17/05/2025
Ga jerin fitattun ‘yan takarar da ake sa ran za su fafata a Zaɓen Gwamnan Jihar Katsina a Zaɓen 2027:
1. Gwamna Dikko Umar Radda (Mai Ci Yanzu)
Gwamna Radda, wanda ke kan mulki tun daga 2023 karkashin jam’iyyar APC, ana sa ran zai nemi wa’adin mulki na biyu. Ya shahara da shirye-shiryen ci gaban al’umma da kafa asusun tallafi ga matasa da ‘yan kasuwa, amma har ila yau yana fuskantar s**a daga wasu bangarorin siyasa kan yadda yake tafiyar da harkokin Gwamnati.
2. Sanata Garba Yakubu Lado Danmarke
Sanata Lado Danmarke na jam’iyyar PDP, tsohon ɗan Majalisar Dattawa kuma gagarumin ɗan takarar Gwamna a 2019 da 2023, Yana daga cikin masu fatan komawa tseren kujerar Gwamna. Ana kallonsa a matsayin gwarzon adawa mai karfi, wanda ke da karɓuwa a sassa daban-daban na Jihar musamman Talakawa
3. Sanata Ahmad Babba Kaita
Tsohon Sanata mai wakiltar Daura Zone Sanata Babba Kaita, Wanda ya sauya sheka daga APC zuwa PDP, Wanda a halin yanzu yana SDP na daga cikin matasan jiga-jigai masu tasiri a siyasar jihar. Ya jima yana bayyana damuwarsa kan yadda ake tafiyar da gwamnatin jihar, lamarin da ke nuna alamar zai iya tsayawa takarar Gwamna domin kawo sauyi.
4. Mustapha Muhammad Inuwa
Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Inuwa, wanda ya yi takarar Gwamna a zaben fidda gwani na APC a 2023 amma bai samu nasara ba, Ya fice Daga Jam'iyyar ya koma PDP. Yana Daga cikin wadanda ake hasashen za su sake shigowa tseren.
KBC Hausa