
24/05/2025
Labari Da Duminsa; Sojoji sun bayyana nasarar bindige ƴan bindiga 21 a dajin Ruwangodiya sun kwato makamai da yawa
Rundunar sojojin Nijeriya ta bayyana nasarar da dakarunta na Operation Fansan Yamma, s**a samu na fatattakar yan bindiga a yankin ƙaramar hukumar Faskari jihar Katsina
Kamar yadda Katsina Daily News ta ci karo da rahoton da rundunar da fitar a yau, ta bayyana cewa a yau Jumu'ah jami'an nata sun yi nasarar fatattakar yan bindiga da yawansu ya kai 21, yayin da wasu da s**a ji ruwan wuta s**a nitse a cikin ruwa, wasu kuma s**a arce da mugun raunuka na bindiga, a yankin Ruwangodiya ta ƙaramar hukumar Faskari
Haka kuma sun bayyana kwato makaman bindigu da alburusai gami da babura da dama yayin harin