Africa Hausa TV

Africa Hausa TV TASHACE TA HAUSA ZALLAH DA ZATA RINGA KAWU MUKU SHIRYE-SHIRYEN KASAR HAUSA DAMA AFRICA BAKI DAYA

Innalillahi wa Inna ilaihi Raju un.Yanzu Yanzu gobara ta tashi a Acikin maqabar ta ta Cikin Garin Gashua Bade LGA Yobe s...
25/04/2025

Innalillahi wa Inna ilaihi Raju un.

Yanzu Yanzu gobara ta tashi a Acikin maqabar ta ta Cikin Garin Gashua Bade LGA Yobe state.

15/04/2025

DUNIYA NA SAFIYAR YAU 15/04/2025

Africa Hausa TV

14/04/2025

DUNIYA NA SAFIYAR YAU 14/04/2025 RADIO HAUSA TV

Mutum takwas Sun mutu bayan da motarsu ta taka nakiya A Jahar BornoAfrica Hausa TV
13/04/2025

Mutum takwas Sun mutu bayan da motarsu ta taka nakiya A Jahar Borno

Africa Hausa TV

An sha mamaki bayan sace mota daga ofishin Nuhu Ribadu a Abuja.An sace motar yayin da ake sallar Juma'a a masallaci da k...
12/04/2025

An sha mamaki bayan sace mota daga ofishin Nuhu Ribadu a Abuja.

An sace motar yayin da ake sallar Juma'a a masallaci da ke Abuja.

Rundunar ƴan sanda ta dauki matakai domin zakulo barayin da s**a yi satar.

Sojoji sun tarwatsa yan darika masu zagayen maulidi a Potiskum-- Hamza Abdullahi Guri Da safiyar yau Asabar ne gamayyar ...
12/04/2025

Sojoji sun tarwatsa yan darika masu zagayen maulidi a Potiskum

-- Hamza Abdullahi Guri

Da safiyar yau Asabar ne gamayyar makarantun Islamiyoyi na cikin garin Potiskum hade da daruruwan masoya Manzon Allah (s) s**a fito zagayen Mauludin haifuwar Annabin rahama, Muhammad (s) a Potiskum, amma Sojoji s**a tarwatsa su.

Yadda abin ya faru shine, makarantun Islamiyoyin sun taru ne a kofar mai martaba Sarkin Fika, Alhaji Muhammadu Abali Ibn Muhammad Idriss, suna haduwa kafin su fara zagaya garin, kamar yadda s**a saba shekara da shekaru. Suna tsaye kwatsam sai ga motocin Sojoji sun nufo su, da zuwan su kawai sai s**a fara dukan su, suna farfasa Keke Napep, da kuma duk wani abin hawan da yake dauke da hoton Shaikh Ibrahim Inyass ko Nasiru Kabara.

Kan kace kwabo, sai guje guje ya barke ta ko ina, inda yara dayawa s**a dinga gudu suna barin kayayyakinsu, yanzu haka an tara daruruwan takalman jama'a a kofar fadar Sarkin Fika.

Danna👉 Africa Hausa TV sannan Kayi danna Follow domin Samun Sababbin Labarai DUMI-DUMI

Da sanyin safiyar yau Asabar aka iske wani mutum da ya hallaka kanshi da kanshi ta hanyar rataya a Doubeli Junction dake...
12/04/2025

Da sanyin safiyar yau Asabar aka iske wani mutum da ya hallaka kanshi da kanshi ta hanyar rataya a Doubeli Junction dake Jimeta.

Kawo yanxu ba'a kaiga gano waye Mutumin ba, kokuma dalilin aiwatar da hakan. Rundunar Yan Sandan Jahar Adamawa ta kaddamar da binchike.

Africa Hausa TV

12/04/2025

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake kiran SIM Fubara da suna Gwamnan Jihar Ribas duk da dai gwamnan ya sabawa ra'ayin Nyesom.

Africa Hausa TV

Ministan harkokin cikin gida na tarayyar Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce gwamnatin kasar za ta fara aiwatar da sabuwa...
12/04/2025

Ministan harkokin cikin gida na tarayyar Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce gwamnatin kasar za ta fara aiwatar da sabuwar manufar dakile masu karya dokar wa’adin zama cikin kasar, inda daga watan Agusta mai zuwa za a fara cin tarar wadanda s**a wuce wa’adin bizarsu a cikin kasar dalar Amurka 15 a kullum.

Africa Hausa TV

Da Alamufa Manyan AREWA Sun Fara farkawa daga Baccin das**a jima Sunayi, Allah yasa mudace 🙏🙏🙏
12/04/2025

Da Alamufa Manyan AREWA Sun Fara farkawa daga Baccin das**a jima Sunayi, Allah yasa mudace 🙏🙏🙏

12/04/2025

DUNIYA NA SAFIYAR YAU 12/04/2025 RADIO HAUSA TV HAUSA

Yadda jihohi 19 na Arewa ke fama da bashin tiriliyan 1.25 na cikin gida da dala biliyan 1.71 na wajeHukumar kula da basu...
10/04/2025

Yadda jihohi 19 na Arewa ke fama da bashin tiriliyan 1.25 na cikin gida da dala biliyan 1.71 na waje

Hukumar kula da basuss**a ta Najeriya ta bayyana cewa jihohin Arewa 19 da babban birnin tarayya Abuja, ana binsu kimanin Naira tiriliyan 1.25 na cikin gida da Dala biliyan 1.71 na ƙasashen waje ya zuwa ga ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 2024.

Bayanan sun nuna cewa a yayinda jihar Kaduna ta kasance ta farko a jerin jihohin da s**a ciwo bashi a ƙasashen waje, jihar Bauchi ita ce ta ɗaya a cikin jerin jihar da ta fi kowace cin bashin cikin gida.

A cewar hukumar, bashin cikin gida ya yiwa jihohin katutu, inda ake bin jihar Bauchi Naira biliyan 143.9 a yayinda jihar Benue da Niger ana binsu biliyan 120, inda jihar Kaduna na fama da dala miliyan 625.

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Africa Hausa TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share