21/10/2025
"... ILIMI ANA YIN SA NE DON ALLAH:.."
___Daga Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
“To na kan ta yi ma ƴan'uwa magana; shi fa karatu za ka yi ne saboda Allah. ‘Iqraa Bismi Rabbika’ za ka yi, ‘Bismi Rabbikal Laziy Khalaq’ za ka yi karatun da sunan Allah.
“Rayuwa fa? Ana yin karatu a samu ‘Certificate’ a samu aiki mai albashi mai tsoka, a ci a sha, har a yi ‘retire’ shi kenan? Wasu haka s**a ɗauki ma'anar karatu ko? Har ya zama yanzu mun kawo marhalar da ba wannan. A da can sai a yi ta ce maka in ka sa ɗanka a makaranta, ka ga za ka huta, in ya yi makaranta, zai zo ya k**a aiki, zai samu albashi mai tsoka, ka ga za ka huta.
“Sai wasu suna sa yaransu a makaranta, su fara aiki, in me ka ke karantawa sai ka k**a aiki kaza kenan, yana ganawa abinda ya dame shi ya k**a aiki, ya k**a aiki tiryan-tiryan sai a ga matsayi ya cigaba, ya samu kaza har ya zuwa 'retire'.
“To shi kenan, shi kuma sai shima ya haifi da ya sa shi a makaranta shima ya yi karatu shima ya k**a aiki shima ya tsufa ya yi 'retire', haka nan shi kenan, ka ga rayuwa kenan — haka waɗansu s**a ɗauki rayuwa, k**ar bata da 'purpose' meye makasuɗin yinta? Ya k**ata a ce ana yi don wata manufa ne.
“To mu karatun addini ya wuce wannan, ba mu ce ba za ka rayu ba, ba mu ce ba za ka iya karanta wani fanni wanda akan yi amfani da shi har a samu albashi ba, alal misali 'Medicine' ko 'Engineering' ba mu ce kada ka yi ba, an fahimta ai. Amma ka yi 'Bismi Rabbikal Laziy Khalaq' ka yi da sunan Allah, ka yi da unwanin addini.
“Na san ina magana da wasu ba'aɗin yan'uwa a Tehran, na ce musu kun ga yanzu lokacin da waɗannan da s**a tsokani Jamhuriya (Iran) ai sun ji ba daɗi ko? Kun ga kuma sak**akon ilimi ne, to amma tambaya; ilimin nan na Hauza ne? Sai s**a ce a'a, na ce amma kar ku ce na soki na Hauza — na Hauzar ne sanadi, shi ya yi Jagoranci.
“Don shi Imam (Khumaini) yana da fahimtar duniyarsa sosai. Akwai lokacin da ana samun raini tsakanin Malaman Hauza da Malaman Jami'a, sai shi ya ce a'a, kowanne ya yi aikin da yake yi wajibi ne, kuma aka bukatar kowanne, duk ilimi ne kuma ana bukatar kowanne, kada wani ya raina wani, an fahimta ai.
“Na ce to, ba mu ce maka ba a ilimi a samu wani abu ba, amma ba ana yi domin a samu wani abin duniya bane, abin duniya yana binka ne, kai dai ka yi ilimin kawai, ka yi shi kawai; musamman ku da ku ke na Hauzozin nan, a yi karatun kawai.
“To (Ga masu cewa) in na gama ina zan samu aiki? Me zan ci? Manta da wannan, ‘Arrizƙu Rizƙaani; Rizƙun Tadribuhu wa Rizƙun Yadribuk’ in ka yi ilimi Fisabilillahi arziki zai biyo ka ne, biyo ka zai yi...!
“Saboda haka idan kai kuwa rayuwa ta dame ka, tunaninka idan ka gama me za ka ci? To shi kenan, sai ka dawo ka yi ta dambe da bidar abinci kuma, yanzu kai me jihadin neman na tuwo ne, a haka kuwa za ka ƙarata. Allah Ya sauwake”.
Ɓangaren jawabin Jagora Shaekh Ibraheem Zakzaky (H) ga daliban Hauzozin Ilmi daga ƙasashe daban-daban a gidansa da ke Abuja, ranar Talata 20 ga Jimadal Thani 1447 (14/10/2025).
©️ Tafsir Da Jawaban Jagora
—21/10 October/2025.