Arewa Reporters 24

Arewa Reporters 24 Shafi ne da ya himmatu wajen kawo labarai na gaskiya tare da sharhi akan al'amuran siyasar Najeriya na yau da kullum. Harma Nishadi

Kungiyar Izala Ta Yi Allah Wadai Da Ķìśan Kiyashin Da Sojoji S**a Yi Wa Musulmai A Kaduna Kungiyar wa’azin musulunci ta ...
05/12/2023

Kungiyar Izala Ta Yi Allah Wadai Da Ķìśan Kiyashin Da Sojoji S**a Yi Wa Musulmai A Kaduna

Kungiyar wa’azin musulunci ta Izala tayi Allah wadai da kisan kiyashi na harin wani jirgin sama da aka yiwa al’ummar musulmai a jahar kaduna yayin da suke gudanar da wani taro.

Shugaban kungiyar Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga gwamnantin tarayya da tayi bincike na gaskiya Akan hakikanin abun da ya faru, kuma ta hukunta masu hannu a cikin wannan lamari.

Lamarin de ya faru ne a kauyen Tudun Biri da ke gundumar Afaka a lardin Rigasa a karamar hukumar Igabi, inda aka yi kuskuren kashe musulman da suke gudanar da wani taro tare da jikkata wasu da dama biyo bayan wani hari da jirgin yaki mara matuki na soja ya kai don farautan ‘yan ta’ada.

Sheikh Bala Lau yayi jimami kwarai, ganin yadda daruruwan mutane s**a rasa ransu a wannan lamari. A karshe yayi addu’ar Allah ya Jikan musulmai muminai, ya baiwa wadanda s**a ji rauni lafiya, ya kuma kiyaye faruwar haka a gaba.

JIBWIS NIGERIA

Shugaban sojin kasa ya Lt. General Taoreed Lagbaja ya kai ziyara kauyen Tudun Biri domin ta’aziya da jajantawa al’umma b...
05/12/2023

Shugaban sojin kasa ya Lt. General Taoreed Lagbaja ya kai ziyara kauyen Tudun Biri domin ta’aziya da jajantawa al’umma bisa iftila’in tashin bom da yayi sanadin rasa rayukan Al’umma.

31/08/2023

MANYAN LIKITOCIN DUNIYA GUDA 11 NE

1. Alqur'ani Mai Girma

2. Yawan shan ruwa

3. Bacci wadatacce da daddare

4. Iska mai kyau

5. Tafiyar rabin awa a kasa kullun

6. Abinci mai gina jiki madaidaici

7. Hasken rana

8. Zuma

9. Habbatus Saudah

10. Yarda da kaddara mai kyau koh maras kyau

11. Furta "Laa'ilaaha illallah"

KARIN BAYANI

Idan kayi zargin kanka kace astaga furula

Idan kaji radadi "Alhamdulillahi"

Idan abu yabaka mamaki "Subhaanallah"

Idan kana cikin farin ciki "Salatin Annabi ﷺ"

Idan kana cikin bakin ciki "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"

Idan kaga abun mai ban sha awa kace "Mashaa Allah Tabarakallah"

Ka fara komai da "Bismillahi"

Ka rufe komai da "Alhamdulillahi"

Ina rokon Allah Ya yarda da ni da ku babu komai bayan yardar Sa sai Aljannah In shaa Allahu...

*Kada ka/ki Wuce Baka turawa jama'a ba. Allah Ya sa muna daga cikin masu samun babban rabo ranar gobe kiyama, aameen Ya ALLAHU.*

Address

Abuja
AREWAREPORTERS24

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Reporters 24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share