Katsina.ng News

Katsina.ng News Jaridar Online ce da aka bude domin wallafa labarai daban-daban da ke faɗin duniya.

Gwamnan jihar Katsina, Dr Dikko Radda ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi a yau Lahad...
07/12/2025

Gwamnan jihar Katsina, Dr Dikko Radda ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi a yau Lahadi.

Ɗan Asalin jihar Katsina, daga ƙaramar hukumar Jibia Air Commodore Garba Ibrahim Jibia, ya sami Babban ƙarin girma a run...
29/11/2025

Ɗan Asalin jihar Katsina, daga ƙaramar hukumar Jibia Air Commodore Garba Ibrahim Jibia, ya sami Babban ƙarin girma a rundunar Sojin sama, zuwa Matsayin Air Vice Marshall, wanda yake daidai da Manjo Janar.

Ƴar Gidan Fitaccen Attajirin Ɗan Kasuwa A Afrika, Kuma Shugaban Kamfanin Sufirin Jiragen Sama Na Max-Air Alhaji Ɗahiru M...
28/11/2025

Ƴar Gidan Fitaccen Attajirin Ɗan Kasuwa A Afrika, Kuma Shugaban Kamfanin Sufirin Jiragen Sama Na Max-Air Alhaji Ɗahiru Mangal Ta Kammala Karatun Digirinta Na Biyu.

📸 -Arewa Beauty

Allah ya yiwa Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa. Ya rasu yana da shekaru 98 a duniya.
27/11/2025

Allah ya yiwa Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa. Ya rasu yana da shekaru 98 a duniya.

Gwamnan Jihar Katsina Dr Dikko Radda Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kasafin Kuɗin Shekarar 2026, Kimanin Naira Biliyan Dari Ta...
26/11/2025

Gwamnan Jihar Katsina Dr Dikko Radda Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kasafin Kuɗin Shekarar 2026, Kimanin Naira Biliyan Dari Takwas Da Casa'in Da Bakwai Da Ɗigo Takwas (897.8bn).

Gwamnatin Katsina ta bada umarnin ɗaliban Makarantun jeka-ka-dawo su ci gaba da zuwa MakarantaGwamnatin jihar Katsina ta...
24/11/2025

Gwamnatin Katsina ta bada umarnin ɗaliban Makarantun jeka-ka-dawo su ci gaba da zuwa Makaranta

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da cewa dokar kulle makarantu bata shafi makarantun jeka-ka-dawo ba. Domin haka Makarantun Firamare da Sakandare na jeka-ka-dawo za su ci gaba da zuwa makaranta kamar yadda s**a saba.

Yadda Gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umaru Radda ya dawo gida Nijeriya bayan kammala ziyarar aiki a ƙasashen Belarus, F...
23/11/2025

Yadda Gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umaru Radda ya dawo gida Nijeriya bayan kammala ziyarar aiki a ƙasashen Belarus, France da kuma South Africa.

Gwamnatin Katsina ta bada umarnin a rufe dukkan Makarantun jihar, saboda matsalolin tsaro.Gwamnatin Jihar Katsina ta bay...
21/11/2025

Gwamnatin Katsina ta bada umarnin a rufe dukkan Makarantun jihar, saboda matsalolin tsaro.

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun gwamnati da ke fadin jihar, bayan karin tashin hankali da rahotannin tsaro da aka samu a wasu yankuna na jihar. Wannan mataki ya biyo bayan taron gaggawa da gwamnatin ta gudanar domin kare rayukan ɗalibai da malamai.

A cikin sanarwar, gwamnatin ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin bunkasa matakan kariyar tsaro, tare da bai wa hukumomin tsaro damar aiwatar da sabon tsari na tabbatar da zaman lafiya a kusa da makarantu. Gwamnati ta ce rufe makarantun zai kasance na ɗan lokaci ne har sai an kammala sake duba tsaron muhimman wurare.

Wannan Mataki da gwamnatin jihar ta dauka, ya biyo bayan garkuwa da ɗaliban makarantun sakandire a jihohin Kebbi da Neja cikin kwanaki kalilan da s**a gabata, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin hukumomi da iyaye a fadin Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Yadda Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kammala wata muhimmiyar ziyarar aiki ta kwana huɗu a birnin Min...
19/11/2025

Yadda Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kammala wata muhimmiyar ziyarar aiki ta kwana huɗu a birnin Minsk na ƙasar Belarus, inda ya cimma manyan yarjejeniyoyi na habaka fasahar zamani, inganta tsaro da aikin noma a jihar.

A lokacin ziyarar, Gwamnan ya sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama a fannonin ilimi, tsaro, noma, da fasahar zamani. Ya ziyarci Hi-Tech Park da kamfanin Beltech Export, wasu cibiyoyin fasaha mafi tasiri a nahiyar Turai, inda ya tattauna batutuwa kan musayar fasaha, tsaro da dabarun kirkire-kirkire a Katsina.

Gwamnatin Katsina za ta shirya muƙabala tsakanin Malam Yahaya Masuss**a da ke Da'awar Al-ƙur'ani Zallah da kuma sauran M...
18/11/2025

Gwamnatin Katsina za ta shirya muƙabala tsakanin Malam Yahaya Masuss**a da ke Da'awar Al-ƙur'ani Zallah da kuma sauran Malamai da ke ƙalubalantarsa a jihar.

Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Dr. Dikko Umaru Radda za ta shirya muƙabala tsakanin Malam Yahaya Masuss**a mai da'awar Al-kur'ani zalla da wasu malamai masu ƙalubalantarsa a jihar

A cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari, Esq ya sanya wa hannu, Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya umarci Malam Yahaya da ya shirya don kare kansa kan zarge-zargen da ake masa, a gaban Kwamitin Malamai.

Hakazalika Majiyar Jaridar Arewa ta jiyo cewa za a fitar da ƙa’idoji da tsare-tsare, kuma duk wanda ya saba wa waɗannan ƙa’idoji, Gwamnati za ta ɗauki mataki mai tsauri a kansa. Mene ne ra'ayoyin ku?

Tsohon Gwamnan jihar Katsina Barr. Ibrahim Shema, ya isa London domin taya Umar Ibrahim Lange, murnar kammala karatun Di...
15/11/2025

Tsohon Gwamnan jihar Katsina Barr. Ibrahim Shema, ya isa London domin taya Umar Ibrahim Lange, murnar kammala karatun Digirinsa a Jami'ar “Westminster da ke birnin London.

Ɗalibin Umar Ibrahim Lange, jika ne ga Tsohon shugaban kasa Marigayi Ummaru Musa Yar'adua.

Yadda aka gudanar da zaman Sasanci tsakaninsu ‘yan bindiga da al'ummar ƙaramar hukumar Kankiya jihar Katsina.
15/11/2025

Yadda aka gudanar da zaman Sasanci tsakaninsu ‘yan bindiga da al'ummar ƙaramar hukumar Kankiya jihar Katsina.

Address

Abuja

Telephone

08124664435

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katsina.ng News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share