14/06/2022
A shekarar da ta gabata, 'yan kasuwa da dama sun soma kara farashi kan kayayyakinsu irin wanda aka dade ba a gani ba. Daya daga cikin manyan kasashen da wannan lamari ya fi muni ita ce Amurka.
Farashin kayayyaki ya tashi da kashi 4.7 a bara - fiye da kowace kasa a cikin kasashe na kungiyar G7 da s**a fi karfin tattalin arziki a duniya, a cewar kungiyar kasashe masu hada kai wajen ci gaban tattalin arziki, wadda a turance ake kira Organisation for Economic Cooperation and Development (OECD). Alal misali, a Birtaniya farashi ya hauhawa ne kawai da kashi 2.5.
A watan jiya, farashi hauhawa da kashi 8.6 a Amurka, daya daga cikin mafiya muni a duniya.
Ba Amurka ce kadai kasar da ta yi fama da abubuwan da s**a haddasa hauhawar farashi a shekarar da ta gabata ba - wadanda s**a hada da karancin samar da kayayyaki sak**akon cutar korona da kuma hauhawar farashin abinci sak**akon aukuwar mahaukaciyar guguwa da fari wadanda s**a sa kaka ba ta yi kyau ba.
Me ya sa aka samu munanar hauhawar farashi a Amurka? A cikin kalma biyu, dalilin shi ne - matukar bukata.
Hakan ya faru ne sak**akon amincewar da gwamnatin Amurka ta yi a kashe makudan kudaden da s**a kai $5tn (£4.1tn) domin kare magidanta da masu kasuwanci daga radadin matsin tattalin arziki saboda cutar korona.
Kudaden da gwamnati take kashewa
Matakin rage radadin matsin tattalin arziki da aka yi wa magidanta - wanda ya hada da ba su chaki na kudi - ya taimaka musu ci gaba da sayen kayayyaki.
Magidanta sun rika amfani da kudaden domin sayen kayan daki, da motoci da kayan lataroni sosai.
Kuma wannan matukar bukata ta kayayyaki ta zo daidai da karancin samar da kayayyaki sak**akon annobar korona, lamarin da ya sa 'yan kasuwa s**a kara farashin kayayyaki.
Wani bincike da Baitulmalun San Francisco ya gudanar ya nuna cewa bai wa mutane kudaden tallafin korona ya ta'azzara hauhawar farashin kayayyaki da kimanin kashi uku zuwa karshen 2021 - lamarin da ya sa hauhawar farashi a Amurka ta ninninka ta sauran kasashe.
Oscar Jorda, wani