19/12/2025
MUQAWAMA
Kalmar Muƙawama a yanzu ta shahara a bakin masu kokarin kai hari a fakaice ga Harka Islamiyya da Jagorancinta, cewa ana nema a mayar da Da'awar Harka Islamiyya zuwa Muƙawama, su kuma ba za su zura ido hakan ya faru ba. A maimakon hakan, za su yi sa'ayi ne wajen cigaba da Harkar, amma a salon da ba na abinda suke kira Muƙawama ba. Ina iya cewa, a salon abinda ake kira "Likimo". Ko da yake su a bayan fage suna cewa ne, suna yunkurin kawo sauyi ne a tafiyar Haraka Islamiyya.
Ma'anar Muƙawama a wajensu yana farawa ne daga dakewa da tsayuwa ƙyam wajen fuskantar zalunci da azzalumai, ko da kuwa za a kashe wanda ya tsaya din, sai (ma'anar a wajensu) ya tuƙe akan, duk wanda ke ma azzalumi barazana ko kasheji akan cewa, in har ya sake ya kai wani iyaka da zaluncinsa, to zai ɗanɗana kuɗarsa. — Wato in kace, in har azzalumi ya nufi kai hari ga waje mafi girman daraja a doron duniya a wajenka, za ka kare kanka da duk irin abinda kake iyawa, ko da kuwa hakan zai kai ka ga rasa ranka.
Ahhh! Malam da wannan furuci, ka ɗauki Da'awa daga matakin kira, ka kai shi matakin muƙawama, kuma ka yi musu laifi, kuma suna da hakki su yi maka raddi don su kubutar da mabiyansu da ke da Wilaya gare su daga zullumi da fargaban abinda ka iya faruwa sak**akon wannan dakewar.
Babban abin takaici shi ne, yadda s**a tsayu wajen kafa hujja irin wadda 'yan Commercial s**a shafe shekaru suna kafawa 'yan gwagwarmaya, na jirkita tarihin Imamai (AS), da kokarin bayar da shi a sigar kare ra'ayinsu na cewa, mafi yawan Imamai (AS) sun yi gwagwarmaya ne cikin sigar Likimo. — Wal izu billah. S**an ce, Imam wane bai rike makami ya yi yaki ba, Imam wane bai yi fito na fito da azzalumai ba, Imam wane ma ya shiga Hukuma ne, da sauransu. Wato suna kokarin nuna su mabiya wadannan Imaman ne a rayuwar da s**a zabawa kansu na yin Shi'anci mare motsi a zamanin jiran bayyanar wanda zai yi yaki ya mamaye duniya da adalci bayan ta cika da zalunci da danniya. Alhali a karshe bakinsu kan furta cewa duk Imaman nan Shahada s**a yi ta hanyar guba ko takobi, wanda wannan kawai yana tabbatar maka da irin dakewar da s**a yi, wanda ta kai ma ga Shahadantar da su ta duk hanyar da ake iyawa.
Me ya hana Imamai daukan mak**ai akan azzalumai? Amsa: Samun mabiya irin ku, masu ra'ayin cewa rayuwarku ne wanzuwar addini, in kuka sadaukar aka kashe ku saboda addini, ko kan kare alamin addini, kun yi asara ne a ganinku. Da ace duk A'imma (AS) sun samu mabiya masu sallamawa irin Sahabban Imam Hussain (AS), wato mutum kasa da 100 masu Iklasi akan bin Imami a lokacin, da tabbas dukkansu sun yaki azzaluman lokacinsu da makami.
A wasiyyar Manzon Allah (S) ga Amirulmuminin (AS), da ace Imam (AS) ya samu mutane 40 masu Iklasi tun a farkon al'amari, da ya yaki mutanen Saqifa ya karbi ikon gudanarwa, ko da kuwa hakan zai kai ga Shahadarsa da mabiyansa. Amma da ya nema ya rasa, mutane s**a zama irinku, masu jin cewa a tafi a hankali, tunda manya sun riga sun karɓi mulki, a bi su a hankali kawai a wanye lafiya. Sai Imam Ali (AS) ya koma rayuwar addini shi kadansa da Iyalansa, da tsirarun da s**a kasance tare da shi. Har sadda al'umma s**a nuna k**ar da gaske suna shirye da su bi shi, ya yanke musu uzuri, karshe s**a tabbata a mabiya ne irinku, ba masu sallamawa da sadaukarwa ba.
Imam Hasan Almujtaba (AS), har yaki ya daura damarar yi, amma fahimtar cewa mabiyan nan irinku ne, masu makyarkyata wa azzalumai, masu raba Wilaya biyu, daya ga Shi'anci a zahiri, dayan ga Shaiɗanci a baduni, dole ya kwance ɗamarar yakin, aka wayi gari yana aikata addini ne a karan kansa, da kokarin neman mabiya na gaskiya da za su dafa masa a gaba, akan haka har aka Shahadantar da shi.
Imam Hussain (AS) wanda dama k**ar haushinsa wasunku suke ji, ba ma ku cika k**a sunansa ku yi misali da tsayuwarsa da Sahabbansa ba. Amma shi kansa yana da zabi biyu a karshe, ko ya mika wuya ga azzalumai, ko ya dake kyam, da ya tabbata yana da mataimaka da s**a shirya biyayya a gare shi don baiwa addini kariya, ya baiwa ire-irenku uzuri, s**a tattafi don su je su yada addini, ko su yi sauran lamuran rayuwarsu k**ar yadda s**a ce, sai ya fuskanci mafi girman runduna tare da yana da mafi kankantar tawaga. Har Allah Ta'ala Ya bashi nasarar da a yau duk duniyar gwagwarmaya, ta Musulunci ko ta wani abu daban, suna daukarsa a matsayin abin koyi wajen fuskantar zalunci da azzalumai.
Imam Zainul Abidin (AS), ya samu mabiya ne? Imam Baqir da Imam Sadiq (AS) waye ya samu mabiya irin na Imam Husain (AS) a cikinsu? Sun samu almajirai ne kawai masu daukan karatu, wadanda da ace za su musu umurni akan jihadi, da duk za su tarwatse ne bakidayansu, k**ar yadda aka gwada wani mai nuna a shirye yake da hasa wuta aka ce ya shige ta, ya dauka Imam zai halakar da shi ne. Mabiya ne da su irinku, irin kuma wadanda kuke kokarin ginawa a yanzu, da ba amfanin da za su yi ma gwagwarmayar Imam Mahdi (AS) in ya bayyana, sai ma kokarin karyata shi da ruwayoyin cikin littafai da sunan ilimi.
Imam Kazeem (AS) ba samun mabiya irinku, irin wadanda kuke kokarin ginawa ne ya haifar da aka k**a shi aka wurga shi a Kurkuku tsawon shekaru, mabiya s**a yi shiru s**a cigaba da Shi'ancinsu da bugun kirjin an kashe Imam Hussain (AS), suna cewa, ina ma sun kasance tare da Imam Hussain a Karbala, da sun taimaka masa, da sauransu. S**a manta da cewa shi wannan da ke kurkuku s**a kasa tabuka komai akansa, bai da wata maraba da Imam Hussain din sam, har sai da aka kashe shi, aka basu gawarsa a wulakance, suna tunanin za su ga Imam (AS) ya fito salun-alun, sun sha fararen kaya, s**a sallaci gawar Imam cikin kayan farin ciki? An fada muku son Imam Kazeem (AS) ne mabiyansa s**a zama 'yan Likimo irin wannan? Da sun tashi akan taimakonsa za a kai ga hakan?
Kamar fa haka ne mutane s**a so Husainawa su kasance a lokacin da Yazidu ya nufi kashe Husainin Zamaninmu (H), Allah Ta'ala Ya kare rayuwarsa. S**a k**a shi s**a tsare a Kurkuku. Husainawa s**a tsayu kyam da gwagwarmayar nuna yatsa ga azzalumai akan su fahimci hadari ne rike abinda suke rikewa, kuma rashinsa barazana ce ga rayuwarsu. Wasu ala dole sai Husainawa sun bar wannan sadaukarwar, sun zama irin mutanen Imam Musal Kazeem (AS). Su bi azzalumai a hankali, har azzalumai su gane ba wata barazana a kansu ko sun kashe shi, su kashe shi, in an yi sa'a su bayar da gawar a masa sallah, ko su bizne shi da kansu, su barmu da bugun kirji a Markaz da Husainiyoyi, da Zikiran kashe Jagoranmu a duk shekara.😢 Kar Allah Ya nuna mana wannan kunyatan.
Suna cewa wai Imam Mahdi (AS) bai bayyana ba saboda rashin mabiyan da s**a shirya? Tambaya, Imam (AS) din in ya bayyana da masu makyarkyata wa azzalumai zai yi amfani ya yi yaki, ko kuwa da 'yan gwagwarmaya masu dakewar da suke iya fuskantar kowace irin barazana akan wanzuwar addini? Jamhuriyar Musulunci ta Iran sak**akon sadaukarwa da zubar da jinanen Shahidai ne ta tsayu, kuma sak**akon irin wannan sadaukarwa da jinanen Shahidai din ne za ta fadada a duniya, har a wayi gari Imam (AJ) yana bayyana zai zama yana da mataimaka a dukkan sassan duniya, ya yi amfani da su ya yi yaki, a samu Shahidai, karshe Allah Ta'ala Ya bashi nasara.
Harka Islamiyya, kira ne zuwa ga yunkurin tabbatar da addini, kuma cigaba ne ne da'awar Imam Khomeini (QS), wanda tsayuwa kyam din matasan Iran, da fahimtar martaban Shahada ta kai lamarin ga nasara, saboda haka irin wannan sadaukarwar ake da bukatarmu da shi a wannan lokacin. Wannan ne yasa Jagoranmu Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) wanda a makon nan aka karrama shi a matsayin mai bi tare da dabbaka tafarkin Imam Khomeini (QS), ya sha fada mana, yana cigaba da fada mana cewa, wanda duk bai shirya ba da ransa ba, ya fita daga cikin Harkar. Ko ba komai, asasi ne na tarbar Imamul Asr (AS), shi kuma ba zai yi aiki da matsorata ne ba, ko da kuwa sun kira kansu da mafiya Ilimi a duniya.
Kuma idan har jajircewa wajen yin Difa'i sunansa Muqawama, to Harka Islamiyya za ta cigaba da zama Muqawama a duk lokacin hujumin azzalumai, musamman ga Jagoranta, kuma k**ar yadda yake a Fiqihu, za mu yi Difa'i din ne da iyakan abinda muke iyawa ko da za mu rasa ranmu. Ba kisa muke ba, ba hari muke kaiwa ba, Da'awa muke yi, amma Da'awa ba yana nufin za a yi ta yinsa ba tare da kariyar kai ba ne, azzalumai da kansu za su iya kaimu kowane irin mataki, kuma idan s**a kai din, za mu yi hamdala mu karba hannu bibbiyu, Insha Allah.
Nasihar Jagora (H) da ya sha nananatawa shi ne, in karantarwa ka zaba, ka yi karantarwarka, ka yi ta koyarwa, amma ka kyale yan gwagwarmaya su yi sadaukarwarsu. Kar ka soki masu sadaukarwa, kace suna Muqawama ne, ko a kashe su bayan sun dake, su yi Shahada, kace ba Shahada s**a yi ba. Ka yi shiru da bakinka akan abinda ya shafi gwagwarmaya, ka cigaba da abinda kai kake ganin shi za ka iya ba da gudummawa a shi, ba wanda zai zarge ka. Amma duk sadda wani ya bude baki yana s**an Harka Islamiyya a fakaice, to babban Mara Kunya shi ne mai cewa warware shubuharsa rashin kunya ne.
Tafarkin addini na da santsi, a yayin da Annabi (S) ya koma ga Allah ya bar Musulmi fiye da dubu dari biyu, amma aka rasa mutum 40 masu Iklasi wajen bin wasiyinsa da gaskiya. A yayin da manyan al'ummar Annabi (S) s**A Shahadantar da ɗiyarsa ɗaya tal da ya bari, kuma sauran al'ummar s**a kalle su a matsayin manya, s**a cigaba da binsu da sunan sun rigayesu a addini, sun fi su shekaru. Abin tsoro a yayin da aka yanka Imam Husaini (AS) da mataimaka 72, a cikin al'ummar kakansa da ta mamaye duniya. Abin tsoro a yayin da aka rika daure Imamai a Kurkuku, tare da suna da masu cewa su mabiyansu ne dubbai, amma s**a kasa yi ma azzalumai bore, har s**a rika Shahadantar da su, s**a dauki ranakun Shahadarsu a matsayin ranakun kuka kawai.
Abin tsoro in ka dubi cewa wanda ya fara sauke Manzon Rahma (S) a gidansa a Madina, ya sadaukar da kansa ga addini, a karshe ya yi tsawon rayuwa, Yazidu Dan Mu'awiya ne ya masa sallar janaza. Firgici sosai a yayin da Zubair bin Awwam ya sadaukar ta hanyar baiwa Sayyida Zahra (SA) kariya da zare takobi a yayin da aka kawo mata hari a gidanta, amma a karshe ya zare takobi ya yaki Imam Ali (AS) a Jamal. Fargaba sosai idan irin su Ubaidullah, wanda ya kasance daga jaruman wannan addinin a farko, har tsanani yasa yana cikin wadanda aka tura su Hijira zuwa Habasha tare da matarsa, amma za a wayi gari ya bar Musulunci ya koma Kirista a Habasha, tare da babu takura sam a inda yake, har ya zama matarsa ta saku, sai Shugaba (S) ne ya aure ta bayan hakan.
Mamaki sosai, a yayin da Abu Zarril Gifari yake ruwaito Hadisin Manzon Rahma (S) da ke umurni da bin Ahlulbaiti (AS) a bayansa, amma aka rika azabtar da shi saboda wannan, har a karshe aka raba shi da Madina, aka mai da shi dajin Rabaza, inda ya rayu shi kadai, ya mutum shi kadai. Gaskiya tana da ɗaci da wahala, kuma tana da haɗari sosai. Amma duk wanda ya fahimce ta, ya daure ya yi iya kokari wajen tsayuwa akanta, ba tare da damuwa da zargin mai zargi ba.
Taujihi, Irshadi, Shawara, Nusarwa, Tabbatarwa da Aiwatarwar Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne Harkar Musulunci, kuma sallama masa ne bin Harkar. Guna-guni, da zagon ƙasa, da kuma fito-na-fito da matsayarsa kuwa, da su ne ake barin Harkar. Kuma s**an matsayarsa ce fada da Harkar, yi ma Jagorancin Harkar guna-guni ko da a cikin taujihi da irshadinsa ne, alama ce ta munafunci ga wanda yake raya kansa a cikin Harkar. Saboda haka 'yan uwa mu shiga taitayinmu. Mu koma ga Jagora (H), mu fahimci Taujihinsa a gare mu, mu sallama masa. Hakan zai zame mana garkuwa daga amsa kowace irin Fikira da za a yi kokarin kunno da kanta a gare mu. Babu shakka har yanzu, har gobe Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky, da Da'awarsa suna tare da Allah Ta'ala, ba su taba barin Allah Ta'ala ba, kuma wallahi jan kafa daga gare shi ne yunkurin barin Allah Ta'ala. Allah Ta'ala Ya tsare mu.
Sabati Taufiqi ne daga Allah Ta'ala. Mu yawaita addu'ar da Jagora s**a mana Irshadi ta; “Ya Allah, Ya Rahma, Ya Raheem, Ya Muqallibal Qulubi Sabbit Qalbiy ala dinik.” Allah Ta'ala Ya bamu sabati.
— Saifullahi M. Kabir
28 Jimadal Thani 1447 (19/12/2025)