
27/04/2024
YANZU-YANZU: Yadda Jama'ar Garin Rigasa S**a Hana A Binne Gawa Biyu.....
Wani Mummunan Al'amari Ya faru A Garin Kaduna! Wasu Mutane Da Ba'a san Ko Su waye Ba Sun Shiga Maƙabartar Layin Bola Dake Unguwar Rigasa Da Wata Motar Asibiti (Ambulance Car), Inda S**a yi Yunƙurin Birne Wasu Gawarwaki Guda Biyu Ba tare Da Sanin Hukumar Maƙabartar Ba😥.
Bayan Jama'ar Gari Sun Sami Labari Shi ne S**a je S**a yo Waje Da Gawarwakin Da Ba'a san Ko na Su Waye ba, Da kuma Dalilin Da yasa Aka Kashesu Ba, Sannan S**a Cinnawa Motar Asibitin Wuta Kamar Dai Yanda Kuke Gani a Hotunan dake Kasa.
Zuwa Yanzu Dai Ba'a san Dalilin Da yasa Aka yi Yunƙurin Birne Gawarwakin a Sirrance ba, kuma ba a san ko Gawarwakin Waye Ba, A Taƙaice Dai Jama'ar Gari Sun Ɗauki Doka A Hanunsu,Wanda Wannan Yunƙurin Ɗaukar Dokar Ne Yasa Aka Rasa Wadanda S**a zo Da Gawar, Domin sun bi ta cikin Hayaniya Sun Sulale sun gudu.
Allah ya kyauta.