19/12/2025
Matasa Daga Arewacin Najeriya Sun Bukaci Tinubu Ya Sallami Ministan Tsaro Bello Matawalle
Ƙungiyar Northern Christian Youth Coalition (NCYC) ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sallami Ministan Ƙasa na Tsaro, Dr. Bello Muhammed Matawalle, sakamakon zarge-zargen da suke nuna cewa yana da alaƙa da ta'addanci wanda tsohon hadiminsa Musa Kamarawa yayi ikirari.
A cikin wata sanarwa da Babban Kwamishinan ƙungiyar, Jeremaid Hudso Bako, ya fitar, ƙungiyar ta ce kira da take yi na nufin ƙarfafa gaskiya, riƙon amana, da dawo da amincewar jama’a ga gwamnati, musamman a bangaren tsaro.
Ƙungiyar ta yaba wa Shugaba Tinubu kan tsige tsohon Shugaban Hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed, tana mai cewa hakan alama ce ta ƙoƙarin gwamnati wajen yaƙi da cin hanci da rashawa. Sai dai ta ce ya dace a yi adalci iri ɗaya ga kowa, ciki har da Matawalle.
NCYC ta jaddada cewa zarge-zargen da ake yi wa Matawalle suna da nauyi sosai, musamman ganin cewa suna da alaƙa da tsaron ƙasa da rayukan al’umma, don haka bai dace a yi shiru a kansu ba.
Ƙungiyar ta ce idan har gwamnatin Tinubu na son a san ta da gaskiya, adalci da shugabanci nagari, to ya zama dole ta ɗauki mataki cikin gaggawa kan duk wani jami’i da ake zargi da aikata abubuwan da za su iya lalata amincin ƙasa tare da sauke ƙaramin ministan da kuma gudanar da binciken gaggawa a kansa.