15/09/2025
Tallafin taki: Sanata Barau ya raba fiye da buhuna 4,600 ga malamai a Kano ta Arewa
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya raba buhunan taki 4,691 ga malaman makarantun firamare, sakandare da kuma makarantun allo (Tsangaya) a shiyyar Kano ta Arewa.
An gudanar da rabon a yankin masana’antu na Sharada da ke Kano, a wani bangare na kokarinsa na tallafa wa shirin gwamnatin tarayya wajen tabbatar da isasshen abinci a kasa.
Da yake jawabi ta bakin Shugaban Ma’aikatan ofishinsa, Farfesa Muhammad Ibn Abdallah, Sanata Barau ya ce wannan shirin an yi shi ne domin karfafawa malaman makarantu da malaman allo, kasancewar su ginshikin ci gaban al’umma.
Ya ce: “A baya mun raba buhunan taki sama da 40,000 ga manoma a fadin jihar Kano. Yau kuma mun mayar da hankali ga malamai, malaman Tsangaya, shugabannin makarantu da malamai na firamare da sakandare, domin su ma su ci gajiyar wannan shiri.”
Sanatan ya kara da cewa an bayar da takin kyauta, tare da kira ga masu karɓa da su yi amfani da shi yadda ya dace domin cimma burin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da wadataccen abinci a kasa.
A cikin rabon, malaman Tsangaya za su samu buhuna 661, malaman sakandare na matakin karamar sakandire za su samu buhu 221, na matakin babbar sakandire za su samu buhu 392, yayin da malaman firamare za su samu buhu 227, sauran kuma za a rarraba su ga wasu rukuni daban-daban.
Shugaban kungiyar Shugabannin Makarantun Firamare na yankin, Musa Auwalu Gwarzo, ya gode wa Sanata Barau bisa wannan taimako, inda ya bayyana shi a matsayin “shugaba na kowa da kowa.”