19/07/2025
Ful'ani sun sake kai hari Bukuyum, sun kashe mutum 11 yau Asabar😭
Ful'ani band'its sun sake kashe wasu manoma 10 tare da sace wasu da dama a safiyar yau a Zamfara
Ƴan ta'adda masu dauke da makamai sun kafa shingen bincike ba bisa ka'ida ba a safiyar yau da misalin karfe 8:30 na safe, a tsakanin al'ummomin Gada da Kairu na gundumar Kyaram, a karamar hukumar Bukuyum ta Jihar Zamfara.
Kafa wannan shingen shingen binciken ababen hawa na haramtattun 'yan bindiga da safiyar yau, ya biyo bayan awanni 12 kacal da sace sama da mutum dari daga cikin fararen hula da ba su ji ba su gani ba a yankin, wanda aka yi a ranar Juma’a da daddare.
Sahel24 Tv ta ruwaito cewa, wad'ɗanda s**a tsere daga harin da 'yan gudun hijira daga Kairu da ke sansani a garin Daki Takwas sun kai rahoto zuwa sansanin sojoji mafi kusa da su da ke Danmarke, wanda bai kai kilomita 25 daga inda aka kafa shingen ba. Sai dai duk da hakan, alamu sun nuna cewar ba su samu wani taimako ba.
Ƴan uwa da abokan arziki na wadanda aka kashe ba su da damar zuwa neman sauran gawarwakin. Manoma goma (10) da aka kashe yayin harin tuni aka binne su ba tare da wani shiri ba.
Muna godiya ga Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto Jibwis Nigeria HQ Nigerian Army Amnesty International Dauda Lawal Dr Ibrahim Abdullahi Gobir PhD.MFR.CON Dr. Abubakar Isa Gombe Sheikh Murtala Bello Assada Sokoto