05/06/2024                                                                            
                                    
                                                                            
                                            MAI GIRMA MATAR GWAMNAN JIHAR KEBBI, DAKTA NAFISA NASIR IDRIS TAYI BIKIN RANAR TSAFTAR MATA A DUNIYA NA SHEKARAR 2024 TARE DA DALIBAI MATA NA COMPREHENSIVE SECONDARY SCHOOL ARGUNGU. 
SANARWA
Mai girma Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nafisa Nasir Idris, ta yi bikin ranar tsaftar Mata ta duniya na shekarar 2024 tare da daliban makarantar sakandare ta 'yan mata ta Argungu, wanda aka gudanar a makarantar. 
A jawabin Mai girma Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nafisa Nasir Idris ta ce manufar bikin wannan rana a fadin duniya shi ne wayar da kan mata kan mahimmancin tsafta a lokacin al’ada domin su kare kansu daga kamuwa da cututtuka masu yaduwa. Ta yi kira ga ’yan matan makarantar da su kasance da dabi’ar tsafta a kowane lokaci, su kuma dauki karatunsu da muhimmanci. 
A nata jawabin kwamishiniyar ilimi na matakin sakandire Dakta Halima Muhammad Bande ta yi kira ga daliban da su kula da abin da za’a koya musu baya ga kula da karatunsu tare da girmama malamansu. 
A cikin sakonnin fatan alheri, uwargidan Sakataren gwamnatin Jihar Kebbi, Hajiya Asma’u Alkali, Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban jama’a ta Jihar Kebbi, Hajiya Halima Hassan Kamba da shugabar kungiyar mata ta ANCOPPS, Hajiya Salamatu Bala Tafida, sun yi kira ga Daliban dasu kasance masu kwaikwayon kyawawan halaye.
A jawabinta na godiya shugabar makarantar, Hajiya Hauwa’u Haliru Sarki ta godewa Mai girma Matar Gwamnan bisa yin bikin ranar a makarantarta da kuma yadda take tallafawa mata da yara a jihar, inda ta lissafo wasu daga cikin kalubalen da ake fuskanta a makarantar tare da yin kira ga Mai girma Matar Gwamnan da ta taimaka wajen magance su. 
Muhimman abubuwan da s**a faru a wajen taron sun hada da karatun Alkur'ani mai girma, gabatar da wasan kwaikwayo, tallafin naira miliyan daya da Alhaji Khairullah Abdullahi ya bayar ga daliban da aka yaye dalibai 234, da jawabin tsafta da gabatar da kayayyakin tsafta ga kowane dalibi wayanda s**a hada da,  man goge baki, buroshin goge baki, sabulu na wanka, sabulu na wanki da sauransu.
Tun farko dai Mai girma Matar Gwamnan ta kai ziyarar ban girma ga Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera a fadarsa. Dakta Nafisa Nasir Idris ta shaida wa sarkin cewa manufar ziyarar ita ce wayar da kan dalibai mata kan mahimmancin tsafta a wani bangare na bikin ranar tsaftar Mata ta duniya a shekarar 2024. 
A nasa jawabin, mai martaba Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera, ya yabawa Mai girma Matar Gwamnan bisa wannan ziyara da kuma shirya taron a Argungu. Ya yabawa gwamnatin Kauran Gwandu bisa gyarar da aka yi na gyara dukkan fadodin sarakunan hudu tare da yi masa addu’ar Allah ya saka masa da alheri. 
Sa hannu;
Ibrahim Mahe
Babban Mataimaki na Musamman ga Matar mai girma Gwamnan Jihar Kebbi, Dr Nafisa Nasir Idris