Jaridar Arewa

Jaridar Arewa Jarida ce ta Online da za ta kawo maku ingantattun labarai na cikin gida Nijeriya, da kuma ƙasashen ƙetare.👉 0912 409 9064
(10)

Al'ummar Zaria sun nuna farin ciki sosai bisa tsayar da Aliyu Cairo a matsayin ɗan takarar  Majalisar Tarayya mai wakilt...
29/05/2026

Al'ummar Zaria sun nuna farin ciki sosai bisa tsayar da Aliyu Cairo a matsayin ɗan takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Zaria. Inda kuma s**a yi kira ga jam'iyyar da kada ta sake yin kuskuren tauye masa nasara, domin hakan na iya sa su zabi jam'iyyar gaba ɗaya a zaɓe mai zuwa.

Ɗan gidan tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Bello El-rufa'i ya ziyarci tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar Shuga...
29/05/2026

Ɗan gidan tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Bello El-rufa'i ya ziyarci tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam'iyyar ADC Atiku Abubakar.

WATA SABUWA: Wike ya yi barazanar kwace filayen otal-otal da wuraren taro da ke ba haramtattun ƙungiyoyi da jam'iyyu hay...
29/05/2026

WATA SABUWA: Wike ya yi barazanar kwace filayen otal-otal da wuraren taro da ke ba haramtattun ƙungiyoyi da jam'iyyu haya

HOTO: Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris (na 2 daga dama a sahu na biyu), yana halartar liyafa...
29/05/2026

HOTO: Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris (na 2 daga dama a sahu na biyu), yana halartar liyafar shekara-shekara da Yarima Mai Jiran Gado kuma Firayim Ministan ƙasar Saudiyya, Yarima Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud, ya shirya a madadin Mai Kula da Masallatan Harami Biyu, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, domin tawagogin gwamnatoci da sauran manyan baƙi na musamman da ke gudanar da aikin Hajji na bana.

Tinubu: Mun Samu Nasarar shimfida tubalin farfadowar Najeriya Yayin cika shekara uku a mulkiShugaban Kasa, Bola Ahmed Ti...
29/05/2026

Tinubu: Mun Samu Nasarar shimfida tubalin farfadowar Najeriya Yayin cika shekara uku a mulki

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa ta samu nasarar shimfida tubalin farfado da tattalin arziki da sake daidaita al’amuran kasa bayan shekaru uku da hawansa mulki.

Tinubu ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar domin cika shekara uku cif a mulkin gwamnatin sa ranar 29 ga watan Mayun 2026.

Shugaban kasar ya ce lokacin da ya karbi mulki a shekarar 2023, Najeriya na cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki, karancin kudaden shiga, matsalar tsaro da kuma tabarbarewar harkokin gwamnati.

Ya ce gwamnati ta dauki matakai masu wahala amma masu muhimmanci domin ceto kasar daga durkushewar tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur da kuma gyaran tsarin musayar kudaden waje.

A cewarsa, Najeriya na kashe kusan naira biliyan 18.4 a kullum wajen tallafin man fetur kafin cire shi, lamarin da ya ce yana hana zuba jari a bangarorin raya kasa kamar hanyoyi, lafiya da ilimi.

Tinubu ya amince cewa matakan da gwamnatin ta dauka sun jawo tsadar rayuwa da wahalhalu ga jama’a, amma ya jaddada cewa sadaukarwar da ’yan Najeriya s**a yi ba ta tafi a banza ba.

“Yanzu Najeriya ta fara samun daidaito kuma tana ci gaba a hankali,” in ji shi.

Shugaban kasar ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya fi samun karfi idan aka kwatanta da shekarar 2023, yana mai cewa kasuwar hannayen jari ta samu gagarumin ci gaba daga darajar kasuwa ta naira tiriliyan 30 zuwa naira tiriliyan 160.

Ya kuma ce gwamnatin sa na gudanar da manyan ayyukan hanyoyi fiye da kilomita 2,700 a sassan kasar nan, ciki har da titin Lagos-Calabar Coastal Highway da Sokoto-Badagry Super Highway da kuma hanyar Abuja zuwa Kano.

A bangaren mai da gas, Tinubu ya ce gyare-gyaren da gwamnati ta yi sun jawo sabbin jarin biliyoyin daloli tare da bunkasa matatun mai na cikin gida domin rage dogaro da shigo da man fetur daga kasashen waje.

Game da wutar lantarki, shugaban kasar ya ce gwamnatinsa na kokarin magance matsalolin da s**a dabaibaye bangaren tsawon shekaru ta hanyar inganta layukan sadar da wuta da kuma zuba jari a makamashi.

A bangaren noma kuwa, Tinubu ya ce gwamnati ta tallafa wa miliyoyin manoma da iri, taki, injina da hanyoyin samun rance domin bunkasa samar da abinci da rage tsadar rayuwa.

Haka kuma ya ce Asusun Lamunin Dalibai na Najeriya ya taimaka wa sama da dalibai miliyan 1.5 da kudade sama da naira biliyan 282 domin samun damar ci gaba da karatu.

Shugaban kasar ya ce gwamnatin sa na ci gaba da gina gidaje masu araha a jihohi daban-daban tare da samar da dubban ayyukan yi ga matasa.

Dangane da tsaro, Tinubu ya ce jami’an tsaro sun kara kaimi wajen yaki da ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka, yana mai cewa an fara samun saukin matsalar tsaro a wasu yankuna.

Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da hada kai tare da nuna hakuri da fatan alheri ga kasa.

“Dole mu fifita hadin kai a kan rarrabuwar kawuna, da fata mai kyau a kan yanke kauna,” in ji shugaban kasar.

Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin ganin an rage tsadar rayuwa tare da samar da karin damammakin ayyukan yi da bunkasa kasuwanci.

29/05/2026

TSOHON AJIYA: Martani Marigayi Idris Dutsin Tanshi Kan Shigar Farfesa Isa Ali Pantami Cikin Siyasa...

An Ɗauki Wannan Hoton A Rana Iran Ta Yau 29 Ga Watan Mayu 2015 Yau Shekaru (11) Kenan, Lokacin Da Marigayi Muhammadu Buh...
29/05/2026

An Ɗauki Wannan Hoton A Rana Iran Ta Yau 29 Ga Watan Mayu 2015 Yau Shekaru (11) Kenan, Lokacin Da Marigayi Muhammadu Buhari Ya Karɓi Rantsuwa A Birnin Tarayya Abuja.

Jam’iyyar NDC za ta tabbatar da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, a matsayin dan takararta na shugaban kasa a yau...
29/05/2026

Jam’iyyar NDC za ta tabbatar da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, a matsayin dan takararta na shugaban kasa a yau Juma’a, bayan ya kasance dan takara daya tilo da ya nemi tikitin jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Moses Cleopas, ya bayyana cewa duk da matsalolin sufuri da rashin jiragen sama sakamakon hutun Babbar Sallah, jam’iyyar za ta gudanar da zabukan fidda gwani na gwamnoni, ‘yan majalisar tarayya da na jihohi a fadin jihohi 36 da Abuja kamar yadda aka tsara.

Jam’iyyar ta kuma gargadi hukumomin gwamnati da jami’an tsaro da kada su shiga harkokin zaben fidda gwani ba tare da izini ba, tana mai cewa duk wanda ya karya ka’ida zai fuskanci hukunci. Cleopas ya bukaci mambobi da masu neman mukamai da su kasance masu zaman lafiya tare da gujewa rikici yayin gudanar da zaben.

Cewar an samu ɓarkewar wata cuta a aikin Hajjin bana duk farfaganda ne Saudiyya ta ƙaryata hakanMahukunta a Saudiyya sun...
29/05/2026

Cewar an samu ɓarkewar wata cuta a aikin Hajjin bana duk farfaganda ne Saudiyya ta ƙaryata hakan

Mahukunta a Saudiyya sun tabbatar da cewa an gudanar da aikin Hajjin bana lafiya ba tare da fuskantar wata barazanar ɓarkewar ko wace irin cuta ba.

Ministan tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa mai ritaya ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Tinubu ta samu maki 65 zuwa...
29/05/2026

Ministan tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa mai ritaya ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Tinubu ta samu maki 65 zuwa 70 kan sha'anin tsaro cikin shekaru uku da fara mulkinsa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Uwargidan tsohon Shugaban ƙasa Aisha Buhari tare da ɗanta Yusuf Buhari ya yin da take gyara masa babbar riga da ya saka ...
29/05/2026

Uwargidan tsohon Shugaban ƙasa Aisha Buhari tare da ɗanta Yusuf Buhari ya yin da take gyara masa babbar riga da ya saka bayan ya kammala shirin fita Hawan Sallah tare da tawagarsa matsayinsa na Talban Daura.

Address

Abuja

Telephone

+2349124099064

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar Arewa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jaridar Arewa:

Share

Category