SR TV HAUSA

SR TV HAUSA Domin Samun Ingantattun Labaru Cikin Harshen Hausa Kuci Gaba da Kasancewa da SR TV HAUSA
(1)

WADANDA SUKA MUTU SAKAMAKON RUFTAWAR MAKARANTA YA KAI 54,-Bin Muhammad KD Daraktan ayyuka na hukumar bincike da ceto ta ...
06/10/2025

WADANDA SUKA MUTU SAKAMAKON RUFTAWAR MAKARANTA YA KAI 54,

-Bin Muhammad KD

Daraktan ayyuka na hukumar bincike da ceto ta kasar, ya shaidawa taron manema labarai cewa: "Mun gano gawarwakin mutane 54 da suka hada da ragowar mutane biyar," Yudhi Bramantyo,

Jami'an ceto na ci gaba da aiki ba dare ba rana domin gano wadanda suka bata. "Muna fatan kammala bincike a yau (Litinin) tare da mika gawarwakin" ga iyalai, in ji Yudhi.

Mataimakin darektan hukumar kula da bala'o'i ta kasar Budi Irawan, ya ce rugujewar ita ce bala'i mafi muni da aka taba samu a kasar Indonesia a bana. Ya kara da cewa akalla mutane 13 ne suka bata.

IRAN ZA TA CILLA TAURARON DAN ADAM DA SANDARARREN MAKAMASHI,-Bin Muhammad KD Hukumar sararin samaniya ta kasar Iran ta b...
04/10/2025

IRAN ZA TA CILLA TAURARON DAN ADAM DA SANDARARREN MAKAMASHI,

-Bin Muhammad KD

Hukumar sararin samaniya ta kasar Iran ta bada sanarwan shirin cilla tauraron dan’adam a cibiyar cilla taurarin dan’adam na Chabahar tare da amfani da sandarerren makamashi.

Kamfanin ndillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban hukumar Hassan Salarieh yana fadar haka a yau Asabar ya kuma kara da cewa, an kammala bangare na farko na cibiyar cilla taurarin yan’adam na Chabahar kuma hukumar ta fara shirin amfani da sandarerren makamashi don cillan taurarin yan’adam da suke gabanta, wadanda a shirye suke a cillasu.

Salarieh yace a halin yanzu akwai tauraron dan Adam mai suna Pars-2 da ke jiran cillawa, sannan hukumar zata ci gaba da aiki a bangare na 2 na cibiyar don kammala aikin cibiyar cilla tararin yan’adam mai amfani da makamashin ruwa.

Kamfanonin taurarin yan’adam na kasar Iran dai suna samar da taurarin yan’adam don ayyukan daban-daban, daga ciki har da sadarwa da kuma ayyukan noma da kula da yanayi da sauransu.

Banda haka hukumar tansa gina taurarin yan’adam haka ma kamfanoni masu zaman kansu a cikin gida, ba tare da taimakon wani daga waje ba.

KASAR IRAN TACE BA TA MARABA DA YAKI AMMA TA SHIRYA DON KARE KANTA,-Daga Bin Muhammad KD Mai magana da yawun gwamnatin I...
02/10/2025

KASAR IRAN TACE BA TA MARABA DA YAKI AMMA TA SHIRYA DON KARE KANTA,

-Daga Bin Muhammad KD

Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemah Mohajerani ta fayyace cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta maraba da yaki, amma tana ci gaba da shirye-shiryen tsaro mafi girma don kare kanta.

Ta kara da cewa Tehran ta bayar da shawarar tattaunawa da Amurka kai tsaye a wata ganawa tare da ministocin Turai, amma wakilin Amurka Steve Witkoff ya ki isa a lokacin da aka tsara.

Mai magana da yawun gwamnatin ta Iran ta kuma bayyana cewa, kasarta na ci gaba da musayar sakwanni kai tsaye da kuma a fakaice, kuma tana ci gaba da kokarinta, sai dai kuma gwamnatocin yammacin duniya su ne ke warware alkawuran da suke dauka.

A nasa bangaren, sakataren majalisar kula da harkokin tsaron kasar, Ahmad Jannati, ya bayyana cewa mayar da takunkumin da aka kakabawa kasar Iran yana yadda ma’abota girman kan duniya ke saba alkawuran da suka yi da kuma rashin rikon amana.

Haka nan kuma ya kara da cewa, ‘yancin kai da karfin da Iran take da shi a kodayaushe su ne tushen kiyayya da gaba da kasashe masu girman kai suke nuna mata.

KASAR AMURKA TA AIKA DA JIRAGEN RUWAN NUKILIYA ZUWA KUSA DA RASHA,-Daga Bin Muhammad KD Shugaban kasar Amurka Donald Tru...
01/10/2025

KASAR AMURKA TA AIKA DA JIRAGEN RUWAN NUKILIYA ZUWA KUSA DA RASHA,

-Daga Bin Muhammad KD

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fada a jiya Talata cewa ya bayar da umarnin aikewa da jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa dake dauke da makaman Nukiliya da su karaci gabar ruwan kasar Rasha, a matsayin kandagarko.

Trump ya kara da cewa; A cikin kwanakin bayan an aiko mana sakon barazana daga Rasha, don haka na aike da jiragen ruwa masu makaman Nukiliya da shi ne makamai mafi hatsari.

Shugaban kasar na Amurka ya riya cewa kasarsa tana gaba da kasashen Rasha da China da ci gaban shekau 25 a fagagen kimiyya dakuma kera jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa.

Malamai daga gidaje Daban-daban a cikin Zaria sun ziyarci Sheikh Ibrahim Zakzaky a gidansa dake birnin Abuja jiya Lahadi...
29/09/2025

Malamai daga gidaje Daban-daban a cikin Zaria sun ziyarci Sheikh Ibrahim Zakzaky a gidansa dake birnin Abuja jiya Lahadi. malamin ya rabawa masu ziyarar kyaututtuka da suka hada da qur'anai da charbuna da zobba,

Bin Muhammad
_SR-TV-HAUSA

YANZU-YANZU: Zamu iya barin darika gaba daya matukar ba za aringa daukar mataki kan masu batanci ga manzon Allah (s) ba ...
26/09/2025

YANZU-YANZU: Zamu iya barin darika gaba daya matukar ba za aringa daukar mataki kan masu batanci ga manzon Allah (s) ba ,

Cewar mawaki Bashir dan dago

KASASHEN IRAN RASHA, CHINA PAKISTAN SUN TATTAUNA KAN AFGHANISTAN-Daga Bin Muhammad KD A jiya Alhamis ne aka gudanar da t...
26/09/2025

KASASHEN IRAN RASHA, CHINA PAKISTAN SUN TATTAUNA KAN AFGHANISTAN

-Daga Bin Muhammad KD

A jiya Alhamis ne aka gudanar da taro na hudu na ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Iran da Pakistan da kuma Rasha a gefen taron MDD karo na 80 da ake yi a birnin New York.

A cikin sanarwar ta karshe, kasashen hudu sun jaddada goyon bayansu ga kasar Afganistan mai cin gashin kanta, da hadin kai da dunkulewar kasar, ba tare da samuwar ta'addanci ko yaki ko safarar miyagun kwayoyi ba.

Bangarorin sun bayyana matukar damuwarsu game da yanayin tsaro a Afghanistan, duba da kasancewar kungiyoyi irinsu ISIS, Al-Qaeda, Tehreek-e-Taliban Pakistan (TTP), Jaish-ul-Adl, Balochistan Liberation Army (BLA) da sauran kungiyoyi makamantan su a matsayin babbar barazana ga tsaron yankin da ma duniya baki daya.

Sun kuma jaddada cewa, karfafa zaman lafiya da yaki da ta'addanci, tsatsauran ra'ayi, da laifukan da suka shafi muggan kwayoyi a Afganistan, na cikin moriyar anfani da zai sami kasashen yankin baki daya.

Tumakai Ma Ana Haifarsu Da Kwalli, Ba Iya Anabi Ba – Kalaman Sheikh Lawan Triumph Sun Haddasa Zanga-Zanga a KanoWani mal...
24/09/2025

Tumakai Ma Ana Haifarsu Da Kwalli, Ba Iya Anabi Ba – Kalaman Sheikh Lawan Triumph Sun Haddasa Zanga-Zanga a Kano

Wani malamin Izala, Sheikh Lawan Triumph, ya jawo ce-ce-ku-ce bayan wani jawabi da ya yi inda ya bayyana cewa haihuwar Annabi Muhammadu (SAW) da kwalli ba gaskiya ba ne “tumaki ma ana haifarsu da kwalli.”

Maganar da aka dauka a bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ta haifar da zanga-zanga a Kano, inda matasa da dama suka fito kan tituna suna nuna fushinsu, tare da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su dauki mataki kan abin da suka bayyana a matsayin batanci ga Annabi (SAW).

Dubban mutane ne suka fito a manyan titunan Kano cikin fushi, inda aka rufe shaguna da dakatar da harkokin kasuwanci a wasu unguwanni. Masu zanga-zangar sun rika rera taken yabo ga Annabi, tare da yin kira da a hukunta malamin da suka zarga da kalaman batanci.

Kungiyoyin addini da dama da kuma wasu malamai sun yi tir da kalaman Sheikh Lawan Triumph, suna mai cewa irin wannan magana na iya tayar da fitina tsakanin al’umma. Sun kuma yi kira da a dauki matakin doka domin kare mutuncin Annabi da tabbatar da zaman lafiya.

Wannan labarin na ci gaba da daukar hankalin jama’a a Kano da ma sauran sassan kasar, inda ake jira matakin da hukumomi za su dauka a kan Sheikh Lawan Triumph.

Daga DailyTrueHausa

MA'AJIYAR BAMA-BAMAI TA FASHE A ƘASAR PAKISTAN MUTANE 24 SUN MUTU,-Daga Bin Muhammad KD Kafofin yada labaran cikin gida ...
23/09/2025

MA'AJIYAR BAMA-BAMAI TA FASHE A ƘASAR PAKISTAN MUTANE 24 SUN MUTU,

-Daga Bin Muhammad KD

Kafofin yada labaran cikin gida sun ruwaito cewa 'yan sandan sun danganta fashewar wata ma'ajiyar bama-bamai na kungiyar 'yan ta'adda ta "Tehreek-e-Taliban Pakistan", amma wasu mazauna yankin sun tabbatar da cewa harin da sojoji suka kai shi ne ya haddasa shi.

'Yan sandan Pakistan sun sanar da cewa: Wata fashewa a wani ma'ajiyar harsasai mallakar 'yan ta'adda a arewa maso yammacin kasar ya kashe mutane 24 da suka hada da mata da kananan yara 10. Lamarin ya faru ne a cikin kwarin "Tira" da ke gundumar Khyber a lardin Khyber Pakhtunkhwa.

FARANSA TACE ZATA AMINCE DA ƘASAR FALASDINU A RANAR LITININ MAI ZUWQ-Daga Bin Muhammad KD Shugaban kasar Faransa Emmanue...
20/09/2025

FARANSA TACE ZATA AMINCE DA ƘASAR FALASDINU A RANAR LITININ MAI ZUWQ

-Daga Bin Muhammad KD

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar a yammacin jiya Juma’a cewa: Zai amince da kafa kasar Falasdinu a ranar Litinin mai zuwa a birnin New York.

Macron ya bayyana cewa: Amincewa da kasar Falasdinu wani bangare ne na cikakken shirin zaman lafiya da ke tabbatar da tsaro da zaman lafiya ga Isra’ila da Falasdinu.

Emmanuel Macron zai gabatar da jawabi don tabbatar da wannan karramawa a ranar litinin da misalin karfe 3:00 na rana a birnin New York (9:00 na yamma agogon Paris), yayin wani taron da zai jagoranta tare da yarima mai jiran gado na Saudiyya.

Fadar Elysée ta ce: “A cewar sabon bayanan da aka samu, Mohammed bin Salman zai yi magana ta hanyar taron bidiyo.”

A cikin wannan mahallin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Pascal Confavro ya bayyana a ranar Juma’a cewa; “Wannan amincewa ba ya wakiltar ƙarshen kokarin diflomasiyya … kuma ba furuci ne na alama ba, amma a maimakon haka wani bangare ne na hangen nesa mai zurfi kuma mafi mahimmanci.”

DANGANTAKA NA KARA TSAMI TSAKANIN FARANSA DA IZIRA1LA KAN FALASDINU .-Daga Bin Muhammad KD Matsayar kasar Faransa na ami...
19/09/2025

DANGANTAKA NA KARA TSAMI TSAKANIN FARANSA DA IZIRA1LA KAN FALASDINU .

-Daga Bin Muhammad KD

Matsayar kasar Faransa na amincewa da Falasdinu a matsayin kasa a hukumance a babban taron zauren majalisar dinkin duniya dake zuwa, ya kawo tarnaki sosai a alakar diplomasiya tsakanin ta isara’ila.

Shugaban kasar faransa Emmanuel Macron ya sanar tun a watan yuli cewa faransa za ta amince da falasdinu a matsayin kasa, za ta shiga cikin jerin kasashe da ke goyon bayan kafa kasashe biyu masu yancin kai.

Ana sa bangaren ministan harkokin wajen Isra’ila Gidion Saar ya gargadi Macron da cewa ba’a maraba da shi a Isra’ila har sai faransa ta canza shirinta na amincewa da falasdinu ,yace wannan shirin zai cutar da tsaron Isra’ila kai tsaye.

Shi ma wani babban jami’in tarayyar turai yayi gargadin cewa alaka tsakanin faransa da isara’ila tana kara tabarbarewa sosai, kuma ana kallon Macron a matsayin kanwa uwar gami.

ANYI TATTAUNAWA MAI TSAWO TSAKANIN SYRIA DA IZIRA1LA A BIRNIN LANDAN-Daga Bin Muhammad KD Kafofin yada labaran Izira1la ...
18/09/2025

ANYI TATTAUNAWA MAI TSAWO TSAKANIN SYRIA DA IZIRA1LA A BIRNIN LANDAN

-Daga Bin Muhammad KD

Kafofin yada labaran Izira1la sun rawaito cewa, an gudanar da wani dogon zaman tattaunawa a birnin London a yammacin jiya tsakanin ministan harkokin wajen Syria Asaad al-Sheibani da ministan kula da tsare-tsare na Izira1la Ron Dermer, tare da halartar jakadan Amurka na musamman Tom Barak.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayyana cewa ganawar ta dauki tsawon sa’o’i biyar, inda bangaren Syria ya gabatar da martaninsa kan shawarar da Izira1la ta gabatar na cimma yarjejeniyar tsaro, inda ta ce an samu ci gaba a tattaunawar.

A baya dai bangarorin biyu sun gana a zagaye na biyu da aka sanar, ban da kuma tarukan sirri da suka gudanar a lokuta daban-daban wand aba a sanar ba, da nufin kulla alaka ta siyasa da tsaro a tsakaninsu.

Shugaban rikon kwarya a kasar Syria, Ahmad al-Sharaa (Joulani) ya bayyana cewa, “Tattaunawar tsaro da Izira1la za ta iya haifar da sakamako a cikin kwanaki masu zuwa,” duba da cewa “yarjejeniyar tsaro da Izira1la ta zama wajibi kuma dole ne a mutunta sararin samaniyar Siriya da kuma yankunanta.”

Tun da farko majiyoyin Syria da Izira1la sun bayyana cewa, wakilin Amurka Tom Barrack ne ya jagoranci taron, wanda ya gana da bangarorin biyu fiye da sau daya a wani yunkuri daidaita alaka tsakanin Syria da Izira1la.

Jaridar Haaretz ta Izira1la ta bayar da rahoton da ke cewa, daya daga cikin muhimman abubuwan da aka tattauna a taron tsakanin Dermer-Sheibani shi ne hana kungiyar Hizbullah ko sojojin Iran ko kuma duk wata kungiya da ake ganin tana adawa da Isra’ila kasancewa a kudancin Siriya.

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when SR TV HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to SR TV HAUSA:

Share

Category