba ya ci gaba da zama a Athletic Bilbao maimakon ya koma Barcelona shi ne "aikin da kulob din ya ba shi."
Duk da haka, abubuwa ba su tafi kamar yadda ake tsammani ba: Suna matsayi na 8 a teburin La Liga, maki 14 tsakaninta da wuraren gasar zakarun Turai.
Suna matsayi na 28 a gasar zakarun Turai, da maki 5 kacal a wasanni 6.
Barcelona ta lallasa su a wasan kusa da na karshe na cin kofin Super Cup (5-0).
Duk da kasancewa daya daga cikin mafi kyawun ’yan wasa a tarihinsu na zamani, Los Leones na taka rawar gani fiye da kowane lokaci kuma ba su kusa cimma burin da s**a sanya a farkon kakar wasa ba.