05/08/2025
CREATIVE ECONOMY DEVELOPMENT FUND...
Wannan tsarin da ma'aikatar Art And Culture suke jagoranta wajen bayar da bashi ga mutane masu harkokin kasuwanci irinsu Content creation, dinki, Games har da Films da sauran sana'oi masu yawa, na hango cewa sun kammala kashi na farko sannan sun fara kashi na biyu a jiya 4 ga watan August...
Na kawo labarin ne saboda nasan akwai matasa anan Arewa da suke ayyukan sanar da al'umma irin wannan damarmakin...
Su bincika suyiwa mutane bayani hanyoyin da ake bi wajen samun wannan bashi da zai iya kaiwa har Dollars dubu goma zuwa dari ya danganta da yawan da aka nema...
Labarin na gani sai na bibiyi website dinsu na tabbatar da cewa gaske ne ana bayarwa don haka na kawo shi nan, bani da kowacce irin alaka da ma'aikatar Art And Culture, sannan ba sune s**a sanyani wannan rubutun ba...
https://cedf.gov.ng/