11/08/2022
Menene Dalilin Lalacewar Shugabanci A Arewa?
Al-mansoor Gusau
Al’ummar Arewacin Nijeriya ita ce al’umma mafi kima da daraja a fadin Afirka, ita ce foton da daukacin al’ummar Afirka ke kallo su yi koyi a gurin gudanar da harkokin rayuwa na yau da kullum, domin ita ka dai ce al’ummar da Turawa ‘Yan-mulkin Mallaka ba su yi wa hawan ‘kawara ba, domin ko da su ka shigo Nijeriya ba su same mu al’ummar Arewa a tsirara ba, sun same mu da sutura a jikinmu tare da Ingantaccen Shugabancin mu k**a daga:
•Sarakuna.
•Limamai.
•Dattawan gari.
•Hakimai.
•Dakatai.
•Masu Unguwanni.
Saboda karfin tarbiyya da kaunar juna irin na al’ummar Arewacin Nijeriya, Turawa ba su iya shigowa Arewa su yi mana mulkin mallaka ba, dole sai da su ka hada kai da Sarakunan Lardin Arewa, daga karshe saboda Dattakon al’ummar Arewa Turawan Mulkin Mallaka ba su iya hannunta ‘Yancin wannan Kasa mai suna Nijeriya ba sai a hannun Dattawan Arewacin Nijeriya:
•Sir.Abubakar Tafawa Balewa.
•Sir.Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto).
Haka zalika Laraba ma da su ka shigo Arewacin Nijeriya ta hanyar kasuwanci tare da yada Addinin Musulunci sun samu al’ummar Arewacin Nijeriya da kyawawan halaye da ingantacciyar tarbiyyar da ta yi dai dai da koyarwar Addinin Musulunci, k**a daga:
•Auren Mace fiye da daya.
•Zumunci.
•Kunya.
•Kara.
•Taimakon juna.
•Tausayi.
•Gaskiya.
•Rikon amana.
Allah (SWT) ya daukaka kima da darajar al’ummar Arewa ba a Nijeriya ba, a fadin Tarayyar duniya baki dayanta, domin babu wani mutum a duniya da ake iya gano ko shi waye ta hanyar saka suturarsa sai mutumin Arewa, babu wata Kasa a duniya da ta isa ba tare da tana koyar da harshen al’ummar Arewa na (Hausa) a Jami’arta ba, haka zalika babu wata Kasa a duniya mai ji da kanta da ba ta gudanar da shirye shirye da harshen (Hausa) a gidajen Rediyo da Talabijin dinta ba.
Shugabannin Arewa na farko sun taka gagarumar rawa gurin ganin sun kare kima da martabar al’ummar Arewa, sun kafa mutanen Arewa ta hanyoyu daban daban, wanda galibin Shugabannin Nijeriya a yau dik wadan da Shugabannin farko ne su ka kafa ba tare da sun san Iyayensu ba.
TAMBAYARMU A NAN ITA CE.
• Rikon da Shugabannin Arewa na yau ke yi ma al’ummar Arewa na yau, a haka Shugabannin Arewa na farko su ka rike amanarsu?
• Me ya sa Shugabannin Arewa na farko su ka watsar da abunda za su samu na duniya su da Iyalansu, su ka zabi cigaban al’ummar Arewa, wanda hakan ya haifi Shugabannin Arewa na yanzu, amma su Shugabannin Arewa na yanzu su ka wulakantar da al’ummar Arewa na yanzu su ka zabi kudi?
Abun mamaki da takaici, a ce wai al’ummar Arewa, mutane mafi daraja a Afirka, yau an wayi gari ana k**a mutanen Arewa masu zuwa Kudancin Kasar nan domin neman abinci, ana tsare su k**ar wasu dabbobi har yau babu Shugaba a Arewa da ya ce komai..!!!
• Yau a Arewa babu murya guda daya mai magana amadadin Lardin Arewa kowa ya saurare ta ya yi da’a da biyayya.
• Yau a Arewa mun rasa makoma kullum ana kashe mana al’umma, amma bakin munafurci da son abun duniya ya sa kowa ya rufe bakinsa, babu mai iya yin magana.
• Yau a Arewa an zabi kudi an watsar da mutunci galibin al’umma, inda za su samu kudi to komai ma za a yi, to a yi idan dai an samu kudi.
• Yau a Arewa al’amurra sun lalace, babu noma, babu kiwo, kasuwanci ya yi rauni, babu aikin yi, Dan-talaka komai hazakarsa bai isa ya samu aikin Gwamnatin Tarayya ba, sai dai aikin kaki
Allah (SWT) ka ga halin da al’ummarka, mutanen Arewacin Nijeriya su ka tsinci kawunansu, Allah (SWT) ka kawo mana dauki da agaji irin na ka, Allah (SWT) ka shiryar da Shugabannin Arewa, Allah (SWT) ka kawo ma Arewacin Nijeriya mafita irin ta ka saboda Annabi Muhammad (SAW).
•Wannan rubutu ra’ayi na ne.
•Wannan rubutu tinani na ne.
•Wannan rubutu hange na ne.
•Wannan rubutu fahimta ta ce.
(Section 39 of the Nigerian Constitution)