Nigerian Times Hausa

Nigerian Times Hausa Kafar yada shirye shirye da sahihan labarai kan al'amuran yau da kullum cikin harshen Hausa.

Kamfanin Jafan Yana Aiki Domin Kirkirar Na'urar Wanke MutumWani kamfanin fasahar kere-kere na kasar Japan mai suna Scien...
31/01/2025

Kamfanin Jafan Yana Aiki Domin Kirkirar Na'urar Wanke Mutum

Wani kamfanin fasahar kere-kere na kasar Japan mai suna Science co limited, wanda ya kware wajen kera kayan bandaki da kicin, a baya-bayan nan ya kaddamar da shirin kera injin wanke dan Adam.

Katafaren kamfanin lantarki na Japan Science Co. limited ya baje kolin 'Ultrasonic Bath', injin wanke ɗan adam wanda zai goge, mutum tare da tausa, ya bushar da mutum a cikin mintuna 15.

Kamfanin na fasahar na Japan yana mai alkawarin kammala kera na'urar wanke mutum ta zamani a wannan shekarar ta 2025.

Kamfanin Science Co. Ltd da ke Osaka, wani kamfani da ya yi fice wajen kera sabbin fasahohin zamani da fasahar kayan wanka da dafa abinci, ya sanar da shirinsa na kera na’urar wanke dan Adam a matsayin wani bangare na samfurinsa na Mirable mai suna 'Project Usoyaro'.

Kimiyya ta bayyana cewa makasudin Project Usoyaro ba wai don tsaftace jikin mai amfani ne kawai ba, har ma don shakatawa da sautin kiɗa mai kwantar da hankali da kallon hotunan da ake
nunawa akan ruwa.

A bayyane yake Project Usoyaro aiki ne na shugaban kamfanin Science Co. Ltd. Yasuaki Aoyama, wanda tun yana da shekaru 10 kacal lokacin da aka kaddamar da na'urar wanke tufafi ta Sanyo a Osaka, ƙirƙirar ta burge shi har ya yanke shawarar inganta ta idan ya sami dama.

Sarkin Dutse Mai Martaba Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi Ya Cika Shekara 2 Da Komawa Ga Allah A Rana Mai Kamar Ta Yau 31 Ga ...
31/01/2025

Sarkin Dutse Mai Martaba Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi Ya Cika Shekara 2 Da Komawa Ga Allah

A Rana Mai Kamar Ta Yau 31 Ga Watan Junairu 2023 Allah Ya Karbi Rayuwar Mai Martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Bamalli (CFR).

Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi, CFR. Mutum ne mai ilimin addini da na zamani, ɗankasuwa, kuma mai son kyautatawa jama'arsa. Yana da jajircewa wajen ganin an aikata gaskiya a dukkan hali. Mutum ne mai son tafiye-tafiye. Rubutun da mai karatu zai karanta dangane da rayuwar Mai Martaba Sarki Nuhu Muhammadu Sanusi, an tsakuro shi ne daga littafin da shi Mai Martaba Sarki ya rubuta da hannunsa mai suna "The Days in My Life".

Haihuwa

"An haife ni da safiyar ranar Juma'a 5 ga watan Janairu na shekarar 1945 wanda ya yi daidai da 20 ga watan Muharram na shekarar hijira ta 1364". a garin 'Yar'gaba. Daga wannan gari na 'Yar'gaba, ana iya hango duwatsun garin Dutse fadar masarautar Dutse. Sunan mahaifiyarsa Fatsumatu wacce ta ke ita ce babbar matar mahaifin mai martaba sarki.

Karatu

Mai Martaba Sarki Nuhu Muhammad Sanusi ya ce: "An saka ni a makarantar Ƙur'ani a lokacin da nake da shekarau 4, a cikin wannan ƙauyen. Na fara da koyon harrufan Larabci cikin yaren Fullanci kafin daga baya na koma harshen Hausa. Bayan na gama na koma furuci sannan kuma na k**a Haddar gajerun surorin Al-ƙur'ani mai girma, a ƙarshe kuma na koyi rubuta Al-ƙur'ani a kan allo".

Ya ci gaba da cewa: "An saka ni a makarantar elemantare a ranar 1 ga watan Afirulu na shekarar 1952 aka saka ni a ajin share fagen shiga firamare (pre-primary class) tare da wasu yara maza 16 da mata 7 sa'annina da aka zazzaɓo daga wasu ƙauyukan na yankin Dutse"

Mai martaba sarki ya gama wannan makaranta a shekarar 1956, daga nan kuma sai babbar firamare (senior primary school) da ke Birnin Kudu, daga 1957 zuwa 1959.

Bayan kammala karatunsa kuma a wannan makaranta sai ya wuce zuwa qaramar makarantar sikandire inda ya samu zuwa Gwarzo a shekarar 1960 zuwa 1961. Ya kammala karatunsa na kwalejin horas da malamai (teachers college) daga 1961 zuwa 1966 a garin Kano. Daga nan kuma sai Babbar kwalejin horas da malamai (Advance Teachers College) da ke Kano daga 1967 zuwa 1970.

Bayan kammala wannan makaranta mai martaba sarki ya samu nasarar zuwa Jami'ar Ohi da ke ƙasar Amurka inda ya samu digiri a fannin Kuɗi (Degree in Finance) daga shekarar 1971 zuwa 1974. Ya kuma yi karatu a jami'ar 'Brandford' da ke ƙasar Ingila a shekarar 1977.

Gogayyar Aiki

Bayan Kammala karatunsa da ya yi, mai martaba sarki ya yi ayyuka tare da gurare da dama, daga ciki akwai: ya koyar a makarantar "Kano Staff Development Centre", sai kuma Jami'ar Bayero a matsayin babban laccara (senior lecturer), sai kuma hukumar ALDA a matsayin jami'in kasuwanci (marketing manager), sai kuma 'New Nigerian Development Company (NNDC)', 1976. Daga nan kuma sai 'Mambilla-Coffee and Tea Plantation', 1976 zuwa 1979. Ya zama mamba na hukumar jiragen sama ta Najeriya (Board member Nigerian Airways) a shekarar 1984 zuwa 1985, zamanin mulkin soja na shugaba Muhammadu Buhari. Ya kuma yi aiki da kamfanin Isyaku Rabi'u (Isyaku Rabi'u Group of Companies). Tun daga shekarar 1986 zuwa 1995 sai ya koma mai cin gashin kansa. Sannan ya halarci taron yin dokoki (constitutional conference) daga 1988 zuwa 1989.

Zamowarsa Sarki

Tun kafin zamowarsa sarkin Dutse, mai martaba sarki ya riƙe muƙamin Babban ɗan majalisar sarki, muƙamin da gwamna Ali Sa'adu Birninkudu ya yi masa a shekarar 1992, wanda aka tabbatar da shi a ranar 17 ga watan Mayu na shekarar 1992.

Bayan rasuwar mahaifinsa a ranar Larabar 29 ga watan Nuwamba na shekarar 1995, gwamnan jahar Jigawa na wannan lokacin, Kanal Ibrahim Aliyu ya tabbatar da shi a matsayin sabon sarkin Dutse.

Mutuwa

Allah ya yi wa Sarkin Dutse, Nuhu Muhammad Sunusi rasuwa.

A ranar 31 Ga Watan Junairu 2023 Yana Da Shekaru 79 A Duniya
Sarkin ya rasu ne a Abuja bayan ya yi fama da jinya.

Madogarar Wannan Rubutun

Sanusi N.M. (2010). The Days in My Life. Jigawa Sate Printing Press, Dutse.

Ujorha T. (2015). Emir with passion for golf, good deeds & greenery:

Ya Allah Ya Jikan Sarki Da Rahama Amen 🙏

ZIKIRIN SAFE DA MARAICE An karbo daga Usman bn Affan (SAWW) ya ce: Manzon Allah (SAWW) ya ce: "Babu wani bawa da zai ce ...
31/01/2025

ZIKIRIN SAFE DA MARAICE

An karbo daga Usman bn Affan (SAWW) ya ce: Manzon Allah (SAWW) ya ce: "Babu wani bawa da zai ce –a cikin safiyar kowaneyini, da kuma yammacin kowane dare-:

«بِسْمِ اللهِ الَّذِي لاَ يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الأَرْضِ وَلاَ فِي السَّمَاءِ، وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ».
Ma'ana: "Da sunan Allah wanda wani abu a cikin kasa ko a cikin sama ba ya cutarwa idan an ambaci sunansa, shi mai ji ne masani".

A karanta shi sau uku, = Ba wani abu da zai cutar da mutum.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce karanta wannan addu’a sau uku safe da yamma zai kare mutum, ta yadda babu abin da zai cutar da shi, kuma wata musiba ba za ta same shi ba

Imam Ahmad da Tirmiziy da Ibnu-majah su ka rawaito shi. Tirmiziy ya ce: hadisi ne mai kyau ingantacce (hasan sahih), lamarin kuma k**ar yadda ya fada ne.

Sarauniya Idia: Uwar Al'ummar Masarautar Benin Da Ke Najeriya A Yanzu A ƙarshen karni na 15, masarautar Benin ta faɗa ci...
30/01/2025

Sarauniya Idia: Uwar Al'ummar Masarautar Benin Da Ke Najeriya A Yanzu

A ƙarshen karni na 15, masarautar Benin ta faɗa cikin tashin hankali a lokacin da Oba (Sarki) Ozolua ya rasu.

Ya bar ƴaƴa maza biyu jarumai waɗanda aka ce an haife su a rana guda, wadda ya kawo saɓani kan wadda zai gaje shi bayan mutuwarsa.

Da ɗaya, sunansa Yarima Esigie da ke riƙe da birnin Benin, yayin da ɗayan kuma Yarima Arhuanran, wadda ya kasance a birnin Udo. A matsayinsu na ƴan uwa babu wadda ya yarda guda ya haye bisa karagar mulki, ba da jimawa ba yaƙi ya kaure a tsakaninsu.

Haka nan, yaƙin ya yi mummunar illa ga matsayin masarautar Benin a matsayin mai ikon yanki. Duba da hakan, ƴan ƙabilar Igala da ke maƙwabtaka da su s**a yi amfani da wannan damar s**a aika da mayaƙa ta hanyar kogin Binuwai don karɓe iko da yankunan arewacin Benin.

Sarauniya Idia, ita ce mahaifiyar Yarima Esigie kuma an ce ta mallaki ƙarfin sihiri da kuma ilimin laƙani. Bugu da ƙari, Sarauniya Idia ta taimakawa ɗanta (Esigie) a yaƙin, ta kuma taimaka wajen fatattakar Arhuanran tare da cin galaba a kan mutanen Igala ta hanyar maido da martabar masarautar Benin.

Domin ya nuna martabar mahaifiyarsa, Esigie ya girmama ta, inda ya ba ta laƙabin "Iyoba" (Uwar Sarauniya), muƙamin da ke da matsayi daidai da na babban sarki.

Koyaushe fuskarta ta kasance a rufe da takunkumin fuska na hauren giwa na ƙarni na 16, wadda a halin yanzu ke ajiye cikin gidan adana kayan tarihi na Birtaniya.

Shatin zane guda biyu da ke tsaye a tsakanin idanuwa na nuni ga alamin ƙullin magunguna wadda aka ce masomin samun laƙaninta ke nan.

ECOWAS ta ba shugabannin Mali da Burkina Faso da Nijar kudin tallafi sun ki su karba, amma kuma sun karbi tallafin motoc...
30/01/2025

ECOWAS ta ba shugabannin Mali da Burkina Faso da Nijar kudin tallafi sun ki su karba, amma kuma sun karbi tallafin motocin daukar marasa lafiya 'Ambulances'. Sun ce ba sa sa son a sani, saboda haka za su shafe fentin motocin – Yusuf Tuggar Ministan harkokin wajen Najeriya

DW HAUSA.

Kisan Mutum Maison Zaman Lafiya Na Duniya Mahatma Gandhi 1948A Rana Mai Kamar Ta Yau 30 Ga Watan Junairu 1948 - Bayan ki...
30/01/2025

Kisan Mutum Maison Zaman Lafiya Na Duniya Mahatma Gandhi 1948

A Rana Mai Kamar Ta Yau 30 Ga Watan Junairu 1948 - Bayan kisan Mahatma Gandhi a gidansa. Firayim Ministan Indiya , Jawaharlal Nehru, ya Shaidawa al'ummar kasar yana cewa " Haske ya fita daga rayuwarmu " Ranar da aka kashe Shi ta zama " Ranar Shahidai " a Indiya.

A ranar ga Janairu, 1948, aka kashe Mohandas Karamchand Gandhi, wanda aka fi sani da Mahatma Gandhi. Nathuram Godse wani mai tsatsauran ra'ayin Addinin Hindu ne ya har*be shi a fili, wanda ya harbeshi da arsashi uku a cikin kirjinsa da bindiga mai sarrafa kanta ta M1934 Beretta yayin da ake Addu'ar magariba a lokacin yana Azumi a gidan Birla na Delhi.

Nathuram Godse yana harbinsa ya yi kokarin harbin kansa amma ya kasa harbin kan sa, ya ruga da gudu, yayin da jama'ar da s**a firgita s**a yi ta kururuwa, 'ya kashe shi, ya kashe shi!' kuma jama'a su kai kansa tare da barazanar kashe shi. An yi masa shari’ar kisan kai a watan Mayu kuma aka rata*ye shi a watan Nuwamba na shekara 1949.

An dai haifi Gandhi ne ranar 2 ga watan Oktoban 1869 a matsayin Mohandas Karamchand Gandhi a Porbardar dake Jihar Gujarat. Iyayen sa sun masa aure yana da shekaru 13 tare da Kasturba Makanji wanda s**a haifi yara hudu tare.

Ya karanta aikin lauya a London tsakanin shekarar 1888 zuwa 1891, kana yayi aikin lauya a Afrika ta kudu tsakanin shekarar 1893 zuwa 1915. A shekarar 1922 a matsayin jigo na jam’iyyar NCP yayi kiran bijirewa turawan Birtaniya dake mulkin Indiya abinda ya sa aka k**a shi aka daure shi shekaru biyu.

A shekarar 1930 ya jagoranci wata zanga zangar da aka yiwa lakabi da ‘Salt March’ daga Ahmedabad abinda ya sa aka sake k**a shi aka tsare. A shekarar 1942 ya kira yajin aikin gama gari dan tilastawa turawan Birtaniya ficewa daga Indiya abinda ya sa aka k**a shi aka tsare har zuwa shekarar 1944.

Indiya ta samu yanci a shekarar 1947, yayin da aka yiwa Mahatma Ghandi kisan gilla ranar 30 ga watan Janairu shekarar 1948, kuma mutane sama da miliyan biyu ne s**a halarci jana’izar sa.

ZIKIRIN SAFE DA MARAICE Ayat al-Kursi: Mafi Girman Kariyaأَعُوْذُ بِاللّٰهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيْمِ. اَللّٰهُ لَآ ...
30/01/2025

ZIKIRIN SAFE DA MARAICE

Ayat al-Kursi: Mafi Girman Kariya

أَعُوْذُ بِاللّٰهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيْمِ. اَللّٰهُ لَآ إِلٰهَ إِلَّا هُوَ الْحَىُّ الْقَيُّوْمُ السَّمٰـوٰتِ وَمَا فِى الْأَرْضِ ، و مَنْ ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلَّا بِإِذْ ِهِ ، و يَعْلَمُ . أَيْدِيْهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ , وَلَا يُحِيْطُوْنَ بِشَىٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَ شَآء السَّمٰـوٰتِ وَالْأَرْضَ، وَلَا يَئُوْدُهُۥ حِفْظُهُمَا ، وهُوَ الْعَلِى الْعَظِيمُ.

A'ūdhu bi-llāhi mina-sh-Shayṭāni-r-rajim. Allāhu lā ilāha illā Huwa-l-Hayyu-l-Qayyyum, lā ta'khudhuhū sinatuw-wa lā nawm, lahū mā fi-s-samāwāti wa mā fi-l-arɗ, man dhā'lladhī yashfa'u 'bi-indahū ilhū, ya'lamu ma bayna aydīhim wa mā khalfahum, wa lā yuḥīṭūna bi-shay'im-min ʿilmihi illā bi-mā shā', wasi'a kursiyyuhu-s-samāwāti wa-l-arɗ, wa lā ya'ūduhū ḥifᓓuhumā-Huwa-yulu- ’Aẓīm.

Ina neman tsarin Allah daga Shaidan La'ananne. Lalle ne Allah, bãbu abin bautãwa fãce Shi, Rãyayye, Majiɓincin dukan kõme. Barci ba ya riskarSa. Shi ne da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. Babu wanda ke yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa. Yanã sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu, kuma ba a sani kõme daga ilminSa, fãce abin da so. Gadon mulkinsa ya shimfida sammai da ƙasa, kuma tsarewarsu ba ya gajiyar da Shi. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma. (2:255)

Sharhi

Ayah al-kursi ta fara da 'Allah'. A cewar malamai da yawa, 'Allah' shine sunan Allah mafi girma, kuma shine sunan da aka fi ambata a cikin Alqur'ani, wanda ya bayyana sama da sau 2,500.

Allah' yana nufin *Wanda ake bautawa. Don haka, āyah ta fara da tabbatar da gaskiya mafi girma: cewa Allah shi kaɗai ne wanda ya cancanci a bauta masa.

Sannan ta siffanta Allah da cewa: “Mai Rayayye ne (al-Hayy)”: Wanda ke da dukkan sifofin rayuwa a mafi cikar siffa k**ar ji, gani, sani, iko da sauransu. Baya mutu, kuma ko da ‘karamar mutuwa (barci) ba ya shafarSa. Rayuwarsa cikakkiya ce, kuma Shi kaɗai ne ke rayawa.

Hoto 📷 Wata Yar Kabilar Turkana a Lokori Tanzania 🇹🇿 Mutanen Turkana a Lokori.Kabilar Turkana ita ce al'ummar makiyaya t...
29/01/2025

Hoto 📷 Wata Yar Kabilar Turkana a Lokori Tanzania 🇹🇿

Mutanen Turkana a Lokori.

Kabilar Turkana ita ce al'ummar makiyaya ta biyu mafi girma a Kenya. Wannan al'ummar makiyaya ta ƙaura zuwa Kenya daga Karamojong a gabashin Uganda. Kabilar Turkana sun mamaye yankin Hamadar Turkana da ke lardin Rift Valley na Kenya. Kamar Masai da kabilu, Turkana suna kiwon shanu, awaki da rakuma.

Dabbobi wani yanki ne mai matukar muhimmanci na al'ummar Turkana. Dabbobin su sune tushen samun kudin shiga da abinci. Sai dai kuma fari da ake fama da shi a gundumar Turkana na yin illa ga rayuwar makiyaya.

Kamar Masai da Samburu, mutanen Turkana su na da launin baki sosai. Mutanen Turkana sunayi wa kansu ado da abin wuya kala-kala. Kayan adonsu an yi su ne da ja, rawaya da launin ruwan kasa.

Satar shanu ta zama ruwan dare a gundumar Turkana da kewayen iyakarta da Uganda da Sudan da Habasha da Kabilun da ke zaune a wannan yanki suna yawan fadan kabilanci don nemawa dabbobi ruwa. Satar shanu ya zama ruwan dare gama gari ga makiyaya da ke zaune a sassan Rift Valley da kewaye. Sak**akon yawaitar kananan mak**ai, satar shanu ta kara zama hadari, kuma gwamnatin Kenya ta shiga tsakani wajen warware matsalar.

Tare da yawan jama'a kusan mutane 250,000, yaren Nilotic shi ne Turkana ke magana da shi, kuma sun yi nasarar kiyaye al'adarsu idan aka kwatanta da sauran kabilu a Kenya.

Mazajen Turkana su na Lullube kawunansu da laka, sai a yi musu fentin shudi sannan a yi musu ado da gashin jimina da wasu gashin fuka-fukan tsuntsaye.

Babban tufafin mutanen Turkana shi ne bargon ulu. Irin suturar da mace take sakawa ana sanin matsayinta na aure. An yi amfani da zanen jiki a al'ada don nuna nasara a cikin al'umma. Ana yi wa maza ko mayaƙan da s**a kashe maƙiya zane (tattoo) don nuna abin da s**a yi wa al'umma.

Yawancin mutanen kabilar Turkana suna bin Addinin gargajiya yayin da kashi 5 zuwa 15% Kiristoci ne.

Kabarin Annabi Yusha'u (عليه السلام)Tudun Yusha'u (da turkanci: Yuşa Tepesi ko Hazreti Yuşa Tepesi), wani tsauni da ke g...
29/01/2025

Kabarin Annabi Yusha'u (عليه السلام)

Tudun Yusha'u (da turkanci: Yuşa Tepesi ko Hazreti Yuşa Tepesi), wani tsauni da ke gabar tekun Anadolu na Bosporus a gundumar Beykoz a birnin Istanbul na Turkiyya, wurin ibada ne da ke dauke da masallaci da kabari da aka kebe wa Yusha'u (Turkiyya: Hazreti Yuşa).

Wannan shi ne maqamin Annabi Yusha (عليه السلام), Annabin da ke da kusanci da Annabi Musa (عليه السلام) kuma ya zama shugaban Bani Isra'ila bayan wafatinsa. An san shi da Joshua a cikin Bible.

Yusha (عليه السلام) shi ne babban jikan Annabi Yusuf (عليه السلام), cikakken sunansa Yusha bin Nun bin Afraeem bin Yusuf. Duk da cewa ba a ambace shi da sunansa a cikin Alkur’ani mai girma ba, a wurare biyu.

Bayan Bani Isra'ila sun gudu daga kangin bauta a Masar kuma s**a yi ta yawo cikin hamada na tsawon shekaru 40 Annabi Musa (عليه السلام) ya rasu kusa da Bayt al-Maqdis, wanda aka fi sani da 'Kasar Alkawari'. Yusha (عليه السلام) ya k**a mulki ya jagoranci Bani Isra'ila a hayin Kogin Urdun da kewayen Yariko (wanda aka fi sani da Ariha). Birni ne mai ban sha'awa mai manyan fadoji. Sai da ya kewaye ta har tsawon wata shida, ya jagoranci rundunarsa, ya ci Yake-yake masu yawa.

An ce a lokacin da za su karbe birnin Kudus a ranar Juma'a ne a lokacin la'asar. Faɗuwar rana ta gabatowa wanda zai sa su tsaya sai ranar Asabar (ranar hutu), ma'ana zasu daina yin faɗan. Yusha (عليه السلام) sai ya roki Allah: “Ya Allah ka kiyaye ta daga faduwa”. . Aka tsaya da rana bata fadi ba, har Allah ya bashi nasara.

An karbo hadisi daga Abu Hurairah (رضي الله عنه) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce: “Hakika mutum bai taba hana rana faduwa ba face Yusha (عليه السلام) a maraicen da ya kai hari Bayatul Maqdis."

Baba 'Yar Karo: Labarin wata Bahaushiya da tayi gwagwarmaya tun kafin zuwan turawaCinikin bayi abu ne da ya kasance ruwa...
29/01/2025

Baba 'Yar Karo: Labarin wata Bahaushiya da tayi gwagwarmaya tun kafin zuwan turawa

Cinikin bayi abu ne da ya kasance ruwa dare a arewacin Najeriya a karni na 19 a lokacin turawan mulkin mallaka. Sau da dama akan kai hari kauyuka daban-daban inda ake k**a mutane a gonaki da gidajensu daga baya a sayar da su a matsayin bayi.

Baba wata tsohuwa ce wadda aka haife ta a 1877, a kauyen Karo da ke kusa da Zarewa a tsohuwar daular Usmaniyya wadda ta hada da Zariya da Kano. Yaƙi shi ne hanya mafi sauƙi da mutane suke amfani da shi wajen samun bayi. Mahaifinta manomi ne kuma yana karantar da Kur'ani. Baba ta hadu da wata baturiya mai suna Mary Smith a 1949. Mary ta wallafa littafi a kan gwagwarmayar ruyuwar Baba 'Yar Karo wanda ya zama abin nazari ga masu karantar tarihin Hausawa a zamanin mulkin mallaka.

A wancan zamanin, ana ta gwabza yaki a daular ta Usmaniyya hakan yasa cinikin bayi ya zama ruwan dare. A cikin litafinta, Mary ta bayyana yadda Sarki ke bayar da umurni makada su hau tsibiri su buga gangan domin sanar da mutane cewa masu k**a bayi suna zuwa kuma sai ka ga mutane suna gudu suna shigowa kofar gari domin tsira.

An k**a wasu daga cikin 'Yan uwan Baba a wani samame da aka kai sai dai daga baya an sako su bayan an biya kudi masu yawa na fansa. "Sun kai farmaki gidan kanin mahaifina a tsakiyar dare. Sun sace matarsa mai juna biyu da yaransa guda uku da wasu bayinsa guda goma. Bayan kwanaki 30, mun samu labarin cewa masu satar bayin sun tafi sai mahaifinmu ya ce mu tafi gonar shinkafarsa dake kusa da rafi," inji Baba.

Baba ta ce kullum suna cikin fargaba ne saboda kada masu sace mutane su k**a su kuma su sayar da su a matsayin bayi. Kazalika, Baba ta bayyana cewa a wannan zamanin ba a tilastawa mata auren wadanda ba su so kuma idan mace ba ta son mijinta, tana iya neman saki ba tare da tsoron tsangwama ba. Ta ce tana da wata suruka wadda ta auri maza 11 a rayuwarta. Baba bata taba haihuwa ba har ta rasu a 1951 duk da cewa da auri mazaje hudu a rayuwarta. Mazajen da ta aura sun hada da Duma, Mallam Maigari, Mallam Hassan da Mallam Ibrahim.

A wani ƙoƙarin sa na inganta rayuwar matasa da samar da aikin yi a faɗin jihar Jigawa, Sanata Bababgida Hussaini mai wak...
29/01/2025

A wani ƙoƙarin sa na inganta rayuwar matasa da samar da aikin yi a faɗin jihar Jigawa, Sanata Bababgida Hussaini mai wakiltar Jigawa North West ya halarci taron yaye ɗaliban da ya ɗauki nauyin basu horo na musammam a sana’ar hannu ta Fata da s**a haɗa da ɗinkin takalma da jaka wanda ya gudana a Cibiyar Koyar da aikin Fata da Kimiyya da Fasaha ta Najeriya (Nigerian Institute of Leather and Science Technology).

A yayin yaye ɗaliban, Sanata Babangida ya gwangwaje ɗaliban da sabon keken ɗinki na zamani da kayan aiki da s**a kai Naira Miliyan 3, tare da basu ƙarin Naira Dubu 100 domin ƙara ƙarfafa musu.

Wannan ya zo me mako guda bayan gudanar da aikin ido kyauta da Sanatan ya dauki nauyi a shiyyar Jigawa North West don sauƙaƙawa masu ƙaramin ƙarfi da ke fama da matsalar lalurar ido a yankin.

Sanaya Babangida ya bayyana cewa zai cigaba da ayyukan raya al’umma har sai Jigawa da yi fice tsakanin takwarorin ta wajen cigaba ta kowanne fanni.

Yau Shekaru 80 Da Kubutar Da Yahudawa Daga Sansanin Gwale-gwale na Auschwitz-Birkenau Kisan kiyashin Yahu**dawa ya faru ...
27/01/2025

Yau Shekaru 80 Da Kubutar Da Yahudawa Daga Sansanin Gwale-gwale na Auschwitz-Birkenau

Kisan kiyashin Yahu**dawa ya faru ne lokacin Yaƙin Duniya na Biyu (1939-1945), lokacin da aka kashe miliyoyin Yahudawa saboda aƙidarsu.

A lokacin Yaƙin Duniya na Biyu: Rundunar Sojojin Soviet ta 322 ta ‘yantar da fursunonin Auschwitz-Birkenau. Rundunar Sojojin Soviet ta 322 ta 'yantar da sansanin taro na Auschwitz-Birkenau a ranar 27 ga Janairu, 1945. 'Yancin ya faru ne a lokacin harin Vistula-Oder.

An amince da ranar 'yantar da Auschwitz-Birkenau a matsayin Ranar Tunawa da Holocaust ta Duniya ta Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya.

A wannan rana ta 27 ga watan Janairu aka cika shekaru 80 da 'yantar da sansanin gwale-gwale na Auschwitz da sojojin Na*zi na Jamus s**a yi amfani da shi wajen kisan kimanin mutanen milyan daya da dubu-dari daya a lokacin yakin duniya na biyu.

A Poland mai mutane kimanin 10,000 da Jamus ta kame a shekarar 1939 ta sake masa suna zuwa Auschwitz. A wajen sojojin Jamus na Na*zi sun kafa sansanin kisa mafi girma na Auschwitz-Birkenau tun daga shekarar 1941. Sahihan bayanai da aka samu sun tabbatar da cewa 'yan Na*zi sun halaka kimanin mutane milyan da dubu-dari daya zuwa karshen watan Janairun shekarar 1945 kuma galibi Yahu**dawa amma akwai 'yan Roma da Sinti gami da wasu tsirarun al'uma.

Me aka yi a wajen?

An zabi wajen saboda ya kasance a tsakiyar Turai inda za a iya kai mutane ta jiragen kasa, wannan na daga cikin abubuwan da aka duba.

Kalmar Auschwitz tana tafiya kut-da-kut da korar mutane, an zabi wurin saboda yana tsakiyar Turai, zai zama inda za a yi safarar mutane daga kowane bangare ta hanyar jiragen kasa, domin haka an duba hanyar zuwa."

Jim kadan bayan farmaki dakarun Jamus karkashin shugaban gwamnati Hitila sun kwashe yankunan kasar Poland, inda aka kashe mutane da dama lokacin harbe-harbe a gabashin Poland. Akwai lokacin da aka kashe Yahu***dawa 900 kusa da birnin Riga. Kuma lokacin aka tsara wannan sansani, tun daga shekarar 1942 an kara yawan jiragen kasa da suke kwasar Yahu**dawa daga bisani sai mutanen su bace, wadanda ake kashe**wa a yankunan Poland da aka mamaye.

"Wuri da gwamnati ta tsara aikata laifuka, kuma aka aikata laifin ta hanyar kashe mutane masu yawa, kuma wasu mutanen da aka ware, wato Yahu**dawa, 'yan Sinti da kuma Roma gami da wasu."

Daga bisani an gano cewa galibin jiragen kasa da suke kwaso mutane suna karewa a sansanin Auschwitz wadanda s**a fito daga Jamus da wasu sassan Turai. Jiragen da ake cewa suna dauke da fursunoni sun kasance mutanen da ake kai su inda ake kashe su. Sojojin Tarayyar Soviet a ranar 27 ga watan Janairun 1945 da s**a kwace sansani kafin kawo karshen yakin duniya na biyu.

Su kansu wadanda s**a yi ceton a kofar shiga Auschwitz, matasan sojoji Tarayyar Soviet daga Ukraine da kuma Rasha da sauran jamhuriyoyin Tarayyar Soviet a lokacin, ba su yarda da abin da s**a gani da idonsu ya gani ba. Sun ga abubuwa da yawa da s**a hada da gawawwakin mutanen da suke tsaye kan kafafunsu, gami da kwarangwal na mutanen da suke raye.

Da dama daga cikin wadanda aka tseratar daga sansanonin sun mutu daga baya saboda rashin lafiya sanadiyyar azabar da s**a sha a lokacin da suke a daure. Hatta bayan yakin rayuwa ta yi musu matukar wahala. Da dama daga cikin wadanda s**a rayu sun iske wasu mutanen na rayuwa a muhallansu, wasu kuma sun gaza samun matsuguni. Kasashen duniya ba su nuna aniyar karbar irin wannan dandazon ‘yan gudun hijira ba saboda yawansu.

A yanzu duniya ta amince da girman laifin da aka tafka a lokacin Kisan kiyashi na Holocaust kuma ya zamo misali na irin mummunan hali da Kisan kiyashi ke haifarwa da kuma bayyana irin dabi’u da ke iya haifar da shi.

A ranar 27 ga watan Janairu na kowace shekara, al’umma a Burtaniya na tunawa da kisan kiyashi na Holocaust.

A biranen Jamus da dama irin Kolon, da Stuttgart, da Hamburg, da Wiesbaden gami da Berlin an kafa wuraren tunawa da mutanen da aka kwasa zuwa sansanin da aka halaka su lokacin yakin duniya na biyu.

Ana tunawa da lamarin a wannan rana ce kasancewar a irin ranar ce cikin shekarar 1945 dakarun Tarayyar Soviet s**a ‘yanta sansanin kisan kiyashin ‘yan Na**zi mafi girma na Auschwitz-Birkenau.

Margaret Sanger Matar Da Ta Kirkiro Tsarin IyaliMargaret Sanger ta sadaukar da rayuwarta wajen halasta hana haihuwa da k...
27/01/2025

Margaret Sanger Matar Da Ta Kirkiro Tsarin Iyali

Margaret Sanger ta sadaukar da rayuwarta wajen halasta hana haihuwa da kuma tsarin iyali ga mata a duniya. Sanger ya yi imanin cewa ikon sarrafa haihuwa yana da mahimmanci don kawo ƙarshen talauci..

An haifi Sanger a Ranar 14 ga watan Satumba a shekarar 1879 a jihar New York a kasar Amurka, ta kuma kasance ta sha ɗaya a cikin yaran mahaifinta. Mahaifinta mai suna Michael, haifaffen ɗan kasar Ireland ne mai sana'ar fasa duwatsu. Sun kasance talakawa kuma suna rayuwa a cikin wani ɗan karamin gida da aka ƙera da itatuwa da kuma ƙarafa..

Mahaifiyar Sanger ta samu ciki har sau 18, inda ta ɓarar da bakwai daga ciki. Sanger ta fara ne a matsayin ungozoma mai taimakawa mutanen da ke fama da lalurori da s**a yi tsanani, inda ta haɗu da wata mata da ta mutu kan lalurar ciki da kuma masu zubar da ciki a bayan t**i.

"A lokacin akwai dokoki da s**a hana aike da bayanai ta akwatin gidan waya kan batun tsarin iyali. Akwai kuma wasu dokokin da s**a haramta amfani da kwayoyin hana ɗaukar ciki a jihohi da dama,'' a cewar Elaine Tyler May, farfesa kan Tarihi da Ilimin Amurka a Jami'ar Minnesota, wacce kuma ta wallafa takarda mai suna America and the Pill..Sanger ta jure abubuwan Cocin Katolika, da yake kallon shan kwayoyin hana ɗaukar ciki a matsayin laifi.

Hakkin yin tsarin iyali

A watan Maris din 1914, Sanger ta wallafa takarda mai suna Woman Rebel, wanda ya yi magana kan hakkin mata na yin koyi da tsarin iyali. Ba a daɗe ba, hukumomi s**a haramta amfani da takardar. Daga baya Sanger ta tsere zuwa Ingila saboda tsoron kar a tura ta zuwa gidan yari. A can, ta samu kwarin gwiwa da irin ayyukan Thomas Robert Malthus, wanda ya kalubalanci cewa mutane a duniya ba za su iya riko da ƙaruwar al'umma ba.

Ya bayar da shawarar daukar matakin kariya na kai da jinkirta yin aure. Sai dai 'yan gwagwarmaya da ake kira neo-Malthusians, na matsawa na amfani da kwayoyi. "Ta kuma fara duba wata hanya...tare da cewa tsarin iyali shi ne hanyar zaman lafiya da kuma kaucewa matsalar ƙarancin abinci,'' a cewar Dr Caroline Rusterholz, masaniya kan tarihi a Jami'ar Cambridge da ke Birtaniya, wacce kuma ke mayar da hankali kan al'umma da magunguna da kuma jinsi.

Asibiti na farko

Bayan komawar Sanger Amurka daga gudun hijira da take yi, a ranar 16 ga watan oktoba 1916 sai ta buɗe asibitin tsarin iyali na farko a ƙasar a birnin New York da ya kasance gida ga talakawa da dama da kuma mata masu gudun hijira. An kai samame asibitin kwanaki kalilan da fara aiki, inda aka k**a Sanger.

Duk da haka bata karaya ba, inda ta sake buɗe asibitin kwanaki kaɗan bayan faruwar lamarin, aka kuma sake k**ata tare da zarginta da janyo damuwa cikin al'umma. Bayan ta bayyana a gaban kotu a 1917, an sameta da laifi, inda aka yanke mata hukuncin zaman gidan yari na kwana 30 ko zaɓin biyan tara.

Amma ta zaɓi zaman gidan yari, inda ta rika bai wa fursunoni bayanai kan tsarin iyali. "A lokacin da lamarin ya faru, ta zama shahararriya a Amurka. In da ta shiga yajin aikin cin abinci,'' a cewar wata da ta rubuta tarihin Sanger, Ellen Chesler.

Bayan sako ta, Sanger ta kalubalanci hukuncin da aka yanke mata, sai dai kotu ta yanke cewa likitoci za su iya bai wa mutane shawara kan magungunan tsarin iyali saboda dalilai na lafiya.

Bala'oi

A lokacin da take fama da shari'a a gaban kotu, ta kuma fuskanci bala'o'i daban-daban a rayuwarta. A shekarar 1914, ta rabu da mijinta mai suna William, sannan a 1915, 'yarta ɗaya tilo Peggy, ta mutu lokacin da take shekara biyar. Ta yi soyayya da maza da dama, har da wanda ke bincike kan dabi'un jima'i. Havelock Ellis da H G Wells.

A shekarar 1922, ta auri wani mai harkar mai James Noah H Slee, wanda ya zama ɗaya daga cikin mutanen da s**a marawa gwagwarmayarta baya.

'Yan gwagwarmayar Eugenics

Sanger ta nemi taimako daga 'yan gwagwarmaya da dama da kuma shiga haɗaka da kungiyoyin da ake gani da wuya a amince da manufofinsu. "Ta haɗa kai da yan gwagwarmayar Eugenics... inda ta samu taimakon kuɗi daga wajensu,'' a cewar Rusterholz.

Matalautan da basu da ilimin tsarin iyali'

Gaɓa-ɗayan shekarun 1920 da 1930, Margaret Sanger ta yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashen duniya da dama, inda take ƙarfafa batun tsarin iyali a China da Japan da Korea da kuma India.

A wata wasika da ta rubutawa 'yan gwagwarmayar Eugenics na birnin Landan wadanda s**a tallafa wa ziyarar da ta yi zuwa India a shekarar 1935, ta ce "zimmarta ne na ganin ta sanar da waɗanda basu da ilimin tsarin iyali don su sani.''

Ta tallata wata hoda da ake amfani da shi a Kasar Indiya

Sai dai mutane da yawa sun yi ƙorafi kan hodar, kan cewa ta na kona fuska sannan akwai wahalar amfani da shi matuka, idan ba a haɗa da magani ba. "Hodar tana da karfi a kan tsarin iyali da kuma samun magungunan hana ɗaukar ciki, musamman ga marasa karfi. Sai dai fasahar bata aiki,'' a cewar Sanjam Ahluwalia. Ta kuma haɗu da masu faɗa aji 'yan Indiya da dama, k**ar Mahatma Gandhi da Rabindranath Tagore.

Yayin da Tagore ya marawa tsarin iyali baya, shi kuma Gandhi bai goyi baya ba. Sanger ta yi iyaƙar ƙokarinta, amma bata iya canzawa Gandhi ra'ayi ba. Ƴaƙin duniya na biyu ya tilasta gwagwarmayar tsarin iyali a dukkan bangarori a yankin Atlanta.

Bayan nan, fargabar ƙaruwar al'umma ta bai wa masu ra'ayin na tsarin iyali damar samun kwarin gwiwa. A wancan lokacin, Sanger da ta kasance cikin fushi kan magunguna da ake da su waɗanda kuma basa aiki, daga nan ta fara hankoron ganin an samu wasu hanyoyi masu sauki.

Ta rubuta mafarki da take na ganin ta wallafa wata takarda mai suna ''Magic Pill'' a shekarar 1939. Mace 'yar gwagwarmaya ta farko da ta fara haɗaka da Sanger, ita ce Katharine McCormick, wata hamshaƙiyar attajira da mijinta ya rasu. Ta kuma kasance wadda ta tallafawa binciken. Ta kuma ja ra'ayin masana da dama irinsu Dr Gregory Pincus domin shiga binciken.

McCormick initially ta samar da $40,000. Daga bisani kuɗin sun ƙaru zuwa sama da $1m. Bayan shekara goma, an gama haɗa maganin, amma akwai matsalar gwaji da kuma tabbatar da ingancinsa. A lokacin an haramta zubar da ciki a Amurka. Amma a shekarun 1950, tawagar su Sagner ta kai ziyara zuwa Puerto Rico da Haiti. An yi gwaji kan matan da ke gudun hijira da kuma waɗanda ke gida, duk da cewa da yawa basu san me suke sha ba.

"Hakane, an samu batutuwan cin zarafi. Amma Babu wata ayar tambaya kan hakan. A shekarar 1965, Amurka ta yawaita maganin ga mata masu aure, sannan daga baya ga ɗaukacin mata a 1972. Ƙasashe da dama sun amince su fara amfani da maganin su ma. Sanger ta cika da farin ciki na ganin maganin ya samu karɓuwa kafin mutuwarta a shekarar 1966.

An dai an sha zargin Margaret Sanger da batun nuna wariyar launin fata a shekaru da dama kan haɗakarta da 'yan gwagwarmayar eugenics da kuma ayyuka da ta yi da 'yan asalin Afirka mazauna Amurka. Al'ummomi bakaken fata sun gayyaceta domin ta kafa musu asibitoci. Shirin ta mai suna ''Negro Project'' na da zimmar bayar da shawarwari kan kwayar maganin ne ga al'ummomi baƙaken fata a kudancin Amurka.

Sai dai hakan ya zamo abin ce-ce-ku-ce da baƙaken fatar ƙasar da kuma shan s**a daga masu adawa da zubar da ciki. A lokaci guda, ta jagoranci fara shirin bayar da ilimi kan lafiyar jima'i da zub da ciki da kuma kula da iyali.

Maganin ya zamo a matsayin ɗaya daga cikin magungunan tsarin iyali da aka fi amfani da shi a duniya baya ga kwaroron-roba. A yanzu mata sama da miliyan 150 ne ke amfani da shi.

Mutuwa

Sanger ta mutu ne sak**akon raunin zuciya a ranar 6 ga watan Satumba 1966 a Tucson, Arizona, tana da shekaru 86, kusan shekara guda bayan wani muhimmin hukunci da Kotun Koli ta Amurka ta yanke a Griswold v. Connecticut, wanda ya halatta zubar da cikin da kayyade iyali a Amurka. An yi jana'izar ta a St. Philip's a cikin Cocin Episcopal Hills. An binne Sanger a Fishkill, New York, kusa da 'yar uwarta, Nan Higgins, da mijinta na biyu, Noah Slee.

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nigerian Times Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Nigerian Times Hausa:

Share