18/10/2025
TARON HADIN KAI DA KARFAFA GINSHIKIN JAM’IYYAR PDP A JAMA’ARE
A yau Asabar, 18 ga Oktoba, 2025, an gudanar da muhimmin taron masu ruwa da tsaki (Stakeholders Meeting) na jam’iyyar PDP a karamar hukumar Jama’are, domin tattauna hanyoyin da za su ƙarfafa jam’iyyar a matakan gida da waje.
Taron ya kasance daya daga cikin mafi muhimmanci a wannan lokaci, kasancewar ya zo ne a daidai lokacin da ake buƙatar haɗin kai, fahimtar juna, da sake gina martabar jam’iyya bisa gaskiya da adalci.
A cikin jawaban da aka gabatar, an jaddada cewa jam’iyyar PDP ta tsaya ne kan ginshiƙan dimokuraɗiyya, adalci da ci gaban al’umma, tare da jan hankali ga muhimmancin aiki tare domin tabbatar da nasara a matakai daban-daban.
Masu ruwa da tsaki sun yi kira da a sake buɗe sabbin hanyoyin haɗin kai da sulhu a tsakanin ’ya’yan jam’iyya, tare da ƙarfafa tushe a mazabu, farfaɗo da ɓangarorin matasa da mata, da kuma inganta hanyoyin sadarwa tsakanin shugabanni da mambobi.
Wani daga cikin jagororin taron ya jaddada cewa:
> “Ba jam’iyya ce kaɗai ke kawo nasara ba idan babu haɗin kai da aiki tare. Lokaci ya yi mu dawo mu ɗora kan tafarkin gaskiya, mutunta juna, da kishin jam’iyya. PDP ba ta rushe ba — tana nan daram, tana ƙara ƙarfafawa.”
Haka kuma, mahalarta taron sun yaba wa shugabannin jam’iyyar a matakan jiha da ƙasa bisa jajircewarsu wajen jagorantar jam’iyya cikin natsuwa da hangen nesa, tare da kira da a ci gaba da mara musu baya domin tabbatar da nasarar siyasa a gaba.
🔵 Jam’iyyar PDP a Jama’are na tabbatar da cewa tare da haɗin kai, mutunta juna, da jajircewa, za ta ci gaba da zama ginshiƙi mai ƙarfafa dimokuraɗiyya da kare muradun al’umma.
Usman Adamu Dawu
Classic TV Albarka Radio Jamaare Gida Jibwis Jama'are