16/01/2026
Fitaccen Malami Kuma Limamin da Ya Ceto Kiristoci 300 a Jihar Filato Ya Rasu
Fitaccen limamin Musulunci, Malam Abdullahi Abubakar, wanda ya shahara sanadiyyar ceto Kiristoci sama da 300 a yayin rikicin jihar Filato a shekarar 2018, ya rasu yana da shekaru 92. Marigayi Abdullahi Abubakar shi ne babban limamin garin Nghar da ke karamar hukumar Barikin Ladi, inda ya shafe shekaru yana hidimtawa al’umma da kuma karantar da zaman lafiya da hadin kai.
Limamin ya yi fice ne lokacin da rikici ya barke a wasu sassan Jihar Filato, inda wasu ‘yan bindiga s**a kai hare-hare. A lokacin tashin hankalin, ya bude kofar masallacinsa da gidansa, ya ba da mafaka ga daruruwan Kiristoci da ke guduwa domin tsira da rayukansu, ba tare da la’akari da bambancin addini ba.
Jarumtaka da tausayi irin na Malam Abdullahi Abubakar sun jawo masa yabo daga cikin gida da wajen Najeriya, inda aka rika daukarsa a matsayin abin koyi na zaman lafiya tsakanin addinai. Bayan rasuwarsa, jama’a da dama sun bayyana bakin cikinsu, tareda ambata shi a matsayin gwarzon bil’adama da ya fifita kare rayukan mutane fiye da komai.