Arewa Ayau

Arewa Ayau Wannan gida angina shine Dan tattaunawa da Nemo mafuta akan matsalolin Arewacin Nigeria

Annabi ya auri Nana A'ishah tana da shekara 15-18 ne, ba wai shekara 9 ba. Cewar Sheikh Muhammad Auwal Shariff Zaria.
12/08/2025

Annabi ya auri Nana A'ishah tana da shekara 15-18 ne, ba wai shekara 9 ba. Cewar Sheikh Muhammad Auwal Shariff Zaria.

A Karshe Dai Mutumin Da Ya Yi Tattaki Daga Jigawa Zuwa Kano Domin Ganin Gwamna Abba Kabir Ya Isa Kofar Fadar Gwamnatin K...
08/08/2025

A Karshe Dai Mutumin Da Ya Yi Tattaki Daga Jigawa Zuwa Kano Domin Ganin Gwamna Abba Kabir Ya Isa Kofar Fadar Gwamnatin Kano, Inda Ya Ce Ko Zai Yi Shekara Guda Ba Zai Tafi Ba Har Sai Ya Ga Abba

A lokacin da yake hanyar tahowa dai, gwamnatin Kano ta bakin kakakin Gwamna Abba ya umarci mutumin da ya koma gida amma duk da haka ya bijire ya taho.

Me za ku ce?

"Ko ni na ce a zabi APC yanzu ba za a zabe ta ba"---Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso a kwanakin baya.
25/07/2025

"Ko ni na ce a zabi APC yanzu ba za a zabe ta ba"---Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso a kwanakin baya.

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!! Gidauniyar Tallafin Karatu ta Sanata Ibrahim Mohammed Bomai na gayyatar duk wadanda sukayi...
20/06/2025

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Gidauniyar Tallafin Karatu ta Sanata Ibrahim Mohammed Bomai na gayyatar duk wadanda sukayi nasarar samun tallafin karatu zuwa ƙasashen waje zuwa bikin miƙa takardun Award Letters.

Rana: 21 ga Yuni, 2025
Lokaci: 11:00 na safe
Wuri: CAMTECH, Potiskum

Kwamishina ya mayar da Naira miliyan 301 ragowar kuɗin ciyarwar azumi a Jigawa Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar J...
07/05/2025

Kwamishina ya mayar da Naira miliyan 301 ragowar kuɗin ciyarwar azumi a Jigawa

Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Auwalu Danladi Sankara, ya mayarwa baitul malin jihar Naira miliyan 301 da su ka yi ragowa bayan kammala shirin ciyarwa na watan Ramadan bana.

Sankara ya sanar da mayar da kudaden ne a yayin taron majalisar zartarwa na jiha wanda gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranta.

Kudin sun yi ragowa ne biyo bayan ware naira biliyan 4.8 da gwamnatin jihar Jigawa ta baiwa ma’aikatar don shirin ciyar da abinci, wanda ya kunshi dukkanin kananan hukumomi 27 da kuma cibiyoyi kusan 700 na ciyarwa.

An ba da rahoton cewa, shirin wanda wani kwamiti ya jagoranta, ya ciyar da mutane sama da 5,550 a kullum a tsawon kwanaki 29 na azumi.

Majalisar zartaswar jihar ta yaba wa matakin da kwamishinan Sankara ya dauka na dawo da ragowar kuɗin, inda ta bayyana hakan a matsayin wani abin yabawa da nuna gaskiya da rikon amana da kuma tattalin dukiyar al'umma.

Senator Ibrahim BOMAI ya kaddamar da tallafin jarin Naira 20k ga mata 4,400 a faɗin Yobe ta kudu.Me za ku ce?
07/05/2025

Senator Ibrahim BOMAI ya kaddamar da tallafin jarin Naira 20k ga mata 4,400 a faɗin Yobe ta kudu.

Me za ku ce?

TIRƘASHI: Gwamnatin Jihar Borno Ta Dakatar Da Kansila Saboda Ya Yi Bidiyo Yana Neman A Taimaki Al’ummar MazaɓarsaAl'umma...
02/05/2025

TIRƘASHI: Gwamnatin Jihar Borno Ta Dakatar Da Kansila Saboda Ya Yi Bidiyo Yana Neman A Taimaki Al’ummar Mazaɓarsa

Al'ummar jihar Borno sun koka kan yadda gwamnatin Jihar Borno ta ƙarƙashin ma’aikatar ƙananan hukumomi ta dakatar da kansilan mazaɓar Yawa Kura da ke ƙaramar hukumar Abadam, saboda zarginsa da rashin tarbiyya ga shugaban ƙaramar hukumar.

A cewar majiyar mu, "Kansilan ya ɗauki bidiyo ne yana bayyana cewa mutane wurarensu sun ƙone ba su da muhalli, ba su da abinci, shugaban ƙaramar hukumar kuma bai zo ya duba su ba. Wannan abin da ya faɗa shi ne ya fusata gwamnati ta ji haushi ta dakatar da shi tare da cewa wai ya saɓa doka ya kuma nuna rashin ɗa’a ga shugaban ƙaramar hukumar". Inji majiyar tamu.

Bayanin dakatarwar dai na ƙunshe ne ta cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙaramar hukumar, da kwamishinan ƙananan hukumomi na Jihar wacce aka buga a ranar 29 ga watan Afrelu, 2025, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta samu rahoto.

Me zaku ce?

SOJOJIN SUN TARWATSA BABBAN KASUWAN WAYA A JAHAR YOBE A Yammacin Yau Lahadi Ne Sojoji Da Mobayil Police S**a Kai Farmaki...
10/02/2025

SOJOJIN SUN TARWATSA BABBAN KASUWAN WAYA A JAHAR YOBE

A Yammacin Yau Lahadi Ne Sojoji Da Mobayil Police S**a Kai Farmaki A Babban Kasuwar Wayan Jahar Yobe Wanda Yake Garin Potiskum

Jami'an Tsaron Sun Shugo Kasuwar Ne Da Yamman Nan Lokacin Kasuwar Tana Cike Makil, S**a Hau Dukan Mutane Da Itace Da Kuma Gindin Bindiga Inda S**a Watsar Da Kasuwar Baki Daya

Jama'a Da Yawa Sun Jikkata Wanda Yanzu Hakama Wasu Na Kwance A Gadon Asibiti, Bayan Haka Anyi Asarar Dukiya Mai Yawa Saka Makon Faffasa Wayoyi Da Computers Da Sojojin S**ayi Allah Ne Kadai Yasan Adadin Asarar Dukiya Da Yan Kasuwar S**ayi

Wannan Babban Barazana Ce A Alummar Potiskum Tunda Har Sojoji Suna Zuwa Inda Mutane Ke Neman Abincin Bakinsu Aci Mutuncin A Musu Asarar Dukiya, Yakamata Shugabanni Tin Daga Kan Mai Girma Gwamna Zuwa Councillor Sarki Zuwa Mai Anguwa Subi Bayan Alummar Potiskum Ganin An Ladaftar Da Sojojin Da S**ayi Wannan Barna Sannan A Biyasu Duk Wata Asara Ta Dukiya Da S**ayi

Dan Wallahi Ko A Mulkin Soja Ba'a Irin Wannan Zalincin B***e Mulkin Farin Hula Da Kowa Yake Da Inci

Allah Yabi Musu Hakkinsu.

Yadda muhawara ta kasance tsakanin wani matashi ɗan Yobe da tsohon Sanatan Kaduna Shehu Sani
06/02/2025

Yadda muhawara ta kasance tsakanin wani matashi ɗan Yobe da tsohon Sanatan Kaduna Shehu Sani

Rahma Sa'idu Mamallakiyar GLK Da Iphone 16 Ta Bude Shago A KanoBikin bude shagon ya samu halartar su Hassan Make Up, G-F...
05/12/2024

Rahma Sa'idu Mamallakiyar GLK Da Iphone 16 Ta Bude Shago A Kano

Bikin bude shagon ya samu halartar su Hassan Make Up, G-Fresh Al'amin, Sadiya Haruna, Samha M. Inuwa da sauransu.

Wace fata za ku yi mata?

23/11/2024

Tambaya.

Wai SYDa. Umar ya daki cikin SYDA Zahra, har SYDA. Zahra tai ɓari, kuma ya karya mata ƙashin haƙarƙarin ta.---A cewar ƴan SHI'A... Amma kuma duk SYDna. Ali na kallo bai yi komai ba.?

31/10/2024

Subhanallahi!
Gwamnatin jihar Yobe ta rage mafi karancin albashi zuwa 17k.

Address

Northern Nigeria
Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Ayau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category