26/08/2025
Yadda Hausawa S**a Bazu a Duniya
Hausawa sun fi yawa a Nijeriya da Nijar, amma daga nan s**a bazu zuwa sauran sassan duniya ta hanyoyi uku:
1. Hanyar Kasuwanci
Hausawa sun shahara da kasuwanci tun da dadewa (ƙasa da ƙasa kafin zuwan Turawa).
Suna yin fatauci da gishiri, auduga, kayan ado, da dabbobi.
Wannan fatauci ne ya kai su har zuwa:
Sudan
Chadi
Mali
Libya
Maroko
A waɗannan wurare, suna kafa unguwanni na Hausa inda suke zama tare da iyalansu.
2. Hanyar Addini (Musulunci da Hajji)
Hausawa sun karɓi Musulunci tun ƙarni na 14.
Yawan tafiya Aikin Hajji a Makkah yasa da yawa daga cikinsu s**a tsaya a Sudan, Saudiya, har ma Yemen.
A Makkah da Madina, har yanzu akwai unguwannin da ake kira Unguwar Hausa saboda tarin Hausawa da s**a zauna a can.
3. Hanyar Hijira (Zaman Takewa da Aiki)
A zamanin turawa da bayan mulkin mallaka, Hausawa suna yin hijira domin neman aiki a: Kasashe inda suke zuwa a'matsayin ma'aikata gwamnati kasuwanci da kuma noma.
Bayan haka kuma, a zamanin yau, yaran Hausa suna zuwa: Yankin Turai wato ( Amurka Birtaniya, Jamus, Faransa) A yankin, Asiya kuma suna zuwa kasashen ( Gulf: Saudiyya, UAE, Qatar)
4. Bazuwar yaran hausa a wannan zamanin.
A yau, Hausawa sun baje kolin su a duniya ta:
Kasuwanci (Import/Export).
Addini (malamai da makarantu na Musulunci).
Sana’o’i (saka, dinki, da fannin kiɗa).
A cikin Nijeriya da Nijar, Hausawa sun zama mafi girma a yawan jama’a. Amma a wajen ƙasashen nan, suna rayuwa a cikin unguwanni masu suna “Unguwar Hausa” ko “Sabon Gari”.
Jadawalin Bazuwar Hausawa.
Ƙarni na 13 zuwa 15 Kasuwanci yakai hausawa kasashen Sudan, Mali, Chadi.
Ƙarni na 14-16 Addini Musulunci da kuma. Hajji yakai hausawa, kasar Makkah, Madina, Yemen
Ƙarni na 18 zuwa 19 Hijira da kasuwanci yakai hausawa kasar Ghana, Kameru, Libya.
Ƙarni na 20 zuwa 21 Aiki da Karatu nakai hausawa yankin, Turai, (Gulf countries)
👉🏽 A takaice: Hausawa sun bazu a duniya ne ta kasuwanci, addini, da hijira. A yau, duk inda ka je a Afirka ta Yamma da Arewa, zaka tarar da Hausawa suna da unguwa nasu.
Asalin tushen hausawa.
1. Nijeriya ita asalin cibiya kuma tushen hausawa a duniya.
Hausawa suna da rinjaye a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Birane kamar Kano, Katsina, Sokoto, Zaria, Daura, Kebbi da sauransu, su ne asalin cibiyoyin Hausa.
2. Niger Republic) Hausawa suna da yawa musamman a kudancin Nijar (Maradi, Zinder, Tahoua).
Wasu masana har suna kiran Nijar da "Ƙasar Hausa" saboda rinjayar Hausa a al’adu da harshe.
3. Ghana Hausawa sun shahara a matsayin ‘yan kasuwa da malaman addini.A'Accra da Kumasi akwai Sabon Gari inda Hausawa suke da ƙarfi sosai.
4. Kamaru ) Hausawa sun zauna a Garoua, Maroua, Ngaoundere da yankunan arewacin ƙasar. Sun rinjayi kasuwanci da Musulunci a yankin.
5. Chadi) Hausawa suna da karfi a N’Djamena (babban birni) da yankunan arewa. Sun shahara da fatauci da sana’ar saye da sayarwa.
6. Sudan) Tun kafin jihadin Usman Ɗan Fodiyo, Hausawa suna zuwa Sudan domin kasuwanci da ilimi. Har yanzu akwai Unguwar Hausa a Khartoum da Omdurman.
7. Libya) Hausawa suna zuwa aiki tun zamanin fataucin bayi da kasuwanci. Yanzu akwai Hausawa da dama da ke zaune a Tripoli da Sabha.
8. Saudi Arabia) A Makkah da Madina akwai unguwannin da ake kira Unguwar Hausa. Hausawa sun kafa cibiyoyin addini, da malamai na Musulunci.
9. Mali) Hausawa sun shahara da kasuwanci a Timbuktu da Gao tun da dadewa.
10. Awannan zamanin hausawa na shiga kasashen ( Burtaniya, Amurka, Kanada, Jamus, Faransa, Qatar, UAE ) Hausawa sun bazu ta hanyar karatu, aiki, da kasuwanci a wa'innan kasashen.
Wannan shine wani bangare na tahiran yaran hausa a duniya.