13/05/2025
KASHE MAHAIFIYATA AKA YI A ASIBITIN KOYARWA NA ABUBAKAR TAFAWA BALEWA BAUCHI (ATBUTH).
Hakika duk wanda kwanansa ya kare babu mai iya kara masa ko da sekon daya, amma tabbas mutane da dama na rasa rayuwarsu a asibitoti sak**akon sakaci, musamman na wasu ma'aikatan jinya.
A ranar 6/2/2025 bayan shafe kwanaki 12 a ATBUTH Bauchi, an shiga da mahaifiyata sashen tace jini (Renal Center ) na wannan asibitin a karo na 4, kafin hakan a wannan ranar likitoci da dama sun zo sun duba ta tana zaune kan gado a hakan ni ma na dawo daga karbar sak**akon wani gwaji na same ta, a wannan lokacin muka yi hira sosai da ita, ta fadamin yadda s**a yi da likitocin da s**a duba ta sannan ta sa aka ba ni takardar da aka rubuta na zuwa tace jini. Daga nan na tafi biyan kudin wannan aikin, wanda kafin na dawo har an tafi da ita Renal Center.
Bayan na dawo sai na wuce warin Renal Center din, sai na samu dukkan yan uwana maza da mata a wari, sun ce wadda take aikin ta hana kowa zama a warinta. Ko a lokacin kuma na samu ita wannan ma'aikaciyar a waje tana ta tadi da wasu, alhali kuma ta daura maman namu kan na'urar tace jini. Ashe a wannan lokacin robar da jinin ke kai komo ta cikinta ta zare, duk jininta ya kwarare a kasa😭 ita kuwa tana waje tana tadin adashe da wasu.
Tace jinin da aka mata karo 3 na baya duk suna barin mutum daya a cikin mu ya zauna kusa da ita har a gama, amma a wannan ranar ita wannan ma'aikaciyar jinyar ta hana kowa zama acikin mu, wanda da akwai wani kusa da ita, a lokacin da hakan bai faru ba😭 Bayan ta gama zancen adashen ta koma sai ta samu maman namu cikin wani irin yanayi, daga nan sai kuma ta rugo waje neman yayun namu mata, suna shiga sai s**a iske ta a cikin wannan yanayi ga jinin a malale a kasa ana ta kokarin gogewa.
Daga nan sai s**a gaggauta mayar da ita dakin da take kwana (ward) cikin sauri. Abin mamakin ya k**ata a yi tatar jinin na tsawon a kalla awa 4 ne a wannan ranar, amma ko awa biyu bai kai ba s**a mayar da ita don sun hararo abin da zai iya faruwa kuma ba su son ta rasu a warinsu. Sannan duk tace jinin da aka mata sau 3 a baya, idan an gama sai mun jira attendant na tsawon lokaci kafin a samu a mayar da ita, amma a wannan ranar ma'aikacin jinya (nurse) da kansa ya turata a wheel chair zuwa ward din da take kwance wanda kasa da awa 1 da mayar da ita ta rasu.
Wannan dalilin ya sanya ya zama dole mu nemi hakkin mu, a kuma ba mu amsoshin wasu tambayoyi da muka mika gaban hukumar wannan asibitin.
Akwai mutane da dama da ke haduwa da ire-iren wannan sakaci na ma'aikatan jinya wanda ke zama sanadin rasa rayukansu.
Hatta likitoti da s**a duba ta a wannan rana sun yi mamakin cewa ta rasu a wannan lokacin ganin yadda s**a same ta da kuma yadda s**a bar ta a wannan lokacin. wanda muka musu bayanin abin da ya faru, s**a ce da sun yi bayanin abin da ya faru da a lokacin an nemi jini da gaggawa, Allahu Akbar, kwanan dai ya kare, amma ta sanadin sakaci na wannan ma'aikaciyar jinya wanda ba za mu taba yafewa ba.
Wallahi tsawon zamanmu, babu likita daya da zan ce ga laifinsa, suna sauraro, kulawa, mutuntawa da daraja marasa lafiya da masu jinyar su, haka kuma akwai dimbin ma'aikatan jinya masu kirki da sanin ya k**ata, Allah Ta'ala ya saka musu da alkairi.
Alhamdulillah tuni mahukuntan ATBUTH sun fara daukar mataki kan wannan lamari, muna kuma cigaba da bibiyar dukkan matakan da su ke dauka.
Babban abin damuwar shine babu wanda ya san waye irin wannan sakacin zai shafa gobe.
A karshe kuma babu abin da ke mana dadi duk da yadda muka shiga dimuwa, firgici da damuwar wannan rashin sai abuwa k**ar haka;
1. Kalmar shahadar da ta zama kalmar karshe da ta furta, wanda ba wanda suke kusa da ita ba, har wanda suke da dan tazara da ita sun shaida hakan.
2. Shaidar halayeanta da duk wanda suke alaka da ita s**a mata.
3. Yadda hatta wanda iya zaman asibitin ne ya hada mu, amma suma s**a nuna damuwa da alhininsu saboda halinta da s**a fahimta a dan karamin zaman da Allah ya hada mu da su.
A karshe ina addu'ar Allah Ta'ala ya gafarta mata ya mata rahama, ya yafe mata dukkan kura-kurenta, ya albarkaci bayanta, ya ba mu ikon koyi da halayenta, amin.
Ibrahim Abubakar Katagum
12/5/2025