30/04/2026
🛑 DAN ALLAH 'YAN UWA MUSULMI, KU DAURE KU KOYA WA YARANKU HALAYE UKU:
1. Yawan gaishe da na gaba dasu.
2. Nutsuwa da barin wasa ahanya.
3. Futa cikin kyakykyawar shiga.
KU HANA YARANKU HALAYEN NAN:
1. Yawan yawace-yawace.
2. Yawan Abokai/ƙawaye barkatai.
3. Rashin kunya da faɗace-faɗace.
KU RIƘA GWABE BAKIN YARANKU:
1. Idan suna sa baki a maganar manya
2. Idan suna kawo tsegumi da gulma.
3. Idan suna zagi ko ƙaryata manya.
KUYI MUSU HORO ME TSANANI:
1. Idan suna wasa da Sallah.
2. Idan s**a fara kwaɗayi da roƙo
3. Idan s**a fara ƙarya da lalaci.
KU ƘARA JAWO YARANKU JIKI:
1. Idan s**a balaga.
2. Idan basu da lafiya.
3. Idan kuna gida a zaune.
KU KWAƊAITAR DA YARANKU:
1. Nacin karatu da rubutu.
2. Dagewa wajen cimma buri.
3. Lada da nasara in anbi hanyar Allah.
KU NUNAWA YARA MUHIMMANCIN:
1. Riƙo da Addinin musulunchi.
2. Zumunchi da ziyarar dangi.
3. Lafiya, Lokachi da kuruciya.
KU DAINA WAƊANNAN A GABANSU:
1. Bayyana tsiraici/mu'amalar aure
2. Wasan banza na ƙuruciya, kallo.
3. Bayyana rashin jituwa a tsakaninku.
KU YAWAITA A GABAN YARANKU:
1. Karatun Alqur'ani da salloli.
2. Aikata gaskiya da Ruƙon Amana.
3. Wadatar zuci da godiyar Allah.
SUKE JIN TSORON KU TA HANYAR:
1. Tsawatar musu in sunzo da wargi.
2. Rashin barinsu babu abinyi.
3. Taqaita nuna musu so ƙuru-ƙuru.
KU DAGE KU CIREWA YARANKU:
1. Tsoron mutuwa.
2. Tsoron talauchi.
3. Tsoron wanda baya tsoron Allah.
KU GOYI BAYAN YARANKU IN HAR:
1. sune ke da gaskiya.
2. Ba sa6o s**a aikata ba.
3. sunyi abu domin kare mutuncinku.
KUKE TSORATAR DA YARANKU:
1. Illar Haɗama.
2. Futinar rigima.
3. Haɗarin taqama da girman kai.
KU RIƘA SANARDA YARANKU:
1. Asali da Tarihi.
2. Mutuwa da kabari.
3. Daɗi da rashin sa.
KU BAWA YARANKU HORO NA:
1. Taqaita cin abinchi.
2. Ƙarancin Barchi da zaman hira.
3. Watsar da dogon buri da sharholiya.
Allah ya taimakemu, ya taimakemu wajen sauqe nauyi 'ya'yanmu day rataya Akan mu.