27/01/2023
Jifan Shugabanni Ba Mafita Bace Ga Mu Al'ummar Arewa.
Banji dadin yadda akayi hayar wasu matasa a jahar katsina s**ai rashin da'a ga shugaba Buhari ba ayau, bayan isar jahar dan taya al'ummar jahar murnar bude sabuwar gadar kasa, karkashin jagoranci na gwamnan jahar Aminu Bello Masari.
Yan uwana matasa ni a fahintata, yanzu lokacine daza mu cire kabilanci, addini bangaranci, ko jam'iyar siyasa wajen zaben shugaba. Mun gwada duk abubuwan nan amma bamu ci riba ba.
Idan har muka ji tausayin dan takara Wai don ya dade yana neman shugabancin ba tareda la'akari da iyawar gudanar da shugabacin ba, to wallahi zamu dawo abin tausayi.
Haka zalika idan muka ce kudi Dan takara zai bamu kafin mu goyi bayansa ko kuma mu kada masa kuri'a, to mu sani fa, mun rigaya mun sayar da 'yancinmu da na kananan yara wa'yanda basu isa zabe ba akan kudin nan da muka amsa.
Mu tsaya da kyau mu yiwa kanmu karatun ta natsu mu goyi bayan Mai son cigaban Najeriya, Mai kuma iya kawo cigaban koda kuwa shi dan wani yanki ne, koda kuwa shi dan wani addini ne, koda kuwa dan wani party ne. Kukan kurciya jawabi!!!
Tafawa Balewa, Ahmadu Bello, Eyo Ita, Michael Athokhamien Imoudu, Joseph Sarwuan Tarka, da dai sauransu sun sadaukar da rayuwarsu wajen gina wannan kasa da samar mata martaba a idon duniya, to lallai tarihi ba zai yafe mana ba idan mu ka Yi fatali da ginshikin da s**a ginata.
Ishaq Sh*tu Daneji
26/January/2023.