15/10/2025
Daga shafin; Barista Audu Bulama
Tabbas mutumin da ya fito jiya ya ce ya yafe wa Maryam Sanda shi ne baban Bilyaminu. Amma na tattauna da dangin mahaifiyar Bilyaminu, waɗanda Bilyaminu ya girma a hannunsu tun daga ranar da mahaifiyarsa ta dawo gida wankansa. Ga abinda su ka ce:
1. Sun ce baban Bilyaminu bai sake zuwa ya duba ɗansa ba tun daga ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar Bilyaminu a gidan iyayenta da ya je bayan ta gama wakan Bilyaminu a 1981.
2. Sun ce bai taɓa sanin ci, ko sha, ko sutura, ko jinya, ko karatun Bilyaminu ba.
3. Sun ce akwai lokacin da kakar Bilyaminu ta tura shi hutu gurin baban lokacin yana firamare domin su san juna, a kuma kai shi wurin kakanninsa na gefen uba a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sokoto, amma uban ya sa shi a mota dawo da shi Birnin Kebbi gurin iyayen kakar tasa a ranar da ya je gurinsa.
4. Sun ce baban Bilyaminu ya yi aiki na misalin tsawon shekara biyu a garin Birnin Kebbi, inda Bilyaminu ya girma, amma bai taɓa leƙa gidan kakar Bilyaminu idan ya girma ba, ya duba yaron ba. Hasali ma, ɓuya ya ke yi domin ba ya so a san cewa ya na garin.
5. Sun ce bai halarci ɗaurin auren Bilyaminu na farko ko na biyun da a ka yi da Maryam Sanda ba. Ko tambayar auren bai je ba.
6. Sun ce baban bai je ko jana'izar ko ta'aziyyar Bilyaminu ba.
7. Sun ce bai taɓa halartar Kotu domin bibiyar Shari'ar kisan Bilyaminu ba.
8. Sun ce sam bai tuntuɓe su ba kafin ya fito ya yi wannan maganar kuma ba wanda ya tuntuɓe su game da yafe wa Maryam Sanda, kuma su ba su yafe ba.
9. Su na zargin cewa miliyan goma uwar Maryam Sanda ta ba wa uban domin ya saryantar da jinin Bilyaminu.
Don uba dai mutumin nan shi ne uban Bilyaminu tun da haka Shari'ah ta ce. Amma abin mamaki ne don mutumin da bai san ciwonka ko kaɗan ba ya ce ya yafe jininka? Ai ko a kwalarsa. Shin uba shi kaɗai zai iya yafe jinin ɗa a Shari'ar musulunci ko kuwa sai dukkanin awliyāʾ al-dam (wakilan jini) sun amince?
Wata shari'ar sai a lahira.