20/09/2025
Isra'ila ta buƙaci Amurka da ta matsawa Masar kan sabon matakin soji da ta ɗauka a Sinai, wani yankin Masar da ke maƙwabtaka da Isra'ila, inda ta ƙaddamar da makamin kariya daga sama na ƙasar Sin mai suna HQ-9B.
Wannan makami na zamani na iya fatattakar jiragen yaƙi da mak**ai masu linzami daga adadin nisa mai tsawo, lamarin da ya tayar da hankalin Isra’ila wacce ta ce hakan barazana ce ga tsaronta.
Masar ta daɗe tana ƙarfafa iyakarta da Isra’ila da Gaza, abin da ke ƙara tada cece-kuce a yankin.
Shin a ganinku, wannan shiri kariya ne ga Masar ko barazana ga Isra’ila?
📷/: Benjamin Bibi Netanyhu/: Credit [Getty Images]