25/04/2026
Farfesa Abdulla Uba Adamu ya sanar da yin ritaya daga Jami’ar Bayero Kano yana da shekaru saba’in, inda ya kawo ƙarshen doguwar rayuwar hidima da kuma gagarumar tafiya ta ilimi da ta shafe kusan shekaru arba’in da shida yana yi.
Ya ce: “Tafiyar ta kasance mai wahala, amma cike da gamsuwa — saboda yadda na koyi yadda zan rungume shi.”
Ya ƙara da cewa: “Jami’ar Bayero ta kasance gidana na kusan shekaru arba’in da shida ba tare da hutu ba. Na shiga tsarin a ranar 24 ga Yuli, 1980 a matsayin malamin jami'a a mataki na farko (Graduate Assistant) a sashen Ilimi.”
Ya kuma riƙe matakai daban-daban har ya zama ɗaya daga cikin manyan malamai da ake girmamawa, inda daga baya ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙirƙira Sashen sadarwa da yaɗa labarai a shekarar 2014.
Ya ce: “Na fuskanci ƙalubale, na yi tuntuɓe a wasu lokuta, amma a koyaushe ina sake ƙoƙarin tsayawa kan ƙafafuna don in ci gaba (da tafiya)”
Farfesa Adamu ya bambanta kansa a matsayin mai bincike, mai ba da shawara ga ɗalibai, kuma murya mai tasiri a fagen ilimi. Ayyukansa sun haɗa ilimi, nazarin kafofin yaɗa labarai, da al’adun zamani na dijital, lamarin da ya sa aka san shi a Najeriya da ma ƙasashen waje.
An san shi da zurfin bincike da hangen nesa mai faɗi.
Farfesan ya ba da gudunmawa sosai wajen bunƙasa nazarin sadarwa da kafofin yaɗa labarai a Arewacin Najeriya, inda ya zaburar da ɗalibai da malamai da dama.
Ya ce: “Ba na nadama kan hanyar da na zaɓa; domin tasa na zama nagartaccen mutum.”
Duk da cewa a farko ana sa ran zai karanci likitanci, sai dai Farfesan ya tsaya tsayin daka kan abin da zuciyarsa ke so.
Ya rubuta: “Na yi tunanin zan zama mai bincike a abin da yanzu ake kira kimiyyar dakin gwaje-gwajen lafiya (medical laboratory science), amma hakan bai tabbata ba. Duk da haka, yayin da ritaya ta gabato, sai na fahimci wani abu mai zurfi: cewa ina yin abin da daɗe ina fatan zama tun da farko— wato mai bincike.”
Ya ƙara da cewa: “Sau da yawa nakan tuna wata tattaunawa da na yi da mahaifina a shekarar 1972. Ya so na karanci likitanci. Ban yi hakan ba—ba don na raina shawarar ba, amma domin na san hanyar da zan ɗauka ba a nan take ba.”
Ya yi godiya sosai ga iyalansa, abokan aikinsa, da al’umma baki ɗaya kan goyon bayan da s**a ba shi na tsawon shekaru.
Ya kuma yaba wa matarsa, “wacce ta jure da irin mai da hankalina da nake kan kwamfutata, intanet, da yin bincikena.”
Sai dai Farfesan ya nuna ƙudirin ci gaba da aikinsa na ilimi, inda ya bayyana cewa kamfanin wallafa littattafai na Bloomsbury ya nuna sha’awa kan wasu littattafansa.
Ya ce: “Sha’awar bincike tana nan daram kamar da. Ina da ayyukan littattafai da dama da nake kan yi, kuma Bloomsbury ta nuna sha’awa a kansu.”
Ya ƙara da cewa: “Na yi ritaya ne ba don na gaji ba.”
Game da Farfesa Abdulla Uba Adamu:
Abdulla Uba Adamu farfesa ne a Najeriya, fitaccen masani kuma mai sharhi kan al’amuran jama’a, wanda aka san shi da gagarumar gudunmawarsa a fagen nazarin sadarwa, musamman a kan kafofin yaɗa labarai na Afirka, al’adun jama’a, da masana’antar finafinai ta Hausa (Kannywood).
An haife shi a jihar Kano a ranar 25 ga Satumba, 1954, kuma ya gina doguwar sana’ar ilimi mai tasiri a jami’ar Bayero Kano, inda ya yi aiki a mukamai daban-daban ciki har da zama mataimakin shugaban jami’a (Vice-Chancellor).
Haka kuma ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban jami’ar koyo daga gida (National Open University of Nigeria – NOUN) daga 2016 zuwa 2021.
Baya ga harkokin jami’a, ya kasance mai shiga cikin tattaunawar jama’a, yana ba da haske kan ilimi, tsokaci kan fasahar sadarwa da sauransu.
Bayan kusan shekaru 46 na hidima ba tare da yankewa ba a jami’ar Bayero Kano, ya yi ritaya bayan ya cika shekaru 70, inda ya bar gado na ilimi, jagoranci, da bunƙasa cibiyoyin ilimi wanda ke ci gaba da tasiri ga ɗalibai, malamai, da masu harkar kafofin yaɗa labarai a Najeriya da ma ƙasashen waje.