22/03/2025
Gwamantin Jihar Borno A ƙarƙashin Jagorancin Kwamishinan mata Ta Jihar Borno Ta Shigar da ƙara A Kotu domin nemawa yarinyar da aka zalunta hakkin ta k**ar yadda doka Ta tanada
Gwamnatin Jihar Borno ta dau matakin gaggawa na shigar da kara a kan Mamman Sheriff da matarsa, wadanda aka k**a a faifan bidiyo suna azabtar da wata yarinya a Pompomari Bypass, Maiduguri. Bidiyon, wanda ya karade kafafen sada zumunta Bayan Ahmed Baba Dikwa ya wallafa shi, ya nuna Mamman Sheriff yana dukan yarinyar da karfi, Tare da goyon bayan matarsa. Rahotanni sun tabbatar da cewa an ci zarafin yarinyar ne kawai don ta shiga harabar Gidansu domin daukar mangoro bayan dawowa daga makaranta.
Bayan samun labarin lamarin, Hukumar Tsaro ta NSCDC, reshen Jihar Borno, ta gaggauta cafke Mamman Sheriff da matarsa, kafin daga bisani ma’aikatun da abin ya shafa su shiga cikin lamarin. Gwamnatin Jihar Borno ta tabbatar da cewa an dau matakin shari’a, inda aka hada gwiwa da Ma’aikatar Harkokin Mata da Cigaban Al’umma, Ma’aikatar Ilimi, da kuma Ma’aikatar Shari’a don tabbatar da adalci.
Ko da yake tana wajen gari, Kwamishiniyar Harkokin Mata da Cigaban Al’umma, Hon. Zuwaira Gambo, ta hanzarta tura tawaga karkashin jagorancin jami’ar kula da jin dadin al’umma, Asabe Muhammad (Yar Bauchi), don bibiyar lamarin. Tawagar ta ziyarci Hedikwatar NSCDC reshen Jihar Borno, inda s**a gana da Mataimakin Kwamandan Hukumar, Obi Ndubisi, da jami’in bincike, Peter, domin tabbatar da cewa ana tafiyar da shari’ar bisa doka.
An tabbatar da cewa Ma’aikatar Shari’a ta karbi shari’ar don gurfanar da wadanda ake zargi, yayin da Ma’aikatar Ilimi ta dau matakan da s**a dace dangane da lamarin. Hukumar NSCDC ta ba da tabbacin cewa za a tabbatar da hukunci mai tsanani ga wadanda s**a aikata wannan danyen aiki, domin adalci ya tabbata.
A gefe guda kuma, Gwamnatin Jihar Borno ta samar da taimakon gaggawa ga yarinyar da iyalanta. A halin yanzu tana samun kulawar lafiya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), inda Dr. Lawan Bukar Alhaji ke daukar nauyin jinyarta. Bugu da kari, Hon. Zuwaira Gambo ta bayar da umarnin raba kayan tallafi ga iyayenta, wanda ya hada da **Dignity Kit, buhun shinkafa mai nauyin 25kg, buhu biyu na garri mai nauyin 25kg kowanne, da tallafin kudi.**
Iyayen yarinyar sun nuna matukar godiyarsu ga Gwamnatin Jihar Borno, Hukumar NSCDC, da ma’aikatun da s**a sa hannu wajen daukar mataki cikin gaggawa. Sun jinjinawa Gwamna Babagana Umara Zulum bisa jajircewarsa wajen kare hakkin yara da duk masu rauni a jihar, tare da tabbatar da cewa duk wanda ya aikata laifi irin wannan ba zai tsira ba.
Wannan matakin da Gwamnatin Jihar Borno ta dauka ya kara tabbatar da manufarta na rashin amincewa da cin zarafin yara, tare da aikawa da sako mai karfi cewa duk wanda ya aikata hakan ba zai kubuta ba. A karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum, adalci zai ci gaba da tabbata a jihar.
KBC Hausa