
21/09/2025
BI DA BI AKE BIN JAGORA BA'A WUCE SHI KUMA KAR YA MAKA NISA.
®Hameed Mirror
Watarana Imam Jawad (a.s) sun hadu da wani Dan Shi'ar su Mai Suna Ahmad Bin Zakariyya a Makka yayin Aikin Hajji, Sai mutumina yake cewa Imam "Ya Imam Gomnan mu masoyin ku ne, Yana tsananin muku biyayya, amma Imam Akwai harajin Gomnati a Kaina Mai nauyi" ya cigaba da cewa ya Imam da zaku temaka mana Koda da rubutun kune domin a saukaka min wannan harajin.
Sai Imam (a.s) yake cewa "Amma Ni Kuma ban sanshi ba" mutum yace "ya Imam Amma shi masoyin ku ne na hakika tabbas in kuka bashi sako zai aikata".
Sai Imam ya Rubuta Masa Takarfa k**ar haka "Assalamu alaika Ya Kai wannan Gomna tabbas Allah (T) ya daura maka hakkokin Al'umma a kanka, ka saukaka wa Al'ummar ka, ka musu rangome domin Allah zai tambaye ka daidai da Kwayar Hatsi da ya salwanta daga Baitil Mali. Wannan Mai sakon masoyin mu ne ka masa rangome daga harajin dake kanshi.
Bayan mutumin ya nufi komawa Garin su sai Labari ya riski sarki cewa ga chan wane ba tahowa da sako daga Imam Sadiq, a take Gomnan ya mike da kafa ya tunkaro fita daga gari domin ya Tarbi wannan Dan sakon, sai da yayi tafiya mai nisa sanan s**a hadu a hanya, Yana Isa ya rungume shi Yana Maraba dashi domin yau ga sako daga imamin Zamanin shi, kafin ya Bude takardan yace Masa, menene bukatar ka na biya maka yanzu, sai yace rangome nake nema daga Harajin da aka dauramin, take sarkin yace "Daga yanzu an cire maka Harajin, sannan za'a ware maka wani albarshi daga Baitil Mali daga yau".
Darasi.
Shi Imam Bai San wannan sarkin ba, Amma daga rubuta Letter shi domin biyayyar sa ga Imamin zamin sa baiga Sarautar dake kanshi ba ya tunkari barin gari domin ya Tarbi Mai wannan sakon, wannan fa rubutun takarda ne kawai, wani irin soyayya yakewa Imam da tinkafin ya Bude takardan ya biyawa Dan sako bukatarshi?, Tom irin wannan sallamawar da Mika wuya da Muwaddah akayiwa Jagora dake shiryar da ku zuwa ga Allah, shin mun Shirya irin wannan sallamawar ga wakilin Imam Mahdi Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) to irin wadannan sune Ashab na A'imma, wadanda ba damuwar su shine dole sai Imam ya San dasu ba aa me zasuyi domin su cikawa Imam burin shi, Mai zasuyi su faranta ran Imam. Amma sai kaga Jagora yayi jawabi wai mutum na Ikrarin Shi mabiyi ne Amma ko a jikinshi b***e ya bibiya, alhalin Jin sakonnin Jagora shine hanya na shirya shine hanyar sanin ina aka dosa Kuma ana inane, Muminai a gyara ana bin Jagora sau da kafa kar a bari Jagora yayi jawabi mutum hai saurara ba.
Ina Kara jaddada bai'ar Mutuwa ga Baban Hameed Sayyid Zakzaky, Allah ka tabbatar da duga-dugan mu akan Addinin ka.
Madogara Littafin As'habul A'imma.