13/12/2025
TARON CIKA SHEKARA 10 DA WAKI'AR BUHARI A ZARIYA A ABUJA
Harkar Musulunci karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), ta fara gudanar da taron tunawa da waki'ar Buhari a Zaria, waki'ar da Buhari yayi umarnin su Burtai s**ayi kwanaki uku suna kisan kiyashi a Husainiyya Bakiyatullah, da gidan Jagora (H) dake Gyallesu, da Darur-Rahma dake cikin garin Zariya ta Jahar Kaduna.
An fara gudanar da taron da addu'a, daga bisani aka gudanar da gagarumin majalisul aza, sannan aka fara sauraren bayani daga wanda akayi waki'ar Buhari a idonsu, Malam Isma'il D Usman, shine ya fara bayani akan yadda waki'ar Buhari ta ritsa dasu a Husainiyya, sai Ammah Habiba Zariya" ita kuma tayi bayani ne akan yadda 'ya'yanta s**ayi shahada da Mijinta. Daga karshe Sheikh Muhammad Abbari wakilin yan'uwa na garin Gombe ya gabatar da jawabi maudu'i mai taken (Shekaru Goma da waki'ar Buhari, sadaukarwa a tafarkin Allah, darussa daga waki'ar Buhari), sannan aka rufe taro da addu'a aka sallahmi jama'a.
Jiya Juma'a shine ya zama rana ta farko cikin jerin ranakun da za'a gudanar da Taron a Abuja, za'a cigaba da taro gobe, idan Allah ya kaimu
'arBuhariShekara10
12th/ Dec/ 2025