23/08/2026
Sojoji Sun Kuɓutar da Mutane 6 da Aka Sace, Sun Kwato Naira 800,000 a Katsina
Sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun kuɓutar da mutane shida da ’yan ta’adda s**a yi garkuwa da su a hanyar Dandume zuwa Sheme, tare da kwato N800,000 da aka karɓe daga hannunsu.
Rundunar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 22 ga Agusta 2026, bayan sojoji sun kai ɗaukin gaggawa tare da fafatawa da ’yan ta’addan, lamarin da ya tilasta musu tserewa cikin daji.
A wani samamen daban da aka gudanar a ranar 21 ga Agusta a yankin Maraban Kankara, sojoji sun fatattaki ’yan ta’adda tare da kwato babur guda.
Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kai hare-hare da sintiri domin hana ’yan ta’adda samun damar gudanar da ayyukansu da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.