23/03/2025
YANZU-YANZU: Kiristochi a Nijeriya sun Fara tuhumar manyan Fastochi Akan Gaza Bada Amsa a tambayoyin da Baban chinedu yake musu.
Gaskiya pastor, ka bani kunya. Rashin iya bayar da amsa ga tambayoyin da Baban Chinedu ya yi maka na iya sa addinin Kiristanci ya rushe, domin kuna da ilimi fiye da mu. Amma me yasa har yanzu ba wanda ya fito daga cikin ku ya wanke mu daga abin da yake fada?
Dan Allah, pastor, ba wai rashin kunya nake ba, amma wannan abu yana bukatar a kula da shi sosai. Ya dace ku kare addininmu. Idan kuka kasa bayar da cikakkiyar amsa mai gamsarwa, mutane za su fara yi mana gori cewa ba ma san inda muke ba.
Ni dai zan jira. Idan kuka iya bashi amsa mai gamsarwa, zan ci gaba da zama Kirista. Amma idan kuka kasa, hakan yana nufin cewa tun tuni kuna yaudarar mu, kuma dole mu nemo hanyar gaskiya. Babu wanda zai san hanya madaidaiciya kuma ya ki bin ta. Mun dauka cewa Kiristanci shi ne mafita, amma idan muka ga akasin haka, dole mu sake tunani.
Na godai a cewar mabiyin Addinin kirista. Christy jenny .