
02/09/2025
GWAMNATIN TINUBU TA KADDAMAR DA GIDAJEN ZAMA GA JAMI'AN YAN SANDA NIJERIYA A JIHAR KANO
Shin ko kun san cewa kwanan nan ne gwamnatin Tinubu ta kaddamar da sabbin rukunin gidajen zama da sauran ababen more rayuwa ga jami’an ‘yan sandan Najeriya a Kano?
Kayayyakin da s**a hada da gidaje guda 300, katafaren ofisoshi 48, dakin ajiye makamai, bita na injiniyoyi da wuraren ibada, babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun ne ya kaddamar da aikin a ranar 6 ga watan Agustan 2025. Wadannan sabbin gine-ginen na nuna wani gagarumin ci gaba ga jin dadin ‘yan sanda.