14/07/2026
Gwamnatin Tarayya ta buɗe rajistar CAC kyauta ga Kananan Masana’antu 250,000
Daga Aliyu Samba
Gwamnatin Tarayya ta buɗe ƙofar neman rajistar kasuwanci ta Corporate Affairs Commission (CAC) kyauta ga ƙananan 'yan kasuwa 250,000 a faɗin ƙasar nan ƙarƙashin shirin haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Bunƙasa Kananan da Matsakaitan Masana'antu ta Nijeriya (SMEDAN) da CAC.
Shirin, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi, na da nufin cire nauyin kuɗin rajistar kasuwanci ga masu ƙananan sana'o'i domin ƙara shigar da su cikin tsarin kasuwanci na hukuma.
Masu cin gajiyar shirin za su samu rajistar Business Name a CAC ba tare da biyan kuɗin rajista ba, domin Gwamnatin Tarayya ce za ta ɗauki nauyin kuɗaɗen rajistar.
An sanar da shirin ne a yayin bikin karrama fitattun MSMEs karo na takwas da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar 27 ga Yunin 2026.
Baya ga rajistar CAC kyauta, waɗanda aka zaɓa za su amfana da horaswa kan gudanar da kasuwanci, tallafin bunƙasa sana'o'i da kuma samun damar shiga shirye-shiryen da za su taimaka wajen faɗaɗa kasuwancinsu.
Yadda ake neman shiga
Masu kasuwancin da ke son cin gajiyar shirin su bi waɗannan matakai:
- Shiga shafin yanar gizon SMEDAN domin yin rajista portal.smedan.gov.ng
- Buɗe sabon asusu ta hanyar cike sunanka, adireshin imel, lambar waya da kalmar sirri.
- Cika bayanan kasuwancinka daidai.
- Idan an tambaye ka ko kasuwancin yana da lambar rajistar CAC, zaɓi "No" idan ba ka da ita.
- Duba bayanan da ka cika domin tabbatar da daidaitonsu, sannan ka tura.
- Jira saƙon tabbatarwa daga SMEDAN idan an amince da buƙatarka.
Haka kuma, waɗanda s**a riga s**a yi rajista a bayanan SMEDAN amma ba su da rajistar CAC na iya samun cancantar shiga shirin kai tsaye.
SMEDAN za ta tuntubi duk wanda aka amince da shi domin sanar da shi matakan da zai bi na kammala rajistar Business Name kyauta a CAC.
Shirin ya biyo bayan yarjejeniyar haɗin gwiwa da CAC da SMEDAN s**a sanya domin yi wa ƙananan sana'o'i 250,000 rajista a hukumance a faɗin Najeriya.
A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, manufar shirin ita ce rage wa ƙananan 'yan kasuwa nauyin kuɗin rajista tare da ba su damar shiga tsarin bankuna da sauran tsare-tsaren kasuwanci na hukuma, domin bunƙasa harkokin kasuwanci da tattalin arziƙin ƙasa.