01/05/2025
AMFANIN SHAN SIGARI GUDA UKU ( 3 )
(Ka karanta har karshe)
1. Masu shan Sigari basa Tsufa!
2. Kare (Dog) bazai iya cizon Masu shan Sigari bah!!
3. Ɓarayi bazasu iya shiga Gidan Mai shan Sigari bah ayayinda yake bacci.!!
MEYASA, MEYE DALILI ?
1.Masu shan Sigari basa Tsufa> Saboda zasu mutu tun suna ƙankanarsu, ( Matasansu ) sakamakon lalacewar huhunsu kamar yadda ma'aikatar lafiya ta gargaɗa.
2. Kare ( Dog ) bazai iya cizon Masu shan Sigari bah!> kawai saboda lokacin da huhunsu ta lalace ( masu shan Sigari ) dole ne su koma tafiya tareda sandar dogaro ( adurkushe ) kowanne lokaci. Kuma Shi Kare yana tsoron Mutane masu rike da sanda a hannu, dan haka bazai iya zuwa ko kusa dasu bah .
3. Ɓarayi bazasu iya shiga Gidan Masu shan Sigari bah ayayinda yake bacci da Daddare > saboda kowanne lokaci Masu shan Sigari suna cikin tari , basa iya bacci cikin natsuwa . Ɓarayi kuma hakan na iya razanar dasu su dauka idonsu farke.
Har Idan wadannan fa'idojin sunyi maka toh Kacigaba da shan Sigari ko kuma kabari.
In Kunne Yaji Jiki Ya Tsira