22/10/2025
Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutane 35 sak**akon mummunar gobarar da ta tashi daga tankar mai da ta yi hatsari a kan hanyar Bida zuwa Lafai, bayan an wuce Badegi, a ranar Talata.
Rahotanni sun nuna cewa waɗanda abin ya rutsa da su sun kone kurmus har lahira, yayin da suke ƙoƙarin kwasar mai daga tankar da ta yi hatsari.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a yammacin Talata, FRSC ta bayyana damuwa kan wannan masifa wacce ta faru sak**akon rashin bin ƙa’idoji, son kai, da watsi da gargadin kiyaye lafiya.
Hukumar ta ce tawagar agajin gaggawa ta isa wurin da lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12:15 na rana, lokacin da tankar mai ɗauke da fetur ta subuce saboda munin hanya, ta kuma hantsila.
Jim kaɗan bayan hatsarin, mazauna yankin s**a taru suna ƙoƙarin kwasar mai daga cikin tankar da ta fadi, sai dai nan take ta k**a da wuta wacce ta hallaka mutane 35 tare da jikkata wasu 46.