06/09/2024
Halin da ake ciki fa yanzu ya wuce batun satar kudin gwamnati, an shiga zamanin "ku kawo na hannunku".
Wannan yana daga cikin matsalolin siyasar kudi.
Sun biya an zabesu, ya k**ata mu sani cewa duk Wanda ya bada kudi domin a zave shi, ya san duk wata hanya da zai bi domin ya mayar da kudinsa ya kuma ci riba.
Idan bamu gyara ba, ba za a samu gyara ba a kasar nan.
Dole mu ajiye siyasar kudi, mu koma zaben nagarta da cancanta.
Mu hada Kai mu yiwa 'yan jari hujja da marasa kishin kasa da jama'a ritaya daga siyasa.
Mulki, a tsari na hankali da gaskiya, ba hanyar samun kudi ko tara abin duniya ko Jin dadi da more rayuwa bane.
Matukar mutanen kirki masu hikima da kishin jama'a basu shiga an dama dasu a siyasa da tsarin Mulki ba, haka 'yan WAWA zasu cigaba da zuwa da jakar kudi suna siyen hanyarsu ta zuwa baitulmanin gwamnati domin jidar duk Wani arziki da kasa da jama'ar kasa s**a mallaka.
A yayin da jikinmu yake gaya mana, Allah yasa a gaba mu yi aiki da maganar Bahaushe ta "IDAN KUNNE YA JI JIKI YA TSIRA".
©Malam Naziru