14/09/2025
Menene Neuralink?
Neuralink wani kamfani ne da Elon Musk ya kafa a shekarar 2016, Babban burin kamfanin shine a haɗa kwakwalwar ɗan Adam kai tsaye da na’urorin computer ta hanyar wani ƙaramin chip da ake dasawa a cikin kwakwalwa.
Wannan chip ɗin da ake dasawa a kwakwalwa zai iya karanta tunanin da kwakwalwar ke yi tare da karɓar umarni daga gare ta, sannan ya aika waɗannan umarni zuwa na’ura.
Ga yadda abun yake a aikace, da farko, za a dasa chip ɗin a kwakwalwa, likitoci ne ke yin wannan aiki ta amfani da wata na’ura mai suna robot-surgeon, Chip ɗin ƙarami ne ƙwarai (kusan girman kwayar shinkafa).
Chip ɗin yana ɗauke da ƙananan wayoyi a cikinsa (electrodes) waɗanda suke karanta saƙonnin da kwakwalwa ke aikawa ta hanyar tunani. Misali, idan ka yi tunani a zuciyarka ka ce “Ina son na kalli film”, nan take kwakwalwa zata aika saƙo zuwa ga computer, sai computer ta kunna film ɗin kai tsaye, ba tare da kayi magana ko ka kunna da hannunka ba.
Kenan na’ura zata yi abin da kwakwalwar ta umurce ta, koda baka saka hannu kayi ba.
Mutumin da ya rasa kafafunsa saboda mummunan haɗari ko mai ciwon jijiya, zai iya sarrafa keken guragu na zamani ta hanyar tunani kawai, basai yayi amfani da hannayensa ba, saboda zai iya gajiya idan da hannaye zai tuka keken amma da tunani kawai keken zai dinga karbar umarni. Haka zalika mutumin da bai iya magana ba, kurma kenan shima zai iya rubuta sakonni a waya ta hanyar tunani kawai kuma ya ba wayar umarni ta aika sakon ta tunani kawai, haka kuma zai iya sarrafa kayayyaki a gida k**ar TV, AC, da sauransu da tunani kawai.
Masana sunyi hasashen cewa Neuralink na iya taimakawa wajen magance cututtukan kwakwalwa k**ar irin su cutar Alzheimer’s (cutar mantuwa), cutar Parkinson’s, da sauran cututtukan da ke hana kwakwalwa aiki yadda ya k**ata.
Nan gaba kuma idan fasahar ta cigaba da wanzuwa ana tunanin zai yiwu mutum ya iya sauke ilimi kai tsaye daga internet zuwa kwakwalwa, ko yin magana da wani ba tare da furta kalma ba, ta tunani kawai.
Haka zalika ana tunanin za'a kawo lokacin haɗa kwakwalwa da Artificial Intelligence (AI) don samun tunani mai ƙarfi fiye da na ɗan adam.
Mutum zai zama k**ar rabi mutum rabi robot Mutum-Robot, kenan..😀
A shekarar 2021, an nuna wasu birai da aka dasa musu chip suna iya kunna game a computer ta hanyar tunani kawai, haka a shekarar 2023, Elon Musk ya sanar da samun mutum na farko da aka dasa masa chip ɗin, kuma ya yi nasarar sarrafa mouse na computer da tunaninsa ba tare da amfani da hannunsa ba.
Amma fa akwai hadari gaskiya a wannan fasahar sosai, domin dasa chip a kwakwalwa ba abu ne mai sauƙi ba, akwai haɗarin samun rauni ko kamuwa da cuta, ko ma rasa rai gabadaya.
Babu tabbacin tsawon lokacin da chip zai iya aiki a jikin mutum, haka zalika Idan aka haɗa kwakwalwa da internet, akwai yiwuwar hacking wato wani na iya kutse ya sarrafa kwakwalwar mutum.
A takaice, Neuralink fasaha ce mai girma da zata iya canza rayuwar ɗan Adam gaba ɗaya. A halin yanzu tana matakin bincike, amma an riga an tabbatar tana aiki da gaske, Idan ta ci gaba da bunƙasa, zata iya sauƙaƙa rayuwa, magance cututtukan kwakwalwa, da baiwa mutum damar yin abubuwan da ba zai iya yi da kansa ba.
Amma fa, tana da haɗari sosai.
Allah ya sa mu dace.
Daga Abdurrazak Saheel