10/09/2025
Kwankwaso, Ganduje da Abba
Kwankwaso ya yi sama da fadi da 2.5 biliyan daga asusun yan fansho na jihar Kano. EFCC ta tono badakalar bayan yan fansho sun kai kokensu. An nemo shi, kuma ya yi fashin baki. Bincike ya tabbatar da ya yi wasa da dukiyar al’ummar jihar Kano da ya kai 41 biliyan da sunan gina gidaje.
Bayan an gina gidajen Kwankwaso ya rabawa yan uwa, abokai, da kuma masu masa hidimar siyasa kusan 324. Yan fansho an barsu a rana. Gwamnatin Kwankwaso ba a harkar fansho kadai ta rika wasa da kudi ba, har da kwangila da tallafin karatu da ake cirewa dalibai da sunan fita kasashen waje karatu.
Kwankwaso ne ya fara kashe ilimin firamare da sakandire bayan Shekarau ya sauka. Da yana son ilimin a hakika da ba cire dalibai kasashen waje kadai zai yi ba, hadawa zai yi da ilimin kasakasa. Bukatar ita ce, a cire matasa masu digiri su je su karo karatu su dawo, daga karshe su saka jar hula su rika kare Kwankwaso. Yau daidaiku ne masu kare kasar Kano da talakawan Kano, amma duk sun zama yan bangar siyasa.
Ganduje ya gaji lalacewar ilimin firamare da sakandire ne a hannun Kwankwaso, amma da yake su yaran da aka dauka zuwa kasashen waje basu da adalci, sai su ka ce shi ya kashe ilimi. Bayan kuma hatta satar kudin al’umma ta hanyar kashe mu raba da sunan Kwangila a hannun Kwankwaso ya koya, da kuma hada yan daba su sassari abokan hamayya.
Ganduje ya fi kowa cire kudade masu nauyi dan zuwa karatu a kasashen ketare. Ya kashe biliyan 20, Kwankwaso kuma biliyan 12, Abba kuma biliyan 5.3. Amma da yake su matasa basu da wayo da ilimi sai suke gani Kwankwaso ne jagora. Idan ana maganar raya jihar Kano da ayyukan cigaba dan saukaka sufuri babu kamar Ganduje. Ya tafka satarsa cikin ilimi, domin shi ya kware a saka hannun jari a samu riba kowa ya samu.
Ba abin mamaki bane dan Abba ya yi sata, gado ya yi a wajen Kwankwaso. Daman barewa ba za tayi gudu danta ya yi rarrafe ba, tayaya za ka saka hannu Audu Rogo ya saci 6.5 biliyan daga ofishinka kuma ka ce ai Ganduje ma barawo ne! Kenan tun asali burinka cin amana ne da gangan, wacce irin magana ce wannan! Yanzu shi Ja’Afar Ja’Afar bashi da hankali ne da ya binciko badakalar? Haba Abba, da wayonka amma ka ba da mu!
Babban takaicina ma shi ne; masu ganin wai Abba ba barawo bane, bayan a gwamnatinsa aka yi satar kwangilar maganin marasa lafiya. Amma da yake ya iya ashana haka ya fito yana nuna bacin ransa. Ga harkar shinkafa dss. Ga barna barjak ta ko ina, ga kuma badakalar Namadi da Danwawu mankas! Duk fa ana sane, kawai an rainawa al’umma hankali ne. Wani kwallo ne ba shege ba! Kar mu ke kallonku. Kwankwasiyya cin amana!
Na tafi fada nemo bayanai!
Tebo