04/04/2024
Taimakon Raunana:
To kuma, mu a wurinmu, lallai addini ne, don a sani, lallai addini ne. Amirulmuminin (AS) yana cewa “Kunu lil mazlumina aunan, wa liz zalimina kasma.” “Kunu kasman liz zalimina, wa lil mazlumina auna.” Ma’ana, ku kasance masu fada da azzalumi, masu taimakon wanda ake zalunta. Wajibi ne cikin wajibobin addini. Manzon Allah (S) yana cewa “Man lam yahtamma bi amril Muslimina falaisa minhum.” “Man ashaba walam yahtamma bi amril Muslimina falaisa bi Muslimin.” Wato, wanda ya wayi gari bai damu da abin da ya shafi Musulmi ba, bashi a cikinsu.
Kuma Manzon Allah (S) ya kamanta al’ummar Musulmi da tamkar jiki daya, wanda in wani bangare aka taba shi sauran jiki na amsawa da rashin lafiya. Ba yadda za a yi idan ido ke ciwo yatsa yace ba ruwansa, ko in yatsa ke ciwo na ciwo ido yace ba ruwanshi. In yatsa ke ciwo ido ya shiga yin ruwa kenan, ba zai kuma yi bacci ba, saboda duk inda ka taba a jikin mutum, duk sauran jikin zai amsa. To haka ya kamanta al’ummar Musulmi. Saboda haka in aka taba wani bangare na al’ummar Musulmi ka ji kai baka ji ba, to baka a jikin, ko kuma ka mace. Don idan wani bangare a jikin mutum ya mace, ko an soka allura ba zai ji ba, in bai ji shigan allura ba, yana nufin wannan bangaren ya mace, ya tashi a jikinsa, ya zama wani abu daban.
To, wanda duk yake ganin abin da ke faruwa yanzu a Falastinu, ya zama shi abin bai dame shi ba, alal akalla ko da ace masallatai, wanda ban san yanzu ko sun kai masallaci nawa ba? Akwai lokacin da aka ce, sun rusa masallaci manya-manya wanda ake sallar Juma’a guda 58, kuma wani lokaci suna rusa masallatan nan akan masallata ne. To ko da wannan ne, kana Musulmi, bai kamata ya dame ka ba?
To ballantana ma mu duk inda ake zaluntar wanda ake zalunta, ko meye addininsa, mu dole mu damu. Domin dole ne mu zama masu taimakon wanda ake zalunta, mu yi fada da wanda ke zalunci. Ko ma meye addininsu, ko da addininsu wani irin addini ne ba irin namu ba, ma’ana ko da su ba Musulmi ba ne.
-Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a cikin bayaninsa na nuna goyon baya ga Al'ummar Falastinu na bana 2024.
25/Ramadan/1445
04/04/2024