03/01/2025
Wata Gaskiya Mai Dachi
Daya daga chikin manyan dalilan da suke daqile mutane zuwa ga nasara aduk abinda s**a saka a gaba shine rashin mayarda hankali (focus) akan abinda suke burin chimma nasara akansa. Wannan matsalar ta rashin focus ta bawa mutane da yawa matsala a harkokinsu da s**a saka a gaba. Misali, A shekarar data gabata ta 2024, miliyoyin mutane sun shigo harkar mining bayan samun labarin fashewar Notcoin, suna shigowa sai s**achi karo da TapSwap da sauran minings na lokachin, kuma kasancewar sunji labarin cewa du-du-du wata uku kawai akayi ana mining na Notcoin sai s**ayi tunanin TapSwap da sauransu suma wata ukun za'ayi. Bayan sun gaji da jiran gawon shanun TapSwap, sannan sauran da sukeyi kamarsu Avacoin basu samu kudi kamar yanda s**aga Notcoin ya bayar ba. Then this ๐
๐ Minings wahalace, dan baiwa tsaya da kafarka, dan baiwa kawai ya koyi trading!
๐ Dan baiwa ya fara koyar trading. Daga baya yace CEX trading wahalace, kuma asara yakeyi.
๐ Dan baiwa yace Dex trading zai koma. Itama yace ya daina asara yakeyi.
๐ Dan baiwa yaji labarin Facebook suna biya, saiya fara follow for follow. Let's go ๐ถโโ๏ธ ๐ช ๐
๐ Follow to follow din dan baiwa bai tsaya iya Facebook ba, abin saida yayi naso zuwa Phantom ๐
๐ Dan baiwa ya fara sabuwar shekarar 2025 da Crypto Jobs ๐
Haka dai dan baiwa zaita chanjawa daga wannan zuwa wancan, daga wancan zuwa wannan. Idan baiyi a hankali ba, haka shekarar zata kare yana bilayi, a karshe kuma ya kare da zagin influencers, yana kiransu yan son zuchiya da sauransu.
Duk wanda kukaga ya chimma nasara a harkar da yakeyi, tsayawa akanta ya koyeta. Yasha wahala sosai, yayi asara, amma hakan bai karya masa gwiwa ba, haka yachi gaba da dagewa har Allah yasa ya fahimchi harkar sosa. Mafi yawan wayanda kuke gani suna cewa sun shiga trade sun fito da riba saida s**ayi asara sosai kafin su fara samun riba. Haka duk wayanda kukaga suna samun kudi a Facebook saida s**ayi aiki tukuru yau-da gabe sannan Facebook s**a fara biyansu. Hakc